ZUWA GA GWAMNA MASARI (2)

Cigaba daga Mukalarmu ta farko Zuwa Ga Gwamna Masari (1)

Jihar Katsina, jiharmu ce mu duka, lalacewar ta da ci gaban ta, namu ne mu duka. Lokaci ya yi da za mu mayar da hankali kan warware mata matsalolinta da sake lalubo matakan da suka dace domin tayar da komadar ci gaban nata. Yanzu ba lokacin da shugabanni za su tsaya wasa da hankalin talakawa ba ne. Kan mage ya waye! Canji ya samu.

Kenan dole ne a nemar wa jihar Katsina hakkinta. Dole ne mutanen Jihar Katsina (kowa da kowa) su mike domin inganta da ciyar da jihar Katsina gaba. A dage domin yi wa al’umma aiki, a kuma tabbata an zauna don yin daunin da ya dace da kowane yanki na Jihar Katsina. A tabbata ana bin diddigin yadda ake sarrafa dukiyar mutane. A sami wasu daga cikin al’ummar jihar ta Katsina, kamar yadda na fada a baya da za su dinga nuni da inda ake barna domin a gyara.

Ya Mai Girma, abin da muke fada a kullum shi ne mu tsaya tsayin daka mu fahimci yadda mulki ya kamata ya gudana. Kowa na da irin gudunmuwar da zai iya bayar wa, tun daga Gwamna har zuwa talakawa. Mu zauna domin tsara yadda mulki zai gudana, domin taimakon kai da kai.

Saboda haka ya Gwamna, ina ya ga ya dace a samar da wani tsari a jihar tamu da za a yi amfani da shi domin a tabbata aiki na gudana yadda ake so. Halin da ake ciki na ruruta da bayyana rashin katabus da aka tafka a baya, musamman a zamanin Gwamnatin Shema ya isa haka nan. An dai yi kokawa, kuma ya Mai Girma, ai ka yi kaye, lokaci ya yi da za a motsa zuwa gaba. Matsalarmu a yau ba ta tsohon Gwamna Shema ba ce, ta inda za mu dosa ne daga inda ya tsaya. Me za mu yi? Yaya za mu yi? Muna da kudaden da za su taimaka mana wajen ganin mun yi abin da ya dace? Kudaden shiga sun ishe mu? Idan ba su isa ba, ina za mu kwakwulo wasu don raya jihar ta Katsina? Wadannan tambayoyi da wasu irin su, ina jin su ne ya kamata mu mayar da hankali kai. Ta tsohon Gwamna Shema ta kare, yanzu ta Gwamna Masari ake yi! Me aka shirya wa al’ummar jihar Katsina?

Nan ne zan fara da jefo tawa gudunmuwar. Ya Mai Girma, daga bayanan da kake ta kururutawa game da abin da aka yi a baya a wancan Gwamnati ta Shema sai mutum ya dauka cewa ba aikin ci gaba ko daya da Gwamnatin Shema ta yi a jihar Katsina, sai facaka da almundahana, wanda na san ba haka kake nufi ba, tun da lokacin kamfen ya wuce, an kuma zabe ka.

Wani abu da na gani shi ne tamkar kwasan karar mahaukaciya ake neman yi wa matsalolin jihar Katsina, alhali ina ga dauki daidai zai fi alfanu. Ya Mai Girma, a maimakon a ce sai an taba kowane fanni na rayuwar al’umma da ya dagule, me zai hana a dubi matsala guda a hau kanta a dinga dirza har sai ta yi laushi, sa’annan a koma kan wata. Me ya sa gwamnati za ta fi mayar da hankali wajen shan kandamau, inda abin da ake bukata shi ne sha ludayi-ludayi? Al’amurran ilimi na cikin tasku! Hanyoyinmu sun bulbulguce! Ingantaccen ruwan sha ya fara gagarar mu! Talauci ya yi wa yawancin mu katutu! Sata da almundahana a kowane fanni na rayuwa sun kusa zama ruwan dare! Ayyukan noma sai kokawa suke yi! Kiwon lafiya shi kan sa ba shi da lafiyar! Siyasa da mulki da zamantakewa na kewar masu kulawa! Duk ga su nan birjik!Bisa irin wannan fasali, shin ana ga kandamau zai biya? Ko alama!

Dangane da haka nake ganin ya dace a ce cikin wata uku da dori da aka yi an san inda aka nufa. Jama’ar jihar Katsina su san cewa akwai gwamnatin Aminu Bello Masari, ba gwamnati mai yekuwar gwamnatin Ibrahim Shehu Shema ta gaza ba. Ba wai nufina ba ne na ce ba wani abu sabo da gwamnatinka ta yi wa al’ummar jihar Katsina tun hawanta karaga ba ko alama, amma dabashirin ciyar da jihar Katsina gaba ne ban gani ko na ji ba a cikin tsawon lokacin da aka hau karagar mulki.

Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa tsari da tabbatuwar tsari da kuma hangen nesa da ingantaccen dabashiri wajen aiwatarwa su ne ke jan ragamar cigaba. Ke nan abin da ake bukata a jihar Katsina a halin yanzu shi ne a san inda aka sa gaba domin yin aiki gadan-gadan, a kuma lura da bin tafarkin da yake shi ne zai fitar da A’i daga rogo. Me ya kamata a yi a wannan fasali?

Dole ne a bayyana wa mutane halin da ake ciki da kuma abin da aka shirya za a yi. Abin jin dadi shi ne ya Mai Girma, an somo da haka. An bayyana halin da jiya ta kasance, saura yau da kuma gobe. Wato dai ga cuta, saura magani.

Abin da ka bayyana a wajen taron da ka yi da masana da dattawan jihar Katsina bayan kwana 100 da hawanka mulki abin da aka saba ji ne kullum daga kowace irin gwamnati da aka yi a baya. Kowace shekara ai batun ke nan, za a inganta harkokin ilmi. Za a biya wa dalibai kudaden makaranta. Za a gina azuzuwan makarantu. Za a samar da takin zamani. Za a gina hanyoyi a birane da karkara. Za a kawar da talauci. Za a samar da ruwan sha. Za a samar da motocin shiga don inganta sufuri. Za a samar da aikin yi, za a….! Ba iyaka.

Amma kullum tambayar da al’umma ke yi shekara bayan shekara ita ce shin an samar da wadannan abubuwa ko dai kawai ana babarodo ne? Shi ya sa yake da kyau a fahimci lamurra da kyau kafin a dora dan ba. Dole ne idan ana son aikin gaskiya, a bayyana wa mutane abin da za a yi da yadda za a yi, da inda za a samar da kudaden yin abubuwan, a lokaci guda, a kuma gani a kasa a lokacin gudanarwa.

Za Mu Ci Gaba

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

    1. Masari idaikace haka zakayi to wlh kashinka yabushe…… Kace kowane yaro dan prmr da dan secondery zayasamu kwai2 da bred kullun basai sundawo gida break ba…. Kace free education za ayi amman munfarajin raderadin kajanye wannan…… To wai kudin ke babu koko ra’ayi kachanja shine abun tanbaya abani.??????????????