Zamu sami mabiya 200,000 a Shafinmu na Facebook – Zamu Warware Wadansu Dabaibayi

In Sha Allah muna sa rai gobe 22 ga watan Satumba 2015, zamu sami mabiya har kusan dubu dari biyu (200,000), a shafin sada zumunta na Facebook. Wannan zai sanya shafinmu zama daya daga cikin shafuka da zasu sami hatimin yarda a shafin facebook. Alhamdu Lillah!
Godiya ga Allahu Subhanahu Wata’ala da ya nuna mana wannan lokaci, da kuma daukaka mana wannan shafi da ya zama daya tamkar da dubu a wurin warwarewa al’umma matsalolinsu da ya jibinci harkar Computer, Waya da kuma Internet.

Muna mika godiyanmu ga dinbin mabiyanmu wadanda suke kokari kodawane lokaci wurin yada dukkan wani rubutu da muka yi a wannan shafi, ta hanyar yin sharing da likes da kuma yin comment. Gaskiya masu yin wannan aiki suna da matukar yawa, akwai wadanda sun fi shakara hudu suna yiwa wannan shafin hidima, da kuma wadanda su kuma a wannan lokaci suke kokarin yada mu. Dukkanin ku muna yi muku fatan Alkairi, da kuma fatan Allah Ya iya mana.

Muna mika sakon godiya ga babban marubucinmu, babban Shehi a fannin Addini kuma haziki, marubuci, mai bincike a harkokin mu na yau da kullum a fannin Kimiyya da Fahasar Kera-kere, wato Mal. Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq). Haka muna godiya ga Hajiya Salaha Wada Wali wacce ta zamo mana kallabi-tsakanin-rawuna, domin ita ce mace ta farko wacce take kokarin yin rubutu a fanni abin da ya shafi waya da matsalolinta. Adamu Abdullahi Kano wanda shima yana yin kokari matuka wurin yin bayanai akan a bubuwan da suka shafi waya da makamantansu.

Haka wannan shafi ba zai manta da irin su Mal. Tukur Kwaironga wanda shi ne babban malami wanda yake kokarin koyar da mu yadda ake motsa hoto da kwamfuta. Shima Mal. Salisu Ibrahim Kano wanda yake yi mana rubutu a kan kwamfutoci a cikin motoci da abin hawanmu. Haka ba zamu manta da irinsu Pro. Ibrahim Malumfasi, Bashir Bature, Muhammad Sulaiman, Muhammad Uba Bauchi, Al’amin Jibrin Hadison, Dahiru Saleh, Abubakar Sadiq Sodangi, Mal. Kamal Isah Kano, Balarabe Yusuf Babale Gajida da dai makamantansu.

Ba zamu manta da ambato jagororin wannan Mujalla ba irinsu, Mal. Abdullahi Haruna, Mal. Isiyaku Sani, Mal. Salisu Umar Salinga, Mal. Dalhatu Khalid, Alh. Nasiru Ibrahim Dan Sani, Mal. Magaji Galadima (Mai Tsidau Kano), Alh. Abubakar Abdullah Hassan (Optimum Trainers Limited), Mal. Tukur Mamu (Babban Edita Desert Herald).

Haka ba zamu manta da manyan Editocinmu ba, musamman babban Edita a bangaren Hausa, Mal. Zubairu Abdullahi Sada, da masu taimakamasa kamar su Mal. Bashir Hadi Ashara da Abdullahi Maikano.

Muna yi muku godiya, Allah Ya saka muku da alkairi ya kuma albarkaci iliminku, ya kuma biya bukata.

Daga karshe muna fata jama’a zaku ci gaba da yi mana hakuri a wuraren da muka kasa, ta dibin tambayoyin da muka kasa amsawa, da kuma alkawuran da muka yi saboda mutuntaka da ajizanci ba mu iya cikawa. Muna kuma fata zamu inganta ayyukanmu nan gaba In Sha Allah.

Nan bada jimawa ba, zamu fada muku wadansu sababbin canje-canje a babban shafin mu na Duniyar Computer, wadanda suka zamo mana dabaibayi a harkar duniyar computer, kuma mun san zaku ji dadin wannan canji.

Godiya muke yi Allah Ya bar zumunci.

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita
Mujallar Duniyar Computer

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Malam Allah Ya saka da alkairi, wannan ilmin da kuke bawa al’umma ilmine me matukar mahimmanci wanda ahurare da dama Sai anbiya kudi masu yawa sannan akoyama. Gashi kuna bamu shi kaura. Allah ya saka muku da mafificin Alkairi Amin!

  2. Allah ya saka muku da alkhairi Duniar Computer, Gaskia munajin dadin Posting dinku a facebook kuna wayar mana dakai sosai. Inada tambaya bayan wannan; Shin yawan restoring na computer yana jawo mata matsalane ko kuma dai bawani matsala. Domin ni yawanci system din tana nauyi amma idan nayi restoring dinta shikenan. So bansan ko akwai matsala ba yawaita hakan.