Yaya ake yin formating a Computer

Duk da cewar akwai manhajoji da dama wadanda ake iya yin formating na kayan kwamfuta kamar Hard Disk, Memory, Pen Drive, Re-Writable CD ko DVD da dai makantansu, sannan da matakai mabanbanta da mutum zai bi domin ganin ya yi wannan formating amma kafin nan

Mene ne Formating?

Formating shine goge dukkan abin da ke cikin abubuwan da ake iya yin ajiyar kayan kwamfuta. Misali Hard Disk, USB Flash, Memory da dai makamantansu, ta yadda za su kasance babu su a ciki.

Mene ne banbanci tsakanin Formating da Deleting?

Shi deleting ya na baka damar ka cire file ko folder a cikin abu ne, shi kuwa formating yana kankare media din ka ne ta yadda koda akwai wani boyayyen abu kamar virus ko zai goge shi, sannan zai baka dama ka canza tsarin yadda shi drive din ya ke kallo files da suke shigowa cikinsa.

Matakan yin formatting.

  1. Bayan ka saka USB Flash ɗinka a cikin ramin USB sai ka shiga My Computer
  2. Bayan ka shiga My Computer sai ka bata shi USB Flash ɗin zaka iya gane shi ne ta ganin ƙarin babban mazubi, ko kuma ta amfani da harafin da kwamfuta ta ba shi ko kuma sunan shi Flash ɗin. Sai ka latsa shi da maɓallin dama (Right Click).
  3. Zai fito maka da abubuwan zaɓi masu yawa sai ka taɓa Format. Zai buɗe maka ɗan ƙaramin Window da ake amfani da shi domin yin formating.
  4. Sai ka zaɓi NTFS a ramin File System.
  5. Ka zaɓi Quick Format domin yin kankarar cikin sauri.
  6. Sai ka taɓa maɓallin Format
  7. Zai fara yin formating ɗin ya danganci girman sa, amma baya jimawa.

Abin kiyayewa shi ne, da zarar ka taɓa maɓallin formattting dole ka barshi ya kammala idan ba haka ba, ka cireshi ko kuma wata matala ta faru na ɗaukewar kwamfutar ko mutuwa to zaka iya rasa USB Flash ɗin gaba ɗaya.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *