Yaya Ake Gane Hoto Da Aka Canza Shi Daga Asalinsa (Photoshop)?

A Wannan lokacin yana da rikitarwa idan muka yi la’akari da yadda hotunan mutane suke yawo hannayen mutane ta hanyar turo musu shi ta hanyoyin sadarwa na zamani kamar Faceboook, Twitter, WhatsApps, Istigram da dai sauransu.

Irin waɗannan hotuna suna da wuyar fahimtar asalin yanayinsu, sannan kuma sau tari mutane ba sa iya bambancewa tsakanin asalin hoto da wanda wani ya ɗauka ya yi mishi gyara ko kuma kwaskwarima.

Wannan na daga cikin hoton da ya shahara a wayoyin mutane wanda aka dauki Sheikh Kabir Haruna Gombe aka hada shi da wadansu mata masu shirya fina-finan Afirka – idan muka lura zamu ga cewar kan wancan mutumin aka cire aka saka na shi.

Duk lokacin da ake ƙoƙarin yin ɓatanci ga wani mutumin da yake da mutunci, sai ka ga an yi amfani da hotonshi, ko dai a ɓata fuskar shi, ko kuma a haɗa shi da wani abu wanda zai zubar mishi da mutunci.

Kusan mutane da dama ba su tsira daga irin wannan al’amari ba, kama daga Malaman Addinai, ‘Yan Siyasa, Sarakuna, ‘Yan Kasuwa, Jami’an Gwamnati da dai makamantan su. Irin waɗannan canje-canje da ake yi, shi ne abu mafi muni, amma waɗansu suna amfani da wannan ilimi ne domin gyaran hoto saboda kyautata surar hoton, ko kuma canza yanayin wurin da aka ɗauki hoton, ko kuma a gyara shi ta yadda zai ba da sha’awa. Da wannan gyara da kuma ɓata yanayin hoto duk ana kiran su da Photoshop!

Ba wai ya tsaya a gyaran hoto ba ne, yana baka damar saka rubutu a cikin hoton, da ƙara abubuwan burgewa , kamar saka gida, ko ɗaki, ko zaunar da mutam inda yake a tsaye, ko canza yanayin wani da kuma ƙara abu ko rage shi a cikin hoto, wanda wannan ƙare-ƙaren shi aka kira da Graphics. Gidajen Jaridu da Mujallu da Kalandar ɗaurin Aure, ko ta ma’aikata, bangon littafi, kwalayen kaset na bidiyo, Fosta da dai makamantansu, nan aka fi amfani da wannan tsari da ake kira da Graphics.

YAYA AKE GANE HOTON DA AKA CANZA?

Wannan shi ma daya ne daga cikin hotunan da wadansu suka yi lokacin da ake maganar takardun Shugaba Muhammadu Buhari suka cire hoton wadansu mutane masu shirya wani wasan ƙwaikwayo a Legas suna aikin bola, suka dasa kan Buhari a jikin mai kwashan bola.

Mutane suna amfani da wannan manhaja da kuma waɗansu manhajoji domin gyaran hoto. Wannan gyara ya fara daga ƙara wa hoto haske da rage masa, zuwa canza yanayin sa gaba ɗaya. Aƙwai manhajoji masu sauƙin koyo waɗanda kyauta ne, waɗansu kamfanoni masu ƙera camera ne suke yin su domin su sauƙaƙa wa mutane wurin gyara hoto. Misali aƙwai manhajar da ɗaukar hoto suke amfani da ita wurin sanya hoto kamar an zuba mishi hoda ko kuma a ƙirƙira waɗansu hotuna a cikin hoto.

Sannan aƙwai manhajar da sayar da ita ake yi, wacce aka tsara ta domin gyaran hoto da ƙara masa surkulle a cikinsa, irin waɗannan manhajoji suna da matuƙar yawa, kuma kuɗaɗensu ya banbanta da wasu, amma manhaja mafi shahara wurin amfani domin gyaran hoto ko kuma canza shi babu kamar Abobe PhotoShop.

MENE NE PHOTOSHOP?

Wannan kuma hoton sarkin Saudiya Fahad da Shugaban Amurka Bush aka hada su suna sumbantar junansu.

A ilmance, idan aka ce photoshop, wata manhaja ce da kamfanin Adobeda ke ƙasar Amurka ya  ƙirƙiro domin ya baiwa masu amfani da shi damar sarrafa hoto mara motsi zuwa duk yanayin da mutum yake so.

Wannan manhaja tana daga cikin manhajojin gyaran hoto mafi girma a harkar kwamfuta, kuma manyan kamfanonin shirya shafukan Intanet, da gidajen jaridu da mujallu har da kamfanoni, duk suna amfani da wannan manhaja ta Photoshop domin tsaftace hotunan gwanayensu ko kuma kayan sayarwa.

Ita wannan manhaja tana da ƙarfin gaske wurin sarrafa hotona mara motsi, ta hanyar da ya kasance babu wani abu da kuke son yi da hoto da ba za ka iya yi ba.

ALAMOMIN GANE HOTON DA AKA CANZA SHI

Wannan hoton na farko shine gaskiya wanda wannan mutumin ya tsufa ga shi kuma babu hakura a bakinsa amma aka gyarashi ya koma tamkar yaro

Aƙwai alamu da dama da mutane suke amfani da su wurin gane yanayin hoton da aka canza shi ko kuma aka yi mishi wani gyara a jikinshi, kaɗan daga cikin su ne;-

  1. Haske: Duk lokaci da aka taɓa hoto za ka samu ana ƙoƙarin ƙara mishi haske. Za ka ga yanayin fuskar mutumin da ke jikin hoton ta yi haske ba kamar yadda yake a zahiri ba.
  2. Launin sa:Launi wani abu ne da ake la’akari da shi wurin fahimtar hoton da aka gyara, domin wani lokaci ana ƙoƙarin a rage mishi ja, ko rawaya ko shuɗi da ke cikinsa. Ta haka za ka samu wani lokaci hoton ya yi ja dau, ko kuma mutum an san shi a zahiri baƙi ne amma kuma gashi a nan ya yi fari.
  3. Ƙara wani abu a jikinsa: Duk wani hoto da ka ga an yi rubutu, to yana nuna maka cewa wannan hoto ya shiga cikin wata manhaja kuma an sarrafa shi. Wani lokaci ana iya fahimtar wannan hoton an canza shi idan aka ga yanayin wurin da mutum ya ɗauki hoton ya saɓa da inda na asali yake. Misali idan mutum ya ɗauki hoto a cikin ɗakin daukar hoto sai aka canza bangon ɗakin zuwa wani sarari ko fili, ana saka mutum a cikin jirgi da dai makamantan wannan, to duk yana nuna mana cewar wannan hoton ana taɓa shi ko kuma ya shiga ɗaya daga cikin manhajojin gyaran hotuna.
  4. Daga babba zuwa ƙarami: Wannan ita ce hanya da ta fi shahara wurin yin amfani da irin waɗannan manhajoji. Domin ana yawan yin amfani da hotunan manyan mutane a mayar da su su koma yara ko suna wasan ƙasa, ko kuma a ɗora su a kan Fo na bahaya, ko a kan turmi da dai makamantansu.
  5. Fitar Da Tsaraici: Sau tari waɗansu marasa tsoron Allah suna amfani da hoton mutane kamilallalu musamman mata ta hanyar ɗaukar fuskokinsu, a cire shi daga jikinsu a kuma dauko hoton wata fasiƙar mace wacce ta sayar da mutuncinta ta fito tsirara, sai su cire fuskar wannan fasiƙa su ɗora ta waccan baiwar Allah, domin ci mata mutunci ko kuma neman kaskantar da ita.
  6. Ɓata yanayin Halitta: Ana gane cewa wannan hoto an canza shi daga asalinsa ta hanyar canza halitta da aka san mutum da ita. Ko ta hanyar ɓata fuskarsa, ko ta hanyar ƙaro mishi idanuwa ko ƙara wa bakinsa girma ko ta zazzago da haƙora da makamantansu.
  7. Kyautata sura: Ana iya fahimtar cewa wannan hoto an taɓa shi ta wurin kyautata wannan hoton, ta hanyar kankare fuska ta yi fyes, ko kuma gyara tsawan hanci da canza baƙar fuska zuwa fara.
  8. Masu Ɗaukar Hoto: Kusan mafi yawan wuraren ɗaukan hoto a yanzu yana da wahala su ɗauki mutum hoto ba tare da gyara shi ba, ko canza shafin bangon da aka ɗauke shi da shi, ko kuma sa wa hoton zaƙi, ko cire mishi muni, ko yin rubutu a jikin hoton.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin irin hanyoyin da ake gane hoton da aka gyara, amma aƙwai waɗansu hanyoyi da ƙwararru suke iya ganewa, ta hanyar amfani da ƙwarewarsu, da kuma ilimin sanin hoto da suke da shi, da kuma la’akari da yanayin yanka da aka yi wa wannan hoto da kuma dubi zuwa ga zaman hoton a wuri.

WAƊANNE MANHAJOJI NE AKE AMFANI DA SU?

A wannan lokacin da muke ciki mutum ba zai iya faɗa maka yawan manhajoji  da ake amfani da su ba wajen gyara ko kuma ɓata hotunan mutane. Waɗanda ake amfani da su a cikin kwamfutoci, ko wayoyin komai da ruwanka ba (smartphones). Amma zuwa ɗaki guda amma ga kaɗan daga ciki, Adobe Photoshop, Adobe Element, Photoshric, Preesa, Istigram, Photo Shine

MENE NE YA SA MUTANE SUKE SON CANZA HOTO DAGA ASALINSA?

Ya danganci manufar da mutum yake da ita a wurin gyaran hoton, domin waɗansu suna amfani da waɗannan manhajaji domin birge kansu ta yadda suke ɗaukar hotunansu, su gyara su, su yi masu  wasu ƙyale-ƙyale domin burge gwanayen su, ko kuma aminan su.

Amma idan muka yi la’akari da yadda waɗansu suke yin amfani da wannan fasahar ta wurin cin mutunci, da ƙoƙarin zubar da darajar waɗansu, sai mu ga su tasu manufar ba ta da kyau kwata-kwata.

Aƙwai masu ɗaukar hotunan ‘yan siyasa su haɗa su  da mata ko yanayi da bai kamata ba, haka waɗansu sukan yi amfani da hotunan malamai su canza yanayinsa domin neman zubar wa da wannan malaman mutunci ko ɓata masu suna.

Hatta sarakuna da manyan ma’aikatun gwamnati su ma ba su tsallake wannan sharrin ba, duk irin wannan wulaƙanci da cin mutunci wurin canza yanayin hotunansu za ka samu ana yinsa a koda wane lokaci.

Saboda haka waɗansu suna gyara hoto domin jin daɗi, waɗansu kuma suna yi domin cin zarafin mutane.

MENE NE DOKA TA TANADA?

Masana shari’a sun ce duk mutum da aka kama shi yana irin wannan aiki, kuma kotu ta same shi da tabbacin cewar shi ya yi to, zai biya tara ga mutumin da ya wulaƙanta, zai yanka mishi iya kudin da yake ganin cewar yayi daidai da mutuncin da ya zubar mishi, shi kuma zai biya sannan kuma kotu zata iya mai dauri mai tsanani.

JAN HANKALI

Kamar yadda kowa ya sani cewar cin mutuncin mutane ba ya halatta a kowane mahanga ta addini, haka kuma mutum duk lokacin da ka samu wani yana ƙoƙarin yi maka ƙarya da ƙazafi kana ƙoƙarin kare kanka domin kada mutuncinka ya zube a idon waɗanda suke ganin ka da mutunci, to haka shi ma wanda kake ƙoƙarin zubar mashi da mutunci yake, yana da mutunci a idon mutane da dama, mahaifin wasu ne shi, mijin wasu ne, shugaban wasu ne, malamin wasu ne. Sai ka kwatanta da na ka mahaifi ko mahaifiyar, ko kuma malami ko shugaban da ka ke so.

Babu wani abu da za ka samu domin ka gwanance a wurin sarrafa hoto da yin ɓatanci ga mutane, haka duk lokacin da ka ɗauki wani hoto ka sarrafa shi domin ɓatanci ka sani da zarar ya fita daga hannunka ba yadda za ka yi ka raba mutane da shi.

Ta wace hanyar za ka bi domin neman Allah Ya yafe maka, bayan ka watsa shi, miliyoyin mutane sun gani, wasu sun ji daɗi waɗansu kuma sun yi Allah wadai da abin da ka yi. Duk abin da bawa ya yi ya sani cewar aƙwai ranar da zai amsa tambaya a gaban Mahaliccinsa.

A ƙarshe muna kira ga al’umma cewa, koyon ilimin sarrafa hotuna ya na da amfani sosai, amma kuma a guji juya shi domin mutuncin jama’a.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *