Categories
Tsaro

YADDA ZAKA GANE IDAN WANI NA LEKE (SPY) A WAYARKA

Kada ka damu! Lallai miliyoyin mutane suma suna cikin damuwa game da cewar ko ana leken asirin wayoyinsu. Kuma tabbas akwai bakin ciki ace kana yin waya amma kuma wani yana nadar sirrinka, ko kuma duk wani motsi da kayi wani na sane da shi.

To kada ka damu, a wannan mukalar zamu nuna maka wadansu hanyoyi da zaka bi ka fahimci cewar ko ana leka maka waya ko kuma ba a leka ta, daga karshe kuma mu sanar da kai yadda zaka iya kare wayarka daga sharrin irin wadannan manhajoji na leken asiri.

Kamar yadda muka bayyana a mukalar mu ta baya, cewar masu bibiyar wayoyin mutane suna saka wani manhaja ce a wayar wacce take yin aiki a karkashin kasa ba tare da kai mai amfani da wayar ka sani ba, wanda a karshe sai kawai su rika samun dukkan abin da kake yi a wayar tun daga kiran waya da amsawa, aikawa da sakonnin sms kai hatta irin amfani da browser da whatsapp suna iya gani, ba ma a maganar hotuna da kake dauka duk a tafin hannunsu kake.

Ga alamomi da zaka iya gane ko da gaske wani ya ajiye maka irin wannan application ko bai ajiye maka ba.

Idan batirin wayarka na saurin karewa

Idan batirin wayarka na saurin karewa ba kamar yadda ka sani ba a yan kwanakin baya to zai iya yuwuwa akwa manhajar leken asiri a wayarka dake yin aiki ta karkashin kasa.

Wannan bai hada da cewar ko kana yawan biga wasanni da wayar bane, ko kuma kana yawan kallo ko sauraren karatu da wayar ba. Domin yin daya daga cikin wannan yana haifar da wayar saurin karewar batirin waya.

Ama idan ba daya daga cikin wannan; sannan kuma wani lokaci ma sai ka sawa wayar a chaji amma ta dade bata cika ba komu cajar taka lafiya lau take, to, wannan shima yana nuna cewar akwai wani manhajar dake aiki a karkashin kasa.

Idan wayarka na yawan yin zafi

Idan wayarka ta kasance cikin dimi ko zafi kodawane lokaci kuma ba kana amfani da irin manyan application bane a kanta kamar buga game ko kallon video da sauraron sauti to watakila wani ya saka maka application a leken asiri.

Wannan dimin bai shafi irin zafi ko dimin da waya take yi ba a lokacin da ke caja ta a wuta domin wadansu wayoyin sukan yi dimi idan suna caji, amma matukar ba a wutar caji take ba sai kuma take yawan yin zafi to akwai wani application da yake aiki musamman ma idan har zafin ana jin shi a fuskar wayar.

Idan kana jin yar hayaniya idan kana waya

Idan kana yin waya ko kana amsa kira da wani yayi maka sai kana jin wani sauti ba baka saba jinsa ba a baya ko na yar karamar hayaniya to wannan yana nuna maka cewar wani na sauraron abinda kake tattaunawa a waya.

Idan wasu daga cikin kayan setin wayar suka dena aiki

Idan wasu daga cikin kayan seta wayar suka dena aiki musamman irin abubuwan da ake cewa su gyara kansu da kansu misalin autocorrect feature to babu shakka yan dandatsa sun saka maka keylogger a cikin wayarka.

Wannan sune kadan daga cikin hanyoyi mafi shahara da ake iya gane cewar ana leken asirin wayar mutum ko ba a yi. Amma idan mutum ya gwada kusan wadanna hanyoyi amma bai gamsu da cewar ana leken wayarsa ko ba a yi ba, to zai iya bin wadannan manyan hanyoyi da zamu lissafo suma domin taimaka mishi wurin tsarewa ko sanin idan akwai wani ja’iri na labe yana bibiyarsa.

Bincikar yanayin tafiyar network dinka

Abinda muke son mai karatu ya fahimta cewar kusan duk abinda ake kokarin sauraro ko bincika a wayarka ana amfani da intanet ne, saboda haka zaka iya fahimtar idan ya kasance kasan data ta nawa ka siya kuma mene ne nauyinta, sannan nawa kayi amfani da ita ta hanyar amfani code da kamfanonin layin wayarka suka baka wanda kake duba data ta nawa ta rage a wayarka.

Dalilin sanin haka domin dukkan application masu bibiyar wayoyin mutane suna amfani ne da intanet, to kaga idan kafin ka fara amfani da waya kasan girman datar da ta rage a wayarka bayan ka dan shiga intanet ka fita sai data ta zabge gaba daya, gashi kai ba video ka kalla ba, ba wani abu mai nauyi ka sauke ba, ba updating wani application kayi ba, to tabbaci hakika wani yana maka amfani da data domin aikawa da abubuwan da suke cikin wayarka.

Girke manhajar maganin masu bincike (anti-spy app) a wayarka

Idan kana tunanin cewar an sa maka spy app a wayarka hanyar da zata fi maka sauki idan ta baya bata yi maka ba sai ka saukar da application da ake kira da anti-spy app wanda shi aikinsa shine ya binciko maka idan akwai wani application da aka saka maka a cikin wayarka wanda yake bincike ko yi maka leken asiri.

Irin wadannan amhajoji suna da yawa a shafugan ajiyar manhajoji dake google playstore wanda wadansu a cikinsu kyauta ne wasu kuma na siya ne. Kodayake wanda suke amfani da wayoyi kirar Android sun fi masu iPhone shiga hatsarin fadawa ga masu leke, kasancewar mafi yawan wayoyin android daman an yi musu rooting.

Amma iPhone matukar ba a fitar da ita daga bursunarta ba (jailbreaking) wayar ma ba zata ba wani damar ya saka maka wani app din leken asiri tunda damar su manhajojin wayoyin iPhone dole sai a Apple Store ake samunsu, kuma su ba zasu yadda a ajiye spy app a server dinsu ba.

Da wadannan yan bayanai muke fatan zasu taimaka muku domin ku san cewar ana leken asirin wayoyinku ko kuma ba ayi.

5 replies on “YADDA ZAKA GANE IDAN WANI NA LEKE (SPY) A WAYARKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *