Yadda Computer take ganin abu a cikinta … duhu na dukan duhu

Mafi yawancin Computer Digital ce, haka na nufin cewar bata fahimtar komai illar ta hanya guda biyu, kunnawa da kashewa (on/off), su kuwa wadannan hanyoyi suna bijirowa ita computer ne ta lambobi guda biyu 0 (sufuli) da kuma 1 (daya). Shi 0 yana nufin kashewa, ita kuma 1 ta nufin kunnawa. Wato ita na’ura duk abinda yake cikinta tana fahimtarshi ne da wannan lambobi guda biyu, babu wani yare da ita na’ura take fahimta illa abinda ya bayyana a gareta na 0 da 1,.

Sabo da haka, matsayin kunawa da kashewa a wajen na’ura ana kiranshi da bit (an takaita shi cikakken sunan shine Binary Digit), shi kuma digit shine mafi kankantar abu da na’ura zata iya rikewa na data. Idan aka samu digo na bit har guda takwas (8 bits) a dunkule sune suke zama byte daya (1 byte). Shi kuwa byte guda zai iya wakiltar abu guda 256 wanda suka hada da harrufa da lambobi da alamomi da makamantansu.

Cakuduwar 0s (da yawa) da 1s (da yawa) sune suke wakiltar wani abu na data wanda ake kira da suna coding scheme (tsarin fassarawa na’ura rubutu ko data). ma’ana a lokacin da ka rubuta harafin 1 a jikin Microsoft Word ita na’urar bata gane cewar 1 a ka rubuta sai idan processor ya shigar da latsawar da kayi wa keyboard a lokacin sai yaga 00110010 ganin hakan sai ya dauko harafin 1 ya nuna maka a jikin Monitor. Haka idan ka rubuta babban harafin M abinda take iya gani shine 01001101. Mafi shahara daga irin tsare-tsare na fassarawa computer rubutu (coding scheme) sun hada ASCII da EBCDIC da Unicode.

ASCII: Yana nufin American Standard Code for Information Interchange, wannan tsari amfi amfani da shi wajen fassarawa na’ura yadda zata gane data. Ana yawan yin amfani da shi a Personal Computers da kuma Minicomputers.

EBCDIC : Wanda yake nufin Extended Binary Code Decimal Interchange Code, ana amfani da wannan tsari kawai a Mainframe Computers ne.

Unicode: Shi kuma tsari ne da yake baka dama ka rubuta tsarin fassara wa computer da ko wane irin yare na duniya. Wato wanda ya fahimci Unicode zai iya rubuta program da yarensa ku Computer ta fahimci yaren.

Sabo da haka, dan adam yana iya yin magana da Digital Computer da take karbar sako daga tsarin bit ta hanyar amfani da ASCII coding scheme. Yadda abin yake a duk lokacin da ka latsa wani maballi a jikin keyboard, sigina ta wutar lantarkin tana canzawa zuwa binary ta yadda ita computer za ta gane wani harafin da aka latsa sannan ta ajiyeshi a cikin memory. Dukkanin wani harafi da aka latsa ajikin maballin keyboard farkon abinda yake faruwa shine ya canza wannan sigina na lantarki zuwa irin byte nashi. Sai ita na’urar ta sarrafa shi data din ta hanyar bytes wacce take amfani da hanyar kunnawa da kashewa on/off. Lokacin da wannan na’ura ta gama sarrafa wannan harafi sai ta sake canzasu zuwa lamba ko kuma harafi sannan ta fitar da shi ajikin monitor ko kuma ta yi maka printing. Yadda computer take gani wasu harrufa a lokacin da ake rubuta su a jikin ta. wato misalin duk lokacin da Computer taji alamar 01001101 to sai ta gane cewar an taba maballin M a jikin keyboard sabo da haka sai ta dauko hoton M a memory nata sai ta saka a jikin Monitor. haka duk rubutun da zaka yi ajiki ko wane irin abune, kamar waya da makamantansu ita na’urar abinda take gani shine 0 da 1 kai kuma kana ganin hotunan harrufa da kake tabawa.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Allah yasaka da Alhairi yasa mucika da imani, ya karamana ilimi mai amfani don mu ilimanta amin. Allah ma albarka ya jikin mahaifa ya kareka da kariyarsa @salisuwapmaster

  2. Wannan gaskiyane! Kuma wannan shi akekira webmaster. Ina gwanin wani? Ganawa. Agaskiya ba abinda zamuce da wannan babban malamin namu malam salisu webmaster. sai dai muce Allah yabarmanashi da imani. Allah yakara Kare manashi daga duk wanda yake bibiyar wannan shafin namu mai dumbin Albarka amin.