Yadda ATM yake yin aiki

ATM wanda ake kira Automated Teller Machine na’ura ce da ake amfani da ita domin diban kudi ko aikawa da sakon kudi ga mutumin da yake ma’ajiya a daya daga cikin bankunan da suke amfani da wannan tsari ba tare da neman taimakon wani ma’aikacin banki ba. Irin wannan na’ura da ake kira da ATM iri biyu ce. Akwai wacce ita aikin ta shine ta bayar da kudi kawai sannan kuma zata iya bayar da bayanan kudi ko rahoton abin da mutum ya ajiye a bankinsa.

Dayar kuwa tana aikin da ya zarce ta farko domin baya da biyan kudi kuma tana ba mutum damar ya iya aikawa da sakon kudi na zahiri, da bayar da wadansu muhimman bayanai na katin ATM din mutum sannan kuma ya fitar rahoton bayanan bankin mutum.

Shi wannan na’ura na ATM bankuna ne kawai suke amfani da su domin biya da fitar da bayanan mutane. Su kuma abokanan huldarsu suna iya amfani da wannan na’ura ce kawai idan suka karbi katin ciran kudi daga bankin nasu.

Shi kuma wannan katin ajikinshi akwai wata ‘yar karamar na’ura da ajikinta akwai maganadisu da yake tattare da bayanai na babban kwamfutocin shi wannan banki da ake amfani da shi wurin sanin me mutum ke ajiye da shi a mazubinshi.

Da wannan dalilin ne ya sa mutum ke saka wannan katin a jikin wannan mashin na ATM ya iya fitar da kudin dake cikin akwatinsa bayan ya saka lambobin sirri guda hudu da bankinsa suka bashi idan komai yayi daidai kudi ya fito daga na’urar iya adadin abinda yake bukata.

Wannan na’ura ta ATM John Shepherd-Barron ne ya kirkire ta a shekarar 1960

ABUBUWAN DA SUKA HADA ATM

Na’urar ATM ta hada abubuwa manya guda biyu

 1. Abubuwan shigar da bayanai (Input Devices)
  1. Na’urar karanta bayanan kati – Card Reader
  1. Na’urar Rubutu – Keypad
 2. Abubuwan fitar da bayanai (Output Devices)
  1. Na’urar fitar da sauti – Speaker
  1. Na’urar nuna rubutu – Display Screen
  1. Na’urar fitar da takarda – Receipt Printa
  1. Na’urar fitar da kudi – Cash Dispenser

Na’urar Karanta bayanan kati – Card Reader

Shi card reader yana daga cikin abubuwan da ake amfani da shi domin a aikawa da ita na’urar ATM bayanai (Input Devices), kuma aikin da shi wannan na’urar take yi (card reader) shine karanta bayanan mutum da yake jikin katin.

Bayan mutum ya zura katinsa a jikin wannan na’ura sai ta karanta bayanan ta bincika shin wannan katin nawane banki ne, kuma mene ne lambar mutum na ajiyarsa, daga nan sai ta tura wannan bayani zuwa ga dakin ajiyar bayanai na ATM shi kuma ya aika zuwa bankin mutum.

Na’urar Rubutu – Keypad

Bayan mutum ya zura katinsa kuma katin ya samu damar haduwa da dakin ajiyar bayanai na ATM da kuma babbar na’urar kwamfutar bankinsa, sai ayi amfani da na’urar rubutu domin shigar da lambobin na musamman da shi me katin ya shirya su domin duk lokacin da zai yi amfani da katin ya saka su.

Da shi wannan keypad din mutum zai saka wadannan lambobi guda hudu, da shi kuma zai iya cewa yana son kudi kaza ko baya bukatar fitar da su. Akwai doka ta musamman ta yadda ake amfani da wadannan maballai a kowace kasa. Sau tari abubuwan da mutum ke aikawa ta wannan keypad a jagwalgwale (encrypted) yake zuwa ta yadda wani ba zai iya karanta wannan bayanin ba koda ya saci hanyar bayanan banki. Akwai maballai guda goma sha shida wanda mutum zai iya rubuta abubuwa kusan 48 na haruffa da makamantansu.

Na’urar fitar da sauti – Speaker

Ita wannan na’urar ta speaker aikin ta shine fitar da sautin maballin da mutum ya bata, a wane lokacin gaisuwa da fada maka sakamakon abin da kake yi, misali idan kana neman bayanai na banki ko na kudi sai ta fada maka cewar aiki na gudana halin yanzu.

Na’urar nuna rubutu – Display Screen

Ina wannan na’ura ita ce ke nunawa mutum inda yake a ciki, daga lokacin da ka zura kati har zuwa lokacin da zaka  cire katin duk abin da zaka rubuta da bayanan kudinka da zabin kudin da za a fitar duk a jikin Display Screen. Ita wannan na’ura ta nuna bayanai wani lokaci bankuna suna amfani da CRT Monitor wasu kuma suna amfani da LCD Monitor ne.

Na’urar fitar da takarda – Receipt Printa

Ita na’urar fitar da takarda tana fitar da rahoton abin da mutum ya fitar na kudinsa tare da kwanan wata da ranar da aka fitar da kudin da yawan kudin da mutum ya fitar da ragowar kudin da ya rage a bankin mutum.

Na’urar fitar da kudi – Cash Dispenser

Ita wannan na’ura kusan ita ce zuciyar ATM domin ita ce ke iya fitar da kudin da mutum ya nemi na’urar ta fitar mishi da shi bayan ATM din ya tabbatar da dukkan bayanan mutum sun zama ingantattu.

Aikin wannan na’ura shine ta irga adadin kudin mutum ya nema, ta kuma bincika wurin ajiyar kudin da aka tara mata ta duba ta gani idan akwai irin kudin kuma sun kai yawan da ya nema sai ta irga ta bayar.

Idan aka yi rashin sa a akwai kudin da ya lankwashe to ita wannan Cash Dispenser sai ta zuba wannan lankwasasshen kudin zuwa wani akwati na daban. Dukkan kudaden da wannan na’urar ta fitar tana kuma ajiyar dukkan abin da ya guda a cikinta, na kudin da ta fitar, da wanda tayi kuskuren rikewa, da adadin abin da aka saka mata da wanda ya rage tare da taimakon na’urar RTC.

ATM Networking

Kamfanonin da suke bayanar da Intanet wato Internet Service Provider (ISP) suna taka muhimmiyar rawa wurin tafiyar da al’amuran ATM. Domin lokacin da mutum ya zura wannan katin na’urar, Intanet shine ke kulla alaka tsakanin shi ATM din da kuma babban bankin mutum.

Bayan da mutum ya rubuta lambar PIN din katinsa bayanan zasu bi ta Intanet zuwa babbar ma’adanar ta, sai ta aika da wannan bayanan zuwa ga babbar na’urar, idan bayanan sun yi daidai sai aba mutum damar yin abinda yake son yi.

Na’urorin ATM iri biyu ne

Mafi yawancin ATM da ake da ake amfani da su iri biyu ne da kamfanonin da suke lura da bayanan su suke bayarwa.

 1. Leased Line ATM
 2. Dial up ATM

Leased Line ATM

Shi na’urar ATM din ana jonata ne kai tsaye da babbar kwamfutar da ke lura da dukkan ATM din ta hanyar amfani da layin waya guda hudu kai tsaye daga ita ATM din zuwa babbar kwamfuta ta hanyar amfani da layin waya na Telephone. An fi son irin wannan na’urar sai dai kudin sakata da amfani da ita yana yiwa bankuna tsada sosai.

Dial Up ATM

Shi wannan na’urar ATM din tana amfani da layin telephone ne ta hanyar amfani da modem. Bankuna suna son yin amfani da wannan na’ura saboda bata tsada wurin sakawa.

Tsaro da ATM yake da shi

Lambobi guda hudu na PIN shine farkon garkuwar katin mutum wanda yake kasancewa sirri ne tsakanin mai shi katin da ATM dinsa. Shi kuma abin da yake rubutawa ajikin ATM din an rubuta wata manhaja da take jagwalgwala rubutun ta yadda babu yadda za ayi wani ya iya sani me mutum yake yi koda ya yayi kokarin amfani da ilimin satar bayanai.

Ana amfani da tsaro mai karfi na Triple Data Encryption Slandered wurin jagwalgwala dukkan bayanai da suke zagayawa tsakanin babban dakin sarrafa bayanai da kuma bankin da mutum yake ajiyar kudi.

Ka’idojin da ATM yake bi domin yin aiki

Kamar yadda muka fada ATM yana amfani da abubuwan shigar da bayanai guda biyu da na fitar da bayanai guda hudu. Wadannan na’urori guda shida sune suke kulla alaka tsakanin ATM din da babban dakin ajiyar bayanan sa, shi kuma dakin ajiyar bayanan ATM shi ne zai yi magana da babban kwamfutar ajiyar bayanan mutum na banki. Dukkan ATM da suke aiki a duniya suna amfani da babbar Database da suke musayar bayanai. Shi ATM din dole yayi magana da babbar kwamfuta (server) da ke ajiyar bayanan ATM. Ita babbar dakin bayanai ita zata yi amfani da Intanet domin magana da bankin mutum. Amma dukkan abubuwan da ATM din yake bukata ya tattara ne a jikin katin ATM din dake hannun mutum.

Lokacin da mutum ya zura katin sa ajikin ATM domin yayi hulda da ATM, shi mutumin shi zai bayar da amsoshin bayanan da ATM ya tambaye shi ta amfani da keypad. Shi kuma ATM zai aika da wannan bayanan zuwa babban dakin ajiyar bayanan sa. Shi kuma babban dakin ajiyar bayanan sai yayi magana da bankin mutum nan take. Idan mutum yana bukatar ya fitar da kudi ne, to babban dakin ajiyar bayanan ita ce zata cire kudin daga cikin bankin mutumin da ya ke dashi a banki. Da zarar bankin ya tura wannan kudi zuwa dakin ajiyar bayanan ATM sai shi wannan dakin ajiyar ya ba ATM izinin fitar da wannan kudi da mutum ya bukata.

Amfanin da ATM yake yi

 1. Ana anfani da ATM a kowane lokaci ba dare ba rana
 2. Akwai sirri wurin mu’amala da ATM da bankin mutum
 3. ATM na ragewa ma’aikatan banki wahalhalu
 4. Ana samun sababbin kudi a ATM
 5. Mutane sun fi samun natsuwa a ATM
 6. Matafiya suna jin dadin ATM
 7. Ana samun bayanai a ATM ba tare da tangarda ba

Saukin da ATM ya kawo

 • Yana kulla alaka tsakanin bankuna
 • Yana bada damar sanin bayanin bankin mutum
 • Yana fitar da takardar bayanin mutum na bankin sa
 • Yana baka damar canja PIN
 • Yana baka damar fitar da kudi
 • Yana baka damar siyan katin waya
 • Yana baka damar biyan kudin aikace-aikace
 • Yana bada damar hulda da bankunan da suke kasashen waje.

Wannan shine karshen bayani game da yadda ATM take yi aiki. Idan akwai wani tambaya ko neman karin bayani sai ka yi a kasan wannan kasida a wurin sharhi.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 1. Assalamu alaikum
  Muna godiya da irin kokarin ku wajen wayar mana kai, a fannin Na’ororin zamani.
  Allah yasa ka da alheri.

  Ga tambaya ta game da ATM: Me ke sa wani lokaci in mutum ya bukaci kudi sai ya juya kamar zai bada amma sa kaji shiru, sannan sai kaji sako cewa ambaka kudin.
  Haka ya taba faruwa dani har sau biyu kuma na sha wahala kafin kudin su dawo. Saboda ba’a Bankin da nake ajiye bane naje cire kudin.
  Ya mutum zai yi domin kauce wa irin wannan Matsala.

  Daga Nasiru Sulaiman Funtua
  08065579595, 08056700407