Yadda ake yin rubutu a ajiye shi a Microsoft Office

Yin rubutu a Microsoft office a matakin farko abu ne mai sauƙin gaske, domin shi daman Microsoft Word ko MS Word aikin shi shi ne ya sauƙaƙa maka wajen yin rubutu zalla da kuma sarrafa shi.

Idan kana son ka rubuta wasiƙa a MS Word da farko sai ka buɗe shi application ɗin. Sai ka fara rubutun abin da kake son ka rubuta. Bayan ka gama to akwai ‘yan abubuwan lura wajen yin rubutu misalin

1)            Font ko font character: idan kana son ka canza tsarin rubutu zuwa wani tsari, kamar canza shi gana wanda ka fara yi da shi zuwa kamar rubutun kwasa, sai ka shi ga nan ka zaɓa

2)            Font Size: girman rubutu a nan ne za ka canza yanayin girma ko ƙanƙantar rubutunka da kake son ya bayyana a cikin shafinka.

3)            Bold: Sanya rubutu ya yi kauri, yin haka ya saɓa wa ƙara wa rubutu girma domin a wannan karon kana son rubutun ya yi kauri ne.

4)            Italic: Karkatar da rubutu ya ɗan lanƙwashe, yin haka ya saɓa wa canza rubutu zuwa kwasa domin shi wannan zai taimaka maka ne wajen lanƙwasa shi rubutun ka domin nuna mahimmancin rubutu ko kuma kalma

5)            Bullets: Su ake yin amfani da su wajen nuna alamun ƙidaya wacce ba a buƙatar a sa mata lambobi. Idan kana son ka yi rubutu amma kuma rubutun ya ƙunshi sai ka lissafa abubuwa kamar sunayen mutanen da su ka yi rajista a makaranta to idan ba ka son lissafin ya nuna lambobi sai ka yi amfani da bullets.

6)            Numbering: Shi kuma shi ne ke mazaunin bullets a lokacin da za ka yi jero sunayen wasu abubuwa kuma kana buƙatar ƙidaya su da lambobi sai ka yi amfani da numbering. Wurin yin amfani da wannan jerantuwar lambobi ka na da zaɓi ka yi amfini da lambobi na 123 ko kuma baƙaƙen harufa ABCD haka za ka iya amfani da lissafin Roman Figure I II III IV.

7)            Alignment: Wannan shi ne tsarin da za ka yi amfani da shi domin ka zaɓi hanyar da kake son rubutunka ya bi. Misalin idan kana son rubutun ka ya fara tafiya daga hannun dama ya ƙare ta hannun hagu sai ka zaɓi Right Alingnment. Haka idan kana son rubutun ya fara daga hagu ya ƙare a dama sai ka zaɓi Left Alignment. Idan kuwa so ka ke ka yi rubutu da zai fara a tsakiyar shafi yana bajewa daga tsakiya sai ka zaɓi Centre Alignment. Idan kuwa so ka ke rubutun ya faro daga hannun hagu sannan ya ƙare ta dama amma kuma ya zama wani rubutu bai wuce wani ba a takardar sai ka zaɓi Justify Alignment

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin hanyoyin da ake fara yin rubutu a MS Word wanda duk wanda ya ke da sha’awar ya rubuta ‘yar wasiƙa ko kuma ya rubuta wani rubutu to, ya yi amfani da ɗan wannan taƙaitaccen bayanin da mu ka yi zai taimaka gaya.

Amma kuma dangane da abin da ya sha fi ajiyar ita wannan takarda da ka yi a cikin computer, shi ma abu ne da ke da mahimmanci, domin amfani ajiya maganin wata rana in ji hausawa. Ana yin ajiyar irin waɗannan rubuce-rubucen ba domin komai ba sai domin idan nan gaba ka tashi za ka sake rubuta irin wannan takarda ba sai ka sako daga farko zuwa ƙarshe ba. Ka ga idan ka ajiye to buɗewa kawai za ka yi ka yi ‘yan gyare-gyaren da kake buƙata.

idan da hannu za ayi zai ɗauke ka kwanaki, kamar ya yi maka lissafin adadin kalmomi da harrufa da suke cikin rubutunka. Duk a cikin MS Office za ka iya rubuta wasiƙa guda ya saka maka sunayen waɗanda za su karɓa lokaci guda (Mail marge), haka kuma a cikin shi MS Office za ka iya saka abin da ake kira da Index da kuma Citations da Bibliography da dai abubuwa da muke iya gani a cikin littattafai na Turawa da Larabawa. Akwai hanyoyi da ake ajiyar rubutu a MS Word amma tun da wannan karatu da muke yi muna yi wa waɗanda ba su iya amfani da shi wannan application ba ne. To, hanya ɗaya kacal a wannan darasi zan nuna sai a darasinmu na gaba.

Bayan ka gama rubutun ka sai ka kai mouse zuwa sama inda aka rubuta file idan kana amfani da MS Word 2003 za ka ga SAVE sai ka latsa shi, zai fito maka wani ƙaramin Windows ya tambaye ka wurin da ka ke son ka ajiye sannan kuma ka ba shi file din suna.

Wannan shi ne a taƙaice yadda ake yin rubutu a MS Word kuma a ajiye shi (Saving).

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *