Yadda ake saukar da video daga YouTube

Matashiya

Kafin mu yi bayanin hanyoyi da ake bi domin a saukar da bidiyo daga dandalin zumunta na YouTube, yana da kyau mu fahimci waɗansu ƙa’idoji da dokokin saukar da abu daga shi wannan zaure na YouTube.

Shi dai wannan kamfani na YouTube mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, a halin da muke ciki a yanzu babu wani ɗaki ko shafi a duniyar nan da ya ajiye hotuna masu motsi kamar YouTube, haka kuma shi ne shafi wanda aka fi ziyarta domin kallon hotuna masu mosti, kuma shi ne shafi na uku a ziyarta a duk shafukan da suke intanet.

Domin an ƙiyasta sama da mutane biliyan ɗaya (1 billion) suke amfani da wannan shafi na YouTube. ɗaka kuma a shekarar 2014 kamfanin ya sami ribar kuɗi zunzurutun Dalar Amurka Biliyon 4 (4 Billion USD), haka kuma kamar yadda kamfanin dubawa da yin hasashe na DMR (Digital Marketing Statistics) suka faɗi cewar a kullum ana kallon bidiyo biliyan 4 a kowace rana.

A wuraren Satumbar 2011, kamfanin ya yi wani alƙawari da har yau bai cika ba, na cewar za su saki wata manhaja wacce za ta ba mutane masu amfani da wayar komai da ruwanka damar kallon bidiyo a YouTube ba tare da amfani da fasahar intanet ba, matuƙar ka buɗe shi bidiyon kafin ka kashe intanet ɗin. Wannan yunƙuri na su, har yanzu bai tabbata ba.

Amma kuma idan ka dubi mafi yawancin bidiyon da yake cikin kwamfutocin mutane da wayoyinsu za ka samu cewar ana samun su ne daga YouTube. To, haka abin yake, domin kusan kafin a fara samun makarantu masu zaman kansu a intanet, mutane da dama suna ɗora karatukansu a shafin YouTube domin jama’a su kalle su. Shi ya sa YouTube ya zama wani dausayin alheri da kuma tsibiri na sharri. Domin kusan dukkanin wani ilimi da mutum yake son ya koya zai yi wahala a shiga cikin shafin YouTube bai same shi ba. Wani lokaci ma shi wannan shafin manyan gidajen jaridu da gidajen yaɗa labarai na talabijin suna amfani da shi wurin ɗora shirye-shirye domin jama’a su yi amfani da shi ko kuma su sake kallonsa.

Shi ya sa kowane irin bidiyo ake samun shi a YouTube, kama tun daga na karatu, wasanni, nishaɗi, faɗakarwa da dai makamantansu, kuma dukkaninsu ana samun masu tsawo da matsakaita. A wani lokaci za ka samu mutum ɗaya ya ɗora bidiyo sama da dubu biyu a shafinsa, kuma ka samu yana da mabiya ko masu kallo sama da miliyoyin adadi.

Taƙaitaccen tarihin kafa YouTube

YouTube na ɗaya daga cikin shafuka a Intanet irin waɗanda ake kiran su da video-sharing website, wato shafukan da ake saka bidiyo domin waɗansu su kalla, ya na da Hedkwata a San Bruno a Jihar California ta ƙasar Amurka. Waɗansu matasa su uku Steve Chen, Chad Hurley da kuma Jawed Karim su ne suka ƙirƙiro shafin a ranar 14 ga watan Fabrairu 2005 bayan da suka bar aiki a wani kamfanin hada-hadar kuɗi a intanet mai suna PayPal. Tun daga shekarar 2005 zuwa 2006 su ne suke da alhakin mallakar komai a shafin YouTube har zuwa lokacin da kamfanin Google ya ga muhimmancin wannan shafi da yadda ya sami karɓuwa a wurin mutane, ya siye shi da kuɗi wuri na gugar wuri har Dalar Amurka Bilyan 1 da Miliyan 650 ($1.65 billion) a watan Satumba 2006.

Daga dama: Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim

Shafin wanda yake ba mutane damar su ɗora bidiyo domin mutane su kalla ko domin su yaɗa shi a shafukan intanet ko kuma liƙa shi a shafukan zumunta. Ana amfani da zarin abin kallo na kwamfuta da wayoyi domin iya kallon su, kamar tsarin WebM da H.264 da MPEG-4 da AVC da kuma Adobe Flash Player.

Ana samun bidiyo daban-daban kamar na wasanni, shirye-shiryen gidajen yaɗa labarai, bidiyon waƙoƙi, fina-finai, karatuka, bidiyo domin ilmantarwa da dai makamantansu.

Mafi yawancin bidiyon da suke YouTube gama garin mutane ne suka ɗora shi, amma kuma ana samun gidanjen yaɗa labarai manya sanannu suna amfani da shi, kamar irin su CBS, BBC da VOA da dai makamantansu.

Wanda bai yi rajista da YouTube ba zai iya kallo ne kawai, amma wanɗa ya yi rajista zai iya kallo, zai iya ɗora shi ma na shi bidiyon domin waɗansu su kalla, zai iya kulla alaka da wani mai daki a YouTube duk lokacin da ya ɗora wani sabon bidiyo a sanar da shi kai tsaye (Subcribe), sannan zai iya yin tsokaci (comment) ga bidiyon da aka bayar da damar yin tsokaci a kai.

Dukkan bidiyon da yake YouTube babu matsala wurin kallonsa matuƙar bai ɗoki hotuna na tsaraici ko na wanda yake dauke da hotuna masu hatsari, kamar kisa ko kuma abin da bai kamata masu ƙaramin ƙwaƙwalsu kalla ba. To irin waɗannan bidiyo dole sai ka fadawa YouTube cewar kai ka wuce shekaru 18 kafin ka ga irin waɗannan bidiyoyin.

Shafin na YouTube yana samun kuɗaɗen shigar shi ta hanyar saka talla da yake yi a kan bidiyo da mutane suke kallo, kuma suna ba masu bidiyon damar mallakar kashi 55% na kuɗin da ake biyansu. Misali a shekarar 2013 kamfanonin da suke ba YouTube talla suna biyan su Dalar Amurka $6.60, idan aka kalli bidiyo ko kuma tallarsu har sau 1000, wanda yake nuna cewar duk wanda ya amince da YouTube su saka talla a kan bidiyon da ya ɗora a shafinsu zai iya samun 0.5x$7.60×55%=N2.09 wannan tsarin an yi amfani da shi a shekarar 2013.

Shafin na YouTube yana iya ƙoƙarin ya ga ya hana mutane ɗora bidiyon da ba ka da hakkin mallaka, wato irin na satar fage wanda kusan da yawa daga cikin bidiyoyin da suke YouTube waɗanda suka ɗora shi ba su suke da haƙ

 

ƙin mallakar shi ba.

Shin daidai ne mutum ya saukar da Video a YouTube?

Babu laifi idan mutum ya saukar da bidiyo daga YouTube domin yayi amfani don karan-kansa ba tare da juyashi ba ko kuma ya canza shi zuwa wata hanya. Amma laifi shi mutum ya saukar da kowane irin bidiyo a YouTube sannan ya yi amfani da shi a wani gidan talabijin ko kuma ya gurza shi ko kuma domin sayarwa.

Kamar yadda kamfanin na google ya fadi a shafin shi na sharadin amfani da bidiyon YouTube sun rubuta kamar haka, “Ba a yarda kayi amfani da Video nan ba sai domin amfanin kanka, ba na neman kudi bane, ba za a diba ba (copy), ba sake gurzashi, ba rabashi, ba nuna shi a gidajen talabijin, ba yin kasuwanci da shi, kada ayi amfani da wani bangare nashi sai da izini rubutacce zuwa ga YouTube”. Daga jin irin wannan sharadi yake nuna mana cewar idan mutum zai saukar da bidiyo daga YouTube kuma yana son yayi amfani domin nishadantar da kansa ko kuma ilmantan da kansa, to babu laifi.

Haka idan muka dubi zuwa ga amfani da shi ta wadansu kafafe, sai muga hatta yadda mutanen mu suke saukar da bidiyo daga wannan gida kuma suyi ta gurzashi, wannan kai tsaye laifi ne. Shi ya sanya daga cikin dokokin amfani da shi, sun fadi cewar idan mutum ba zai yi amfani da intanet ba ne, ya kalla kai tsaye, to shima ba su yarda ya saukar da shi ba domin kallo.

Saukar da bidiyo daga YouTube yana kawo wa wannan kamfani cikas ga harkokin kasuwancin su. Mutane da dama su na yawan tambayar mu shin, irin waɗannan shafuka kamar google, ko facebook, ko YouTube mene ne ribarsu? Sai mu fada musu cewar shigar da muke yi suna amfani da shafukan su, shi ne ribar su, domin manyan kamfanoni na duniya suna yin la’akari da yawan mutanen da suke shiga dakuna a intanet, kuma wannan dalilin yake sanyawa a basu talla.

Mene ne dalilin da yasa ba maballin saukar da bidiyo kai tsaye a shafin YouTube?

Kamar yadda muka fadi cewar a shekarar 2014 kamfanin google ya sami ribar dalar Amurka biliyan 4 wanda yake daidai da Naira Biliyan Dari Tara (900,000,000,000) ta su bidiyoyin da ake kallo a shafin YouTube. Wannan ribar ta samu ne saboda talla da yake bayyana a jikin bidiyo lokacin da mutum yake kallo.

Wannan shi ne ma dalilin da ya sanya wani lokaci idan mutum yana son kallo a YouTube sai ya jira na ‘yan dakikoki biya domin kallon talla kafin ya baka zaɓin ko ka ci gaba da kallo ko kuma ka wuce zuwa ga shi bidiyon da ka nemi ka kalle shi. Matsalar nan ita ce, idan mutane suka sauke shi bidiyon kun ga babu yadda za ayi kamfanin su sami kudi, dalilin haka ya sanya su kamfanin basa so mutum ya ce zai saukar da shi.

Ko ba mu yi dogon bayani ba, kasan cewar da dukkanin bidiyoyin da suke cikin wayoyinmu za a barsu a shafukan da suke sai dai kawai mukalla a sama da kudaden da za su samu sai ya ninka wanda suka samu a shekarar 2014. Amma dai duk da haka mutane da yawa suna ta ƙoƙarin su ga yadda za ayi su saukar da wadannan bidiyoyi a kwamfutocinsu da wayoyin domin su iya amfana da su a wani lokaci.

Mene ne ya sa bidiyo yake da cin MB?

Dalili kuwa shi ne domin bidiyo hotuna ne aka tara su a wuri guda. Yadda abin ya ke shi ne, duk wani bidiyo da mutum ya gani tun daga dakika daya zuwa awanni daga hoto daya ne zuwa hotuna 25 zuwa hotuna 60. Idan ka duba na’urar daukan hoto misali Camera ta wayarka, zaka ga daga bayan an rubuta lamba a gaban lambar an rubata Pixel, misali 2 Mega Pixel. Wannan megapixel sinadari ne da ake auna kyau da girman da Kamara zata iya daukar hoto da shi.

Idan aka ce kamarar wayar ka ta na da 5-megapixel to ana son ka sani cewar wayar ka zata iya daukan hoto guda wanda sai an sami digo miliyan biyar a jikinshi. Shi daman Pixel a ilimin daukan hoto na nufin digo duga ko kuma rami guda da kala zai iya zama na hoto a cikinsa. Saboda haka, idan aka ce wayar mutum ko kuma kamarar shi tana daukar hoto mara motsi guda daya wanda ya kai nauyin 2Mb, to idan zata dauki bidiyon dakika guda sai ka hada 2mb x 25 = 120mb.

A takaice duk mafi yawan bidiyon da muke kallo suna da zubu iri biyu ne, PAL da NTSC, bidiyon da aka daukeshi da fasahar PAL a kwane dakika ana samun hotuna 25 ne, wanda kuma aka yi amfani da fasahar NTSC ana samun hotuna 29 zuwa 30 a kowane dakika guda. Ba a maganar cewar lokacin da kamarar take daukan hotunan tana kuna hadawa tare da sauti wanda shima yana da nasa nauyi.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya bidiyo ya ke nauyi kasancewar tarin hotuna ne da sauti a hade a wuri guda.

 

Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

Da Me Ake Amfani A Saukar Da Bidiyon Youtube A Kwamfuta Ko Kuma Wayoyin Hannu?

Ba zamu iya ƙididdigar yawan manhajoji manya da ƙanana da ake da su ba wurin samun saukin sauke bidiyo da suke kan shafukan intanet ko kuma shafin YouTube ba. Abin lura a nan shi ne, kasancewar duk lokacin da mutum zai shiga intanet, musamman shafin google ya rubuta wata tambaya ta neman sanin yadda mutum zai yi wani abu, amsosi daruruwa ne za su bayyana wanda idan mutum ba ya saba ba ne, sai ya rude ko kuma ya kidime, ya rasa wacce ce amsa ta gaskiya.

A wannan darasi ba za mu baku sunan manhaja ko guda ba, musamman manhajoji masu zaman kansu, saboda mafi yawansu ana biyan kudi ne wurin yin amfani da su, ko kuma a fake da su a cika maka kwamfuta da wadansu kananan manhajojin bogi wadanda za su fitine ka da cewar ko akwai virus a cikin kwamfutarka ko kuma tana tabiya ba cikin hanzari ba.

Akwai shafuka a intanet masu yawa waɗanda su aikinsu shi ne, idan mutum ya ziyarce su sannan ya ga wani bidiyo a intanet ya bashi sha’awa kuma ya na son ya saukar da shi sai ya kwafo link din bidiyo, ya daura a wancan shafin su kuma sai su bashi wani link din da zai yi amfani da shi ya saukar.

To suma irin waɗannan shafuka suna da yawa, kuma suma akwai abin lura, domin wadansu suna boye kananan manhajoji domin cutar da kwamfutocin mutane ko kuma wayoyinsu. Shi yasa a wannan gabar zan dauki shafi mafi sauki da kuma hanya mafi soyuwa domin in yi wa jama’a bayanai masu sauki ta yadda za a saukar da wannan bidiyo.

Iya Kudin ka iya Shagalin ka.

Daga cikin abin da masu sauke bidiyo suka fi ala’akari da shi musamman wadanda sababbin shiga ne, shi ne mene ne nauyin bidiyon da zan sauke? Wannan haka yake, domin duk lokacin da aka turowa mutum bidiyo ta WhatsApp sai ka ji yace wa zai sauke shi saboda ai ya kai MB (Megabyte) kaza.

To, lallai ya kamata duk wanda yake son ya sauke bidiyo a YouTube ya sani cewar MB na kuka, kuma wani lokacin ma kokawar da ya ke yi mai tsawo ce. Su dai YouTube suna da tsari na kyawun bidiyo tun daga 240p (prograssive scan) har zuwa 8K (Ultra High Definition), wanda wannan yake nuna mana cewar mutum zai iya lashe tun daga MB 3 zuwa abin da ya kai gig domin kallo ko kuma saukar da bidiyo daga YouTube.

Saboda haka ya danganci ya kake son kyau na bidiyon ka, idan kana son saukar da kyakkyawan bidiyo to ka sani kana bukatar MB da yawa, kuma iya yawan mintunan da bidiyon yake da shi, iya nauyin ko girman MB da zai iya lashewa.

Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

Duk da dai wannan hanyoyin da za mu fada ana iya amfani da su wajen saukar da kowane irin bidiyo ne mutum ya gani a intanet matukar zai iya kallonshi kai tsaye, amma zamu kebe wannan zuwa ga shafin YouTube sai dai kuma idan kana son yin amfani da shi a wani shafi sai ka yi amfani da hanyar da muka ambata.

Amfani da SaveFrom.Net Helper

Wannan wata ‘yafr karamar karin manhaja ce wacce ake karata a kowace browser wanda aka fi sani da (add-ons). Wannan ‘yar karamar manhaja tana daga cikin manhajojin saukar da bidiyo daga YouTube wanda ya fi kwanne shahara a yanzu. Ana amfani da wannan manhajar domin saukar da duk wani bidiyo da yake shafun YouTube, Facebook, Vimeo da wadansu shafuka sama da 140 ta hanyar taba maballo guda.

 1. Zaka shiga shafin ta wannan hanya (en.savefrom.net/user.php).
 2. Shafin ya bude zai baka wani babban maballi da aka rubuta (Download) sai kawai ka taba shi.
 3. Zai saukar da ita wannan manhaja kuma zai fahimci wace browser ka yi mafani da ita wurin sauke shi. Tunda mun ce wannan manhajar kari ce ga browser wato add-ons bata da girma.
 4. Da zarar ya gama saukarwa, sai ka bude wurin da ya saukar ko kuma ka taba shi ta manuniyar cewar ya gama sauka daga jikin browser dinka, yin haka zai bayyanar maka da allon tabbatar da cewar kai ne kake son ka girka (installing) wannan manhajar ta hanya laba maballin yes.
 5. Daga nan zai daura shi wannan add-ons din ta hanyar kara shi a kan kowace manhaja ta browsing, kamar Opera, FireFox, Chrome, Safari, Internet Explorer da dai duk wata browser da kake amfani da ita a cikin kwamfutar ka.
 6. Zai nemi ya kulle duk wata browser da take bude, domin ya tabbatar da cewar girkawar da ka yi ta zauna daidai, sannan ya sake bude shi.
 7. Duk bidiyon da kake son ka sauke kawai bude shi za ka yi ya fara nunawa (playing), yana farawa zaka ga wani karin maballin a gefen yawan mutanen da suka yi subscribing din page kafin yawan wadanda suka kalli biyon an rubuta download da alamar kibiya na kallon kasa sai kawai ka latsa shi.
 8. Idan kuwa an lika bidiyon ne a wani gida kamar wani ya kai shi shafin zumunta na facebook zaka ga ya kara maka wani dan karamin labule a sama yana fada maka tsarin saukar da bidiyon tun daga zari FLV, MP4 a nan ma zaka ga maballin download amma wannan karon daga sama gefe babu kuma kibiya a jikinshi sai ka taba shi, zai fito maka da irin nauyi ko kyau na bidiyon da kake son saukar sai kawai ya fara sauka.

Wadannan kyawu (quality) na bidiyon da zaka saukar zaka iya saukar da tun daga tsarin bidiyo na FLV 240p, MP4 360p, MP4 720p, MP4 480p, WebM 360p, 3GP 144p, 3GP 240p da kuma sauti mai tsarin MP4 128kbps. Wadannan sune irin tsarin bidiyo da zai saukar, kana da zabi daya daga ciki, iya yawan lamba iya girman MB da zai ci, misali mafi kankanta a cikinsu idan muka cire na sautin MP4 128kbps ne, 3GP144p shi ne mara nauyi, wanda kuma ya fi kowanne kyau da nauyi shine MP4 720p.

Amma idan mutum yana son saukar da bidiyo mai tsananin kyau wanda ake kiranshi da HD (High Definition) ko kuma sauti mai tsarin MP3 tunda shi sauti na MP4 ba kowace kwamfuta ko waya ce suke iya amfani da su ba.

Amfani da Ummy Video Downloader domin sauke HD ko MP3 daga YouTube

Ummy Video Downloader ita ma karamar manhaja ce wacce ake karata a jikin browser kamar SafeFrom.Net Helper sai dai ita tana baka damar saukar da bidiyo mai tsananin kyau High Defination da kuma sauti na MP3

 1. Zaka shiga shafin Ummy Video Downloader ta wannan hanya (ummy.com), sai ka taba maballin saukarwa (Download).
 2. Za ka jira ya gama sauka sai ka girka shi (installing) a cikin kwamfutar.
 3. Idan ka bude shafin na youtube kuma ka zakulo bidiyon da ka ke son saukarwa sai ka kwafe link din biyon ka bude manhajar Ummy Video Downloader sannan ka saka wannan link din zai baka damar saukar da dukkanin tsarin kyau na bidiyon da kake buka ciki har da High Defination da kuma MP3.
 4. Wani lokaci kuma zai baka dama ce a kasan bidiyon da ka bude a karkashen SaveFrom.Net Helper sai ka zabi HD ko MP3.

Amfani da SSYOUTUBE.COM

Wannan hanya tana daya daga cikin hanyoyin saukar da bidiyo a shafin YouTube da kuma sauran gidajen da ake ajiyar bidiyo a intanet. Ita wannan hanyar bata bukatar sauke kowace irin manhaja, kuma bata bukatar yin wani abu mai rikitarwa. Sai dai sharadi na farko shi ne:

 1. Ba za ka yi amfani da sananniyar manhajar bude YouTube ba misali idan kan amfani da wayar hannu kuma ka saukar da manhajar YouTube to ba zaka yi amfani da ita ba, za ka bude browser ce ka shiga YouTube kai tsaye.
 2. Ka bude bidiyon da kake son ka sauke.
 3. Daga saman inda ya ke nuna adireshin inda bidiyon yake sai ka share dagahttps://www. sai ka karaSS a wurin sai ka dannan maballin GO ko kuma Enter a jikin Keyboard dinka. Misali com/watch?v=M4w2uQVpTGM, sai ka mayar da shi ssyoutube.com/watch?v=M4w2uQVpTGM
 4. Da zarar ka yi haka wannan shafin zai fita daga shafin YouTube zai wuce kai tsaye zuwa SSYOUTBE.COM in da zaka ga shafin ya canza zuwa SafeFrom.Net nan take zai bayyanar maka da wannan bidiyo ya kuma baka damar saukar da kowane irin kalan bidiyo kake son saukarwa.

 Saukar da bidiyo daga kowane irin website

Idan ka ga wani bidiyo a wani website kuma kana son saukar da shi zaka iya amfani da wannan tsarin wurin saukar da shi wannan bidiyon da ma wadanda suke cikin wannan website ba tare da samun wata matsala ba.

 1. Ka bude shafin da akwai bidiyo a ciki
 2. Ba tare da ka sa ya fara nunawa ba, sai ka kara sfrom.net/ ko savefrom.net/ wannan ya sha banban da na ss domin na ss shi share http://www. a ke yi amma wannan shi kara shi ake yi a farkon http:// misalihttp://www.duniyarcomuter.com sai ya koma sfrom.net/http://www.duniyarcomputer.com ko kuma savefrom.net/http://www.duniyarcomputer.com
 3. Wannan zai bayyanar da dukkanin bidiyon da suke cikin wannan website din a shafin savefrom.net tare ba ka maballin saukar da bidiyon ba tare da ka sami wata matsala ba.

Saukar da bidiyo kai tsaye ta savefrom.net

Wannan shi ne hanya ta karshe da zamu nuna muku a cikin wannan darasi na yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube ba tare da wata manhaja ba.

 1. Zaka bude sharin savefrom.net ta hanyar bude shi ta browser dinka ka rubutahttp://www.savefrom.net
 2. Sai ka sake bude shafin ka na YouTube a wani falle na daban ko wata browser inda kana da sama da daya a cikin kwamfutarka ko kuma wayar ka, sai ka bude bidiyon da kake son saukarwa.
 3. Daga saman browser dinka, wurin address bar sai ka kwafe link din da bidiyon yake.
 4. Ka dawo wancan shafin da ka fara budewa na savefrom.net ka saka a cikin ramin da ake zuba link din sai ka danna maballin download.
 5. Nan take zai dauko maka bidiyon da yake cikin wancan shafin na YouTube, tare da kala-kalan nauyi da kyau da kake son saukarwa.

Wannan shi ne karshen darasin  da muka yi alkawari zamu kawo muku wanda ya shafi yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube, sannan wannan hanyoyi musamman hanya ta uku da hudu duk ana iya amfani da su a kwamfuta da kuma wayoyin komai da ruwanka. Kodayake a wani lokaci nan gaba kadan zamu lissafo muku wadansu manhajoji da ake amfani da su a saukar da bidiyo ta wayoyin hannu.

Muna fata za ayi amfani da wannan ilimi wurin saukar da abin da ya dace ba abubuwan da bai dace ba. Allah ka shaida mun kubuta daga duk wanda ya ya saukar da abin da ka haramta a kalla.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *