Yadda ake saukar da video daga YouTube (2) : Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

DARASI NA FARKO

Da Me Ake Amfani A Saukar Da Bidiyon Youtube A Kwamfuta Ko Kuma Wayoyin Hannu?

Ba zamu iya ƙididdigar yawan manhajoji manya da ƙanana da ake da su ba wurin samun saukin sauke bidiyo da suke kan shafukan intanet ko kuma shafin YouTube ba. Abin lura a nan shi ne, kasancewar duk lokacin da mutum zai shiga intanet, musamman shafin google ya rubuta wata tambaya ta neman sanin yadda mutum zai yi wani abu, amsosi daruruwa ne za su bayyana wanda idan mutum ba ya saba ba ne, sai ya rude ko kuma ya kidime, ya rasa wacce ce amsa ta gaskiya.

A wannan darasi ba za mu baku sunan manhaja ko guda ba, musamman manhajoji masu zaman kansu, saboda mafi yawansu ana biyan kudi ne wurin yin amfani da su, ko kuma a fake da su a cika maka kwamfuta da wadansu kananan manhajojin bogi wadanda za su fitine ka da cewar ko akwai virus a cikin kwamfutarka ko kuma tana tabiya ba cikin hanzari ba.

Akwai shafuka a intanet masu yawa waɗanda su aikinsu shi ne, idan mutum ya ziyarce su sannan ya ga wani bidiyo a intanet ya bashi sha’awa kuma ya na son ya saukar da shi sai ya kwafo link din bidiyo, ya daura a wancan shafin su kuma sai su bashi wani link din da zai yi amfani da shi ya saukar.

To suma irin waɗannan shafuka suna da yawa, kuma suma akwai abin lura, domin wadansu suna boye kananan manhajoji domin cutar da kwamfutocin mutane ko kuma wayoyinsu. Shi yasa a wannan gabar zan dauki shafi mafi sauki da kuma hanya mafi soyuwa domin in yi wa jama’a bayanai masu sauki ta yadda za a saukar da wannan bidiyo.

Iya Kudin ka iya Shagalin ka.

Daga cikin abin da masu sauke bidiyo suka fi ala’akari da shi musamman wadanda sababbin shiga ne, shi ne mene ne nauyin bidiyon da zan sauke? Wannan haka yake, domin duk lokacin da aka turowa mutum bidiyo ta WhatsApp sai ka ji yace wa zai sauke shi saboda ai ya kai MB (Megabyte) kaza.

To, lallai ya kamata duk wanda yake son ya sauke bidiyo a YouTube ya sani cewar MB na kuka, kuma wani lokacin ma kokawar da ya ke yi mai tsawo ce. Su dai YouTube suna da tsari na kyawun bidiyo tun daga 240p (prograssive scan) har zuwa 8K (Ultra High Definition), wanda wannan yake nuna mana cewar mutum zai iya lashe tun daga MB 3 zuwa abin da ya kai gig domin kallo ko kuma saukar da bidiyo daga YouTube.

Saboda haka ya danganci ya kake son kyau na bidiyon ka, idan kana son saukar da kyakkyawan bidiyo to ka sani kana bukatar MB da yawa, kuma iya yawan mintunan da bidiyon yake da shi, iya nauyin ko girman MB da zai iya lashewa.

Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

Duk da dai wannan hanyoyin da za mu fada ana iya amfani da su wajen saukar da kowane irin bidiyo ne mutum ya gani a intanet matukar zai iya kallonshi kai tsaye, amma zamu kebe wannan zuwa ga shafin YouTube sai dai kuma idan kana son yin amfani da shi a wani shafi sai ka yi amfani da hanyar da muka ambata.

Amfani da SaveFrom.Net Helper

Wannan wata ‘yafr karamar karin manhaja ce wacce ake karata a kowace browser wanda aka fi sani da (add-ons). Wannan ‘yar karamar manhaja tana daga cikin manhajojin saukar da bidiyo daga YouTube wanda ya fi kwanne shahara a yanzu. Ana amfani da wannan manhajar domin saukar da duk wani bidiyo da yake shafun YouTube, Facebook, Vimeo da wadansu shafuka sama da 140 ta hanyar taba maballo guda.

 1. Zaka shiga shafin ta wannan hanya (en.savefrom.net/user.php).
 2. Shafin ya bude zai baka wani babban maballi da aka rubuta (Download) sai kawai ka taba shi.
 3. Zai saukar da ita wannan manhaja kuma zai fahimci wace browser ka yi mafani da ita wurin sauke shi. Tunda mun ce wannan manhajar kari ce ga browser wato add-ons bata da girma.
 4. Da zarar ya gama saukarwa, sai ka bude wurin da ya saukar ko kuma ka taba shi ta manuniyar cewar ya gama sauka daga jikin browser dinka, yin haka zai bayyanar maka da allon tabbatar da cewar kai ne kake son ka girka (installing) wannan manhajar ta hanya laba maballin yes.
 5. Daga nan zai daura shi wannan add-ons din ta hanyar kara shi a kan kowace manhaja ta browsing, kamar Opera, FireFox, Chrome, Safari, Internet Explorer da dai duk wata browser da kake amfani da ita a cikin kwamfutar ka.
 6. Zai nemi ya kulle duk wata browser da take bude, domin ya tabbatar da cewar girkawar da ka yi ta zauna daidai, sannan ya sake bude shi.
 7. Duk bidiyon da kake son ka sauke kawai bude shi za ka yi ya fara nunawa (playing), yana farawa zaka ga wani karin maballin a gefen yawan mutanen da suka yi subscribing din page kafin yawan wadanda suka kalli biyon an rubuta download da alamar kibiya na kallon kasa sai kawai ka latsa shi.
 8. Idan kuwa an lika bidiyon ne a wani gida kamar wani ya kai shi shafin zumunta na facebook zaka ga ya kara maka wani dan karamin labule a sama yana fada maka tsarin saukar da bidiyon tun daga zari FLV, MP4 a nan ma zaka ga maballin download amma wannan karon daga sama gefe babu kuma kibiya a jikinshi sai ka taba shi, zai fito maka da irin nauyi ko kyau na bidiyon da kake son saukar sai kawai ya fara sauka.

Wadannan kyawu (quality) na bidiyon da zaka saukar zaka iya saukar da tun daga tsarin bidiyo na FLV 240p, MP4 360p, MP4 720p, MP4 480p, WebM 360p, 3GP 144p, 3GP 240p da kuma sauti mai tsarin MP4 128kbps. Wadannan sune irin tsarin bidiyo da zai saukar, kana da zabi daya daga ciki, iya yawan lamba iya girman MB da zai ci, misali mafi kankanta a cikinsu idan muka cire na sautin MP4 128kbps ne, 3GP144p shi ne mara nauyi, wanda kuma ya fi kowanne kyau da nauyi shine MP4 720p.

Amma idan mutum yana son saukar da bidiyo mai tsananin kyau wanda ake kiranshi da HD (High Definition) ko kuma sauti mai tsarin MP3 tunda shi sauti na MP4 ba kowace kwamfuta ko waya ce suke iya amfani da su ba.

Amfani da Ummy Video Downloader domin sauke HD ko MP3 daga YouTube

Ummy Video Downloader ita ma karamar manhaja ce wacce ake karata a jikin browser kamar SafeFrom.Net Helper sai dai ita tana baka damar saukar da bidiyo mai tsananin kyau High Defination da kuma sauti na MP3

 1. Zaka shiga shafin Ummy Video Downloader ta wannan hanya (ummy.com), sai ka taba maballin saukarwa (Download).
 2. Za ka jira ya gama sauka sai ka girka shi (installing) a cikin kwamfutar.
 3. Idan ka bude shafin na youtube kuma ka zakulo bidiyon da ka ke son saukarwa sai ka kwafe link din biyon ka bude manhajar Ummy Video Downloader sannan ka saka wannan link din zai baka damar saukar da dukkanin tsarin kyau na bidiyon da kake buka ciki har da High Defination da kuma MP3.
 4. Wani lokaci kuma zai baka dama ce a kasan bidiyon da ka bude a karkashen SaveFrom.Net Helper sai ka zabi HD ko MP3.

Amfani da SSYOUTUBE.COM

 Wannan hanya tana daya daga cikin hanyoyin saukar da bidiyo a shafin YouTube da kuma sauran gidajen da ake ajiyar bidiyo a intanet. Ita wannan hanyar bata bukatar sauke kowace irin manhaja, kuma bata bukatar yin wani abu mai rikitarwa. Sai dai sharadi na farko shi ne:

 1. Ba za ka yi amfani da sananniyar manhajar bude YouTube ba misali idan kan amfani da wayar hannu kuma ka saukar da manhajar YouTube to ba zaka yi amfani da ita ba, za ka bude browser ce ka shiga YouTube kai tsaye.
 2. Ka bude bidiyon da kake son ka sauke.
 3. Daga saman inda ya ke nuna adireshin inda bidiyon yake sai ka share daga https://www. sai ka kara SS a wurin sai ka dannan maballin GO ko kuma Enter a jikin Keyboard dinka. Misali https://www.youtube.com/watch?v=M4w2uQVpTGM, sai ka mayar da shi ssyoutube.com/watch?v=M4w2uQVpTGM
 4. Da zarar ka yi haka wannan shafin zai fita daga shafin YouTube zai wuce kai tsaye zuwa SSYOUTBE.COM in da zaka ga shafin ya canza zuwa SafeFrom.Net nan take zai bayyanar maka da wannan bidiyo ya kuma baka damar saukar da kowane irin kalan bidiyo kake son saukarwa.

 Saukar da bidiyo daga kowane irin website

Idan ka ga wani bidiyo a wani website kuma kana son saukar da shi zaka iya amfani da wannan tsarin wurin saukar da shi wannan bidiyon da ma wadanda suke cikin wannan website ba tare da samun wata matsala ba.

 1. Ka bude shafin da akwai bidiyo a ciki
 2. Ba tare da ka sa ya fara nunawa ba, sai ka kara sfrom.net/ ko savefrom.net/ wannan ya sha banban da na ss domin na ss shi share http://www. a ke yi amma wannan shi kara shi ake yi a farkon http:// misali http://www.duniyarcomuter.com sai ya koma sfrom.net/http://www.duniyarcomputer.com ko kuma savefrom.net/http://www.duniyarcomputer.com
 3. Wannan zai bayyanar da dukkanin bidiyon da suke cikin wannan website din a shafin savefrom.net tare ba ka maballin saukar da bidiyon ba tare da ka sami wata matsala ba.

Saukar da bidiyo kai tsaye ta savefrom.net

Wannan shi ne hanya ta karshe da zamu nuna muku a cikin wannan darasi na yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube ba tare da wata manhaja ba.

 1. Zaka bude sharin savefrom.net ta hanyar bude shi ta browser dinka ka rubuta http://www.savefrom.net
 2. Sai ka sake bude shafin ka na YouTube a wani falle na daban ko wata browser inda kana da sama da daya a cikin kwamfutarka ko kuma wayar ka, sai ka bude bidiyon da kake son saukarwa.
 3. Daga saman browser dinka, wurin address bar sai ka kwafe link din da bidiyon yake.
 4. Ka dawo wancan shafin da ka fara budewa na savefrom.net ka saka a cikin ramin da ake zuba link din sai ka danna maballin download.
 5. Nan take zai dauko maka bidiyon da yake cikin wancan shafin na YouTube, tare da kala-kalan nauyi da kyau da kake son saukarwa.

Wannan shi ne karshen darasin  da muka yi alkawari zamu kawo muku wanda ya shafi yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube, sannan wannan hanyoyi musamman hanya ta uku da hudu duk ana iya amfani da su a kwamfuta da kuma wayoyin komai da ruwanka. Kodayake a wani lokaci nan gaba kadan zamu lissafo muku wadansu manhajoji da ake amfani da su a saukar da bidiyo ta wayoyin hannu.

Muna fata za ayi amfani da wannan ilimi wurin saukar da abin da ya dace ba abubuwan da bai dace ba. Allah ka shaida mun kubuta daga duk wanda ya ya saukar da abin da ka haramta a kalla.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 1. A gaskiyan lamari babu abin da za mu ce, sai dai Allah ya saka muku da alheri, Allah kuma ya kara muku basira amin. Baya ga haka zan so ace kuna da wani reshe ko makarnta wadda za ku dinga bada darussa kan Computer. Domin ni a ganina hakan zaisa mutane irina yin rijista don karawa da wannan ilmi mai mutukar faida da daraja. Da fatan mafarkina wataran zai kasance gaskiya. Duniyar Computer 4 ever.