Yadda Ake Kashe Kwamfuta Aduk Lokacin Da Ka Ke So Batare Da Ka Taɓa Ta Ba (AUTOMATIC SHUTDOWN)

dalibai-a-duniyar-computerAkwai hanyoyi guda biyu da za mu yi amfani da su wajen sanya Kwamfuta ta kashe kanta da kanta (automatic shutdown) ;

HANYA TA FARKO 1:- Ka yi (right click) wato ka taɓa ɓangaren dama na mouse a kan desktop a wajen da ba komai, waɗansu zaɓi za su bayyana sai ka zaɓi (New), bayan ka taɓa new waɗansu zaɓin zai sake fitowa sai ka zaɓi (SHORTCUTS), zai buɗe maka wani shafi akwai wajen rubutu sai ka rubuta (shutdown -s -t 3600) ba tare da wannan baka biyun ba, sai ka taɓa (NEXT) sai kuma ka taɓa (FINISH).

Icon zai bayyana a kan desktop dauke da sunan shutdown sai kai double click a kan sa, shi ke nan ka ba wa kwamfutarka umarni ta kashe kanta a lokacin da ka saka mata.

KARIN BAYANI;- 3600 yana matsayin awa ɗaya a lissafin daƙiƙoƙi domin 60secs × 60mins = 3600secs. Za ka iya amfani  da duk adadin mintin ko awa da kake so. Misali ; 900secs = 15mins, 1800= 30mins da dai sauran su .

YADDA AKE TSAYAR DA LOKACIN DOMIN TSAYAR DA UMARNIN DA KA BA TA KA DA TA KASHE KANTA

A sake kirkirar wani shortcut ɗin sai a rubuta (shutdown -a ) ba tare da ka sa wannan alamar baka ɗin ba, sai ka taɓa NEXT sai FINISH icon zai sake bayyana da shutdown(2) sai kai double click a kan sa shi kenan ka tsayar da lokacin da ka sa.

HANYA TA 2:- Ka taɓa (start menu)  sai ka rubuta (shutdown -s -t 3600) shi ma ba tare da wannan alamar bakan ba sai ka danna (ENTER) Kwamfuta ta san umarnin da ka ba ta, na ta kashe kanta idan lokacin da ka ba ta ya yi.

Shi ma idan kana so ka tsayar da lokacin sai ka sake taɓa (START MENU) sai ka rubuta (shutdown -a) shi ke nan ka tsayar da lokacin.

 

KAMAL BALA ISAH, Dalibi ne a Makarantar Duniyar Computer Online za a iya samunsa a lamba.41 MANLADAN

ƙaramar hukumar DALA   jahar KANO, GSM:08029457921

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *