YADDA AKE BUDE IMEL A YAHOO!

Kasancewar yawan bukatar da ake da ita wanda jama’a su ke yi na tambayarmu ya ake bude imel na yahoo ko google ko kuma msn muka ga ya dace mu yi maku bidiyo na musamman guda biyu wadanda za su koyar da ku yadda ake kirkiran wadannan akwatuna na imel.

Kamar yadda bayanai suka gabata a darasin mu me taken MENE NE IMEL a wancan darasin mu yi cikakken bayanai kuma gamsasshe domin sanin mene ne imel me kuma muhimmancin kirkiransa a wurin mu.

To a wannan bidiyon zamu koyar da yadda za a kirkiri imel amma kuma na kamfanin yahoo. A bidiyo mai zuwa kuma zamu koyar da yadda ake bude imel da kamfanin google

Ga duk me son ya sauke wannan bidiyo domin ya kalle shi a wayarsa ko a kwamfutarsa zai iya saukarwa ta wannan hanyoyi guda biyu.

1) Masu Kwamfuta da Ipad da Iphone ga nasu DOWNLOAD

2) Masu kanana wayoyi ga nasu DOWNLOAD

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *