Ya kamata in damu da Hackers kuwa?

Kalmar Hackers ta wayaita a bakin samari da ‘yan mata masu harkar computer da kuma sarrafa ta a wannan zamani, wannan kalma ta yawaita a kusan ko wane lungu da sako na duniya, kasantuwar yadda kowa ya ke daukar wannan kalmar, amma a yammacin duniyar da kuma nahiyar turai kowa na jin tsoron hackers kuma ba yason a jingina ita wannan kalmar a gare shi. Hasalima duk wanda ya san cewar computer shi bata da ingantaccen Antivirus software a cikin babu abinda yake jima Kwamfutarshi tsoro kamar Hackers!

Su waye Hackers a ilmance?

Zaka ji da zarar mutum ya san computer ko kuma ya iya sarrafata sosai sai kaji a na kiran shi da kalmar harcker. A gaskiya kalmar “hacker” tana da ma’anoni da dama da kuma fassara iri-iri, amma idan aka dawo akan harkar da ta shafi computer kuma kana son ka yi maganar hackers da computer to bai wuce ta basu ma’ana guda biyu ba wadanda su wadannan ma’anoni biyun duk kana bukatar saninsu. Kamar yadda aka fasara kalmar hacker a wani dictionary mai suna “Merriam-Webster” “Hacker kwararren masanin ilimin sarrafa computer (programmer). Shi kuwa wannan ma’ana da suka ba da ta kunshi kusan mutane da dama masu amfani da computer amma kuma wadanda ba a tunanin zasu iya cutar da wani.

Amma ma’ana ta biyu tafi ta da hankali matuka, domin Hacker shine mutumin da ya shiga cikin Kwamfutar mutum ta barauniyar hanya domin ya saci wasu mahimman bayanan shi ko kuma ya yi maka ta’adi”. Idan muka fuskanci wannan ma’ana ta biyu yana nuna mana cewar dukkanin wani abu da hacker yake kokarin yi shine ta’addanci tare da Kwamfutar mutane ta hanyar da kuma barna, domin hakan na faruwa ba tare da sanin mai amfani da Kwamfutar ba.

Yaya Hacker suke yin Hacking?

Daya daga cikin hanyoyin da hackers suke yin amfani da ita domin su iya shiga cikin Kwamfutar mutum shine ta yin amfani da Malware. Malware wani dan karamin software ne ko kuma program da ake sa ran zai iya barka dukkan wata  ta kariya a cikin Computer domin yayi ta’adi.

Wasu hackers sukan kirkiri wadansu kananan program domin nishadi wanda ajikin wannan dan karamin program din sai su saka mishi dan karamin malware domin shi wannan malware din ya rika yin barna a cikin computer ba tare da mai Kwamfutar ya sani ba. Wasu kuma wadanda mugunta suka saka a gabansu sai su kirkiri malware wanda shi babu abinda yake yi face ya tattaro mahimman bayanai da kake rubutawa ko kuma ka ajiye a cikin Kwamfutarka daga bisani sai ya maidowa da wanda yayi shi wadannan bayanai, shi kuma da wannan bayanai zai yi amfani wajen shiga Kwamfutarka har ya sace maka kudadenka da kuma wasu mahimman kayanka. Irin wadannan malware wadanda suke satar kalmomin sirrin mutum (password) ko kuma dukkan wani maballi (keyboard) da ka latsa suna daukashi suna aikawa da hackers a na kiranshi da “keylogger”.

Ya ake Malware yake shiga Kwamfuta?

Mafi yawacin malware da suke shiga cikin computer mutane ba su sanin lokacin da suke shiga. Wannan kuwa yana faruwane a lokacin da ka shiga internet domin yin downloading wani abu ko kuma ka bude sakon imel da a cikinshi akwai malware tare da shi.

Shi malware sau tare yana zuwa ne a sakon imel da bakasan wanda ya aiko maka da shi ba, ma’ana mafi yawancin sako na banza da wofi da soki burutsu (junk ko spam) da ake aikowa da shi su suke tattare da malware. Haka Malware yana iya shiga Kwamfutar mutum idan mutum ya shiga website domin yin downloading, kawai abinda hackers suke so shine da zarar ka latsa link domin bude wani shafi ko kuma saukar da wani abu sai malware ya fado cikin computer kawai, ba tare da ka sani ba.

Me zai faru idan Kwamfuta ta ta fada hannun Hackers?

Matsalar guda ce yana da wahala a iya gane wane ne ya kirkiri malware da yayi ta’adi a Kwamfutarka, ko da yake wani lokaci hukumomin sukan yi bincike mai zurfi har su gano wanda ya kirkiri shi wannan malware din. Sai dai idan har aka yi rashin sa’a ka fada hannu to babu wanda zai gyara maka ita Kwamfutar sai dai kai ka cire kudi daga naka aljihun ka biya, idan kuwa kwashe maka kudi aka yi to babu wata hukuma da zata dauki alhaki. Shi yasa make da mahimmanci kasan yadda zaka bi ka hana Hackers shiga kwamfutar ka.

To ya za ayi in tsare Kwamfuta ta daga Harckers?

Hanya mafi inganci da zaka bi domin kare Kwamfutarka daga matsaloli irin wannan shine ka daurawa Kwafutarka software wadanda aka yi su musamman domin lura da malware, ko kuma wadanda suke tare malware idan ka shiga website ko kuma ka bude imel da ba ka amince da wanda ya aiko maka da shi ba. Wadannan program ba wadansu ba illa ant-virus software ko kuma anti-malware software. Mafi ya yawan irin wadannan software basu da tsada kuma suna da saukin sakawa a cikin computer kuma kamfanonin suna kokari matuka wajen lura da irin wadannan cututtuka da suke iya shiga Kwamfutar mutum. Su wadannan anti-virus software suna iya binciken kwamfutar ka su gano maboyar malware ko virus kuma su fitar da shi ba tare da kai mai Kwamfutar ka sani ba. Saka irin wadannan anti-virus software na da kyau mutum ya lura koma ya sani cewar arha bata ado, kuma mafi yawancin anti-virus na kyauta ko kuma wadanda basu shaharaba basu iya kare Kwamfutarka, ko kuma wasu ma sukan koma makamin da su hackers suke amfani da shi wajen shigowa computer. Ka saka sanannen anti-virus, kuma shahararre, sannan wanda kuma yana na ilimin virus sama da miliyan tara, domin tsakanin virus da Trojans da malwares ana da sama da miliyan tare da wani abu

Daga karshe muna son ka sani kai mai karatun Hackers gaskiya ne kuma suna nan suna kokarin yadda zasu yi su kifar da kai da kuma Kwamfutarka, saboda haka sai muyi hattara!

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Madalla, da wannan karin bayani da akwai wa mutane.

    Hackers a hausance mukan kirasu da ‘Yan Dandatsa, hacking kuma Dandatsanci. (Fassarar Prof. Abdallah)

    Ma Assalam.