Ya Girman Microsoft Excel 2010 Yake?

Wannan ita ce ta Malam Usman Namaibindiga ya rubuto, kuma lallai yana da kyau al’umma su fahimci cewar idan akwai wani program da ake amfani da shi a Windows da aka sami nasarar yinshi babu kamar MS Excel akwai dalilai da dama, amma yanzu dangane da amsar da Namaibindiga ya yi: wato falle guda na Excel idan za ka bude shi za ka gan shi da gida-gida kamar gidan suga, to wannan gidaje a cikin su ake yin amfani da shi, to idan ka dauko Calculator ka tara 16,384 X 1,048,567 shi ne zai baka 17,179,869,184 wato wannan shi ne yawan ramukan da yake da shi. Ina kuwa son mai karatu ya gane cewar wannan shafi guda ke nan na Excel za ka iya kara shafuka iya yawan da kake so.
Idan kuwa mutum yana amfani da monitor da yake da Resolution 1600×1200 idan yana son yaga takardar shi ta excel guda daya wato kowani rami ya fito a cikin screen guda to sai ya samo monitor guda Miliyan hudu da dubu dari shidda za su iya fito da dukkanin ramuka wannan shafi. Idan kuma aka ce maka ka shigar da harafi daya-daya a cikin kowane ramin da ke cikin worksheet na excel guda kamar ka rubuta 1 a cikin kowane rami to sai ka yi shekaru dari biyar kafin ka kammala cike wadannan ramuka. Idan kuwa har ka samu ka kai shekarun ka gama cika shi, to idan kana bukatar takarda domin ka fitar da wannan aiki a cikin A4 paper size, to kana bukatar falle har miliyan talatin da shida, wanda idan aka jera su sun fi tsawon meter 12,000 na kafa.
Wannan a takaice shi ne girman takarda guda na Microsoft Excel, wanda a cikin shi wannan Excel babu wani lissafi na duniyannan ba ba za ka iya yi a ciki ba. Sai dai kawai a ce mutum bai san yadda zai sarrafa shi ba. IDAN KAJI AN CE CALCULATOR HUTA To EXCEL KE NEN

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *