Windows 10: Mahajar da zata jima tana sheke ayarta!

Ana sa rai yau 29 ga watan Yuli 2015 shahararren kamfanin nan da yake kera manhajoji na ƙasar Amurka Microsoft sai bayyanar da sabuwar Babbar Manhaja (Operating System) wanda mutane suka dade suna tsumaya mai suna Windows 10.

A cikin yanayi irin na ban mamaki wannan manhajar ta kaucewa duk wani zato da tsammani da mutane masu rade radin suna ko ginin manhaja, na cewar tunda babban manhajar su ta karshe ita ce Windows 8 to sun san dole ma Windows 9 shi ne mai biyo wa.

Ba wannan ba ne abin da kamfani na Microsoft ya yi na ban mamaki ba, daya daga cikin abu da ya baiwa mutane mamaki shi ne yadda kamfanin ya dau alwashi cewar duk wanda yake da manhajar Windows 7 ko Windows 8.1 a kan na’urarsa zai sami wannan manhajar kyauta ba tare da ya biya sisin kwabo ba. Duk da irin son kudi da mutane suke gani cewar kamfanin na Microsoft ya na da shi amma a wannan karon ya baiwa mara da kunya.

Ko da yake, wadansu masana suna ganin cewar kamfanin yayi haka ne saboda barazana da ya ke fuskanta a kasuwar manhajoji ta duniya da kuma yadda wannan shahararren kamfanin mai suna Google ya ke ta kara kutsa kai cikin harkokin manyan manhajoji wacce babban manhajar nan ta Android ta kasance ta na ta samun karbuwa a wurin kamfanonin da suke kera kayan kwamfuta.

Amma ba a nan gizo ke sakar sa ba, domin aƙwai wadansu sababbin canje-canjen da Windows 10 zai zo da shi wanda ana ganin lallai wannan canjin zai sake habako da kasuwar Microsoft da kuma samun karbuwa a duniya baki daya.

Mafi girman abin da kamfanin na Microsoft suka yi shi ne na ganin sun hade babbar manhajarsu da kananan manhajojin da suke yin aiki a kananan na’urori musamman woyoyin komai da ruwanka. Haka daga cikin abin jin dadi shi ne yadda kanfanin ya sanya manhajar ta Windows 10 ta kasance da daya tamkar da dubu a wurin shirya kayayyakin ka, hada dada hotuna da hotuna masu motsi, da rubuce-rubucenka, da karatuka ko wakokin sauti a wuri guda.

Windows 10 Kyauta: Wannan shi ne babban canji da aka samu a wurin shigowar wannan manhaja domin kasancewarta kyauta zai tabbatar da cewar duk wata kwamfuta da ke aiki tare da manhajar Windows tana aiki da babban manhaja ingantacciya ba ta fasakwauri ba. Wanda suke da kwamfuta mai Windows 7 da Windows 8.1 da zarar kamfanin ya saki wannan manhajar zasu iya sauke shi kai tsaye daga babban shafin na Microsoft.

Wannan saukewar ya takaitu ne kawai ga wadanda suke amfani da ingantacciyar babbar mahaja da Windows 8 ko 7 da take cikin ita kwamfutar, amma ga wadanda suke da manhajojin da 7 ko 8 ba, su suna da buƙatar su siya wannan manhajar wacce take kamawa daga N23,000 har zuwa N46,000 ya danganci da wani tsari na Windows kake amfani da shi.

Su kansu wadanda suke da Windows XP ko Vista su sani cewar Windows 10 ba ya canzuwa kai tsaye a na’urorin su (upgrading) kamar yadda zai yiwu kai tsaye ya canza kansa ga mai Windows 7 ko 8. Masu Windows XP da Vista zasu iya saka windows 10 ta hanyar goge tsohon wannan Windows din zuwa saka sabon Windows 10

Ga wadanda kuma suke amfani da manhajar Windows ta fasakwauri su zasu iya samun ita wannan manhajar amma kuma za su sami gargadi da zai riƙa bayyana a gefen dama na kasan ita manhajar yana fadakar da kai cewar lallai wannan manhajar ba ta asali ba ce.

Ita wannan sabuwar manhaja ta Windows 10 tana iya hawa kowace irin na’ura da ta mallakin karfin kayan aiki da take buƙata kama daga girman RAM da Processor wannan tsarin yana aiki a kwamfuta haka yana aiki a wayar komai da ruwanka.

Ga irin sinadarai da kwamfutarka take buƙata kafin Windows 10 ya iya shiga cikin ta:-

  • 1 gigahertz (GHz) ko wanda ya fishi
  • RAM: 1 gigabyte (GB) (32-bit) ko 2 GB (64-bit)
  • A kalla aƙwai sararin 16 GB a babbar ma’ajiyar ta (Hard Disk)
  • Graphics card: Microsoft DirectX 9 graphics device tare da WDDM driver
  • Kana da akwatin Imel na Microsoft sannan kana da damar shiga Internet.

Sannan yana da kyau mu sani cewar wannan damar samun wannan garabasar windows 10 na kyauta shekara gudace kacal duk wanda bai samu mallakar wannan manhajarwa har bayan shekara guda to lallai zai biya kafin ya mallake ta.

A rubutun mu na gaba zamu kawo muku abubuwa muhimmai da Windows 10 yake da su.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *