Windows 10: Abubawa 10 Muhimmani da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Mutane da da ma sun sami sabon Windows 10 da ya kasance manhajar da ake ta cece-kuce a kanta, masana da kuma masu sa ido a kan harkokin yau da kullum a ɓangaren manhajoji a yanzu dai suna ta san barka da wannan sabuwar manhaja.

Mu kan mu a Duniyar Computer muna daga cikin mutane ƙalilan da suka fara amfani da wannan manhaja kusan watanni hudu da suka wuce. Wacce muka yi amfani da ita wacce kamfanin Microsoft ya ke baiwa masana harkar kwamfuta domin su gwada su kuma basu shawarwari da ƙorafi a kai kafin a saki wacce kowa da kowa zai yi amfani da ita.

Kamar yadda muka alƙawurranta muku a cikin muƙalar mu ta (Windows 10: Mahajar da zata jima tana sheke ayarta) cewar za mu bayyanar muku da waɗansu muhimman canje-canjen da wannan sabuwar manhaja ta Windows 10 take tafe da shi.

Ga jerin sababbin canje-canjen da za a samu tare da Windows 10.

Windows 10 Kyauta

Wannan shi ne babban canji da aka samu a wurin shigowar wannan manhaja domin kasancewarta kyauta zai tabbatar da cewar duk wata kwamfuta da ke aiki tare da manhajar Windows tana aiki da babban manhaja ingantacciya ba ta fasakwauri ba.

Start Menu

Kamar yadda da yawa daga cikin waɗanda suka guji amfani da Windows 8 suke fada cewar ba zai yiwu ba ace sun saba da Start Menu ace haka nan rana guda a neme shi a rasa. Cire wannan Start Menu ya kawowa Windows 8 koma baya sosai a inda mutane da dama suka gwammace su koma Windows 7 kasancewar shi yana da Start Menu a jikinsa. To madalla da sauraran koke-koken jama’a da kamfanin Microsoft suka yi domin ya dawo da wannan maɓalli da yake bayar da sama mutum ya buɗe manhajojin da suke cikin kwamfutar sa ba tare da ya shiga Welcome Screen ba kamar yadda yake a Windows 8 ko Windows 8.1.

Wani abun jin dadi yadda kamfanin Microsoft ya sake kyayata Start Memu ta yadda da zarar ka taba shi, za ka ga ya buɗe tare da jerin waɗansu shafuka da za ka iya shirya abubuwan da kake son ka riƙa buɗewa kodawane lokaci. Abin sai wanda dai ya gani.

Cortana

Wannan wata manhaja ce da take yiwa kamfanin Google barazana, sai gashi a wannan karon ta biyo Windows 10. Mene ne aiki ta? Tana taimaka wa mai amfani da Windows 10 wurin samun sauƙin yin bincike a cikin na’urarsa. Ta hanyar da ake amfani da ita kuwa shi ne ta furta kalmar “Hey Cortana” kana faɗin haka duk abin da ka fadi zai rubuta a jikin akwatin binciken ta, sai ta fara bayyanar maka da amsa ba tare da taba keyboard koMouse ba. Za ta iya binciko duk wani abu dake cikin kwamfutar, kama daga aikace-aikacen ka, hotuna da Video da manhajoji kai har zata iya tsallakawa intanet ta zaƙulo amsar abin da kake neman ba tare da taba wani abu daga jikin ta ba. misali za ka iya tambayar ta da harshen Turanci “Show me photos from December” ma’ana nuna mini hotunan da aka saka miki daga watan Disamba ba tare da bata lokaci ba duk wani hoto da aka saka a cikin wannan kwamfutar a wannan watan za su fito. Wannan sabon manhaja taCortana za a iya samunta ne a jikin Taskbar duk da an yi ta da rami mai tsawo amma kuma kana da damar rage ta daga tsawo zuwa hoton da ke nuna alamarta kawai.

Edge Browser

Wannan ita ce sabuwar manhajar buɗe shafukan intanet da kamfanin Microsoft ya mayar da hankali a wannan sabon Windows din. Duk da har yanzu za ka iya samun Internet Explorer amma kuma kamfanin ya ce wannan sabuwar manhaja ta Edge, manhaja ce da zata yi gogayya da manhajojin buɗe shafukan Internet kamar su Google Chrome daMozilla Firefox waɗanda su ne suke gogayya da Internet Explorer da kuma zarra da suka yi mata na ganin suna tafiya da sabon tsarin gina shafukan Internet na HTML5. Amma a wannan karon ita wannan sabuwar browser ta Edge an soma gina ta ne daga farkon mazubin HTML5 sannan kuma an ƙara mata wani irin sinadari wanda zai iya baiwa mai amfani da ita damar ɗaukar hoton shafin da yake ciki, ya yi rubutu a kansa ko kuma ya saka wata alama da alƙalin rubutun na zane wanda ake amfani da shi a kwamfuta, ko ma dai ya yi amfani da wannan shafin domin ya karantar da wani abu da ya gani ba tare da yin amfani da karin wata manhaja ba. Baya da cire masa maballin Home da aka yi, duk da haka yana iya baka damar ajiye shafin da ka buɗe a matsayi  favourite da kuma ajiyar shafuka domin idan babu Internet a yi buɗe su. Sannan kuma Edge bata nauyin buɗe shafukan intanet, haka kuma tana da sauri sosai.

Task switcher

 

Mutane da yawa su san cewar idan mutum ya taɓa maɓallin Alt da Tab da suke jikinkeyboard ɗin shi a lokaci guda zai bashi damar canja fito da buɗedden Window da wani ya danne shi ba zuwa sama ba. Misali lokacin da mutum ya buɗe manhajoji sama da biyu a lokaci guda ɗaya ce kawai za ka iya yin aiki da ita lokaci guda idan kana son ka koma ɗayar sai ka yi amfani da Mouse ka taɓa ɗaya ta buɗe. To, amfani da Alt+Tab a lokaci guda zai baka damar fito da wanda yake ɓoye ba tare da ka taba Mouse ɗin ka ba. To Windows 10 ya zo da ɗan ƙaramin maɓalli a ƙasan shi da zai baka damar idan ka taɓa shi zai maka aikin da Alt+Tab yake yi a lokaci guda. Maimakon raba fuskar kwamfutarka gida biyu da kake iya yi a Windows 8, a Windows 10 kana da damar raba Screen din ka kusan gida hudu kuma ka yi aiki da su a lokaci guda.

Taskbar

kamar yadda muka sani tunda Cortana ta na jikin Taskbar ne ga kuma manhajoji da mutum ke iya liƙa su a jikinsa,  haka kuma ga Tray dake gefen shi, wato inda muke ganin agogon kwamfuta da alamar karawa da rage sauti, abin zai iya zama ruɗu ga mutum idan aka ce ga kuma wata manhajar a kunne domin yawa da tarkace da ke jikin Taskbar. Amma a Windows 10, sun yi wani sabon canji na baka damar mayar da kowane irin abu da ke jin Taskbar mai tsawo ko kuma gajere. Haka sun fito da waɗansu abubuwan da mutum yake buƙata a lokacin da yake aiki da kwamfuta a jikin Tray kamar Wi-Fi da mutum yake amfani da shi, haka sun canza wurin karo sauti ko rage shi. Sannan ga mai son lura da hasken Monitor da yake amfani da shi a jikin Laptop zai iya rage hasken shi da kuma karo shi duk a wuri guda.

Action Center

Idan mutum yana amfani da wayar hannu misali kamar wayar da ke da manhaja ta Android ko iOS ya san aƙwai manuniya wato Notification wanda da zarar wani sabon saƙo ya shigo cikin wayar zai bayyana a saman wayar ko a tsakiya sai mutum ya taba sannan wannan saƙon ya shiga cikin manhajar da ta dace da shi. To a Windows 10 sun kawo nasu Notification din a gefen dama wanda suke kira shi da Action Center. Wanda duk wani saƙo da ya shigo cikin ita wannan kwamfutar ta ka zai bayyana a wannan wurin ne.

Inganta Windows Explorer

Kamfanin Microsoft sun ƙara inganta Windows Explorer to hanyar ƙarin da suka yi a jikin maɓallin Home da suka ƙara abubuwan da mutum yake yawan buɗewa a kowanne lokaci. Saka wannan maɓalli na frequently zai ƙara ba mutum sauƙin buɗe wa. Haka sun sake ƙayata mazubin takardu Folder sannan kuma sun yi zubi irin yadda wanda yake amfani da kwamfuta da waya ko ƙananan kaya zai iya amfani da su ba tare da samun ko ganin wani irin canji ba.

Universal App

Image result for windows 10 universal apps

A irin wannan lokaci da kusan komai ana ƙoƙarin komawa da shi cikin wayoyin hannu, musamman manhajoji da ake amfani da su a wayoyin komai da ruwanka (SmartPhone) kamfanin na Microsoft a wannan karon kuma a cikin Windows 10 ya sanya dukkan manhajojin da za su iya aiki a cikin kwamfuta su zama sun iya aiki a cikin wayoyi da kuma ƙananan na’urori. Wannan ya ke nuna mana ke nan duk waɗansu ayyuka da hotuna da bidiyo da mutum yake da su a cikin kwamfutar sa idan yan da wata waya mai amfani da manhajar Windows to zai iya yin amfani da su a lokaci guda. Microsoft sun sami nasarar cimma wannan tsari na Manhaja Bai Daya ta hanyar amfani da tsarin ajiyar kaya naOneDrive wanda za ka iya amfani da shi domin ajiyar kayan kwamfutar ka a ma’ajiya ta giza-gizai (Cloud Storage).

Ƙarin Inganci

Bayan da suka saurari ƙorafe-ƙorafen mutane dangane da kasa bambancewa tsakanin wurin gyara ko seta al’amuran kwamfuta da na waya, a karon farko kamfanin Microsoft ya saurari koken jama’a inda ya bayar da tsari iri biyu. Tsari na farko shi ne ya dawo daControl Panel kamar yadda aka san shi a cikin Windows 7 zuwa ƙasa. Sannan kuma tsarin Setting wanda wayoyin komai da ruwanka suke amfani da shi, shi ma yana nan kamar yadda dai aka san shi a Windows 8. Sai dai kamar yadda muka yi bayani a samaAction Center shi ne zai ɗauki ragamar harkar Notification  da lura da ƙulla alaƙa tsakanin na’urorin da ake son a haɗa su da ita wannan kwamfutar.

Windows Phone

 Image result for windows 10 phone

Idan muka buda yadda kasuwar wayoyi take ƙara haɓaka da tumbatsa, sannan mun san yadda kamfanin Google da yake da Android da kuma kamfanin Apple da yake daiPhone za mu tabbatar da cewar Windows Phone wacce kamfanin Microsoft yake da ita haƙiƙa ta kusa ta mace gaba ɗaya. Shi ya sa a wannan karon kamfanin yayi wani irin canji wanda ake sa ran zai farfaɗo  da tagomashin Windows Phone. Duk da cewar ita manhajar da zata zo a cikin wayoyin Microsoft ya yi kama matuƙa da Windows 8 amma aƙwai sauye-sauye masu dama a cikin wannan manhaja ta waya.

HoleLens

Image result for windows 10 hololens

Tabaran Dubarudu da kamfanin Microsoft suka ƙirƙiro wanda ya doke na Google wanda ya ke sa mutum ya fitar da zahirin abin da yake iya gani a cikin na’ura zuwa wajen duniyar mu. Misali idan ka saka wannan Tabarau baka buƙatar Monitor ko Screen domin ci gaba da ayyukan ka, misali idan kana son kayi aiki da zarar ka saka wannan tabarau za ka ga komai ya bayyana a gabanka kamar yadda ka ke ganin zahirin abu. Duk abin da kake son kayi za ka yi amfani da hannunka, kamar irin su Game za ka yi amfani da hannunka wurin sarrafa shi, haka wanda yake yin zane na gidaje da dai aikace-aikace. Amma kuma idan wani yana gefen ka zai ga kamar ka zama zautacce ko wanda ya saki layi, saboda kai abin da kake gani daban shi kuma yana ganin kana wasanni da hannayen ka. To, kamfanin Microsoft shi ne kamfani na farko da ya hada babbar manhajar sa da Holographics.

Fahimtar Yanayi (Mode)

Wannan shima wani tsari ne da kamfanin suka shigo da shi a kwamfutocin da ake yin su a yanzu wanda ake kiran su da Hybrid a tsarin gininsu, wato kwamfuta ce mai tsari iri biyu a wuri guda. Idan aka buɗe ta a gaban ka za ka yi tsammanin Laptop ce, amma kuma ana iya zare maɓallan rubutun ta (keyboard) sai ka ga ta koma kamar Tablet PC. Kasancewar ana iya cire keyboard a jikin ta shi ya sa ake kiran irin waɗannan na’urori daHybrid. Amma kuma inganci da Microsoft suka saka a cikin Windows 10 shi ne na fahimtar irin waɗannan na’urori duk lokacin da suke haɗe da keyboard to ita wannan manhajar zata fahimci cewar yanzu keyboard yana jikinsu saboda haka za ta mayar da hankalin ta wurin keyboard ɗin ne. Idan kuwa aka cire keyboard ɗin ta koma Tablet PCto sai ya fito da keyboard a fuskar Screen ɗin Tablet ɗin, sannan ya bayyanar da tsarin yin amfani da hannu wurin sarrafa ita Tablet ɗin.

Kayan Wasa na Xbox

Masu amfani da kayan wasannin Microsoft wanda aka fi sani da Xbox za su sami damar yin amfani da manhajojin Xbox a cikin kwamfutocin su a yanzu wanda a baya babu wanigame na Xbox da ake iya amfani da Windows wurin buga shi. Sannan kuma zasu iya yin amfani da na’urar nan ta DVR wacce take iya baka damar kwafe wasanninka ka kuma nuna shi kai tsaye. Kodayake, wannan canjin a kwamfuta ne kawai amma kamfanin Microsoft ba su fitar da sanarwar ko masu amfani da wayoyin Windows Phone za su sami wannan garabasar ba.

Wannan suna abubuwa mashahurai da ya kamata duk mai amfani ko yake son ya mallaki Windows 10 ya kamata ya sansu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *