Wayoyi 10 mafi tsada da kudinsu yafi albashin ma’aikatan wasu jahohi a Duniya

Da zaka tambayi masu sayar da waya wace waya ce tafi tsada a Duniya waya ta farko da zai kawo maka ita ce iPhone kasancewar kudinta yana iya kaiwa har N750,000 a kudin kasata Najeriya. A wannan rubutu da zamu kawo wasu wayoyi ne da kudinsu ya wuce hankalin mai hankali. Su wadannan wayoyi ne da aka yi su kamar kowace irin waya saidai kuma an kai su wasu kamfanoni na musamman irin wadanda suke kara kawata kayan ado na zinari da daimon domin kara canza musu zubi da kyau.

10. iPhone Princess Plus

Kudinta N63,768,600 ($176,400 USD)

Ita wannan iPhone Princess Plus  ita ce ta zo a na 10 a cikin jerin sunayen wayoyi mafi tsada a Duniya. Wannan wayar wani mutum mai suna Peter Aloisson ne ya hada ta da wayar iPhone wanda ya sa mata daimon guda 318 wanda aka samu jimillar nauyin su tsakanin 16.5 zuwa 17.75 karat.

9. Black Diamond VIPN Smartphone:

Kudinta N108,450,000 ($360,000 USD)

Wannan wayar Jeren Goh ne ya kirkire ta itama tana cikin wayoyi mafi tsada a Duniya an yi amfani da tsarin wayar Sony Ericson ne sai aka lullubeta da zinari, da wasu duwatsu na alfarma sannan da bakin daimon.

8. Vertu Signature Cobra:

Kudinta N130,140,000 ($360,000 USD)

Waya ce da aka yi domin ado da kwalliya, hakan ya sanya ta kasance na 8 a cikin jerin wayoyin da suka fi tsada a duniya. Kamfanin da ke siyar da kayan sarkoki na kasar Faransa mai suna Boucheron Vertu ya tsara ta, itama waya ce da aka lullube ta da zinari da duwatsu na alfarma. Tsarin ginin yawar ya danganci da irin design da wanda zai siya wayar yake bukata.

7. Gresso Luxor Las Vegas Jackpot:

Kudinta N361,500,000 ($1 Million USD)

Wannan wayar ta cire tutar da ta kai har dalar Amurka Miliyan daya saboda an yi amfani da itacen wata bishiya ce dake Nahiyar Afirka wacce aka ce tafi shekara 200 wurin fitar da bayan wayar, amfani da wannan bangaren itace mafi tsada a duniya ya sanya wayar tayi tsada, Gresso shine mutumin da ya tsara wannan wayar. Duk da waccan bishiyar wannan mutumin bai tsaya nan ba sai da ya sa mata bakin daimon a jikinta ya kuma hada da giram 180 na zinari sannan kuma kowane maballi aka yi amfani da duwatsu masu tsada wurin yinsu.

6. Diamond Crypto:

Kudinta N469,950,000 ($1.3 million USD)

Ita wannan wayar Peter Aloisson ne ya tsara ta, waya ce da aka yi amfani da manhajar Windows CE wurin gina ta, ya zuba mata daimon 300 wanda hakan ya sanya ta ta zamanto ta 6 a cikin jerin wayoyin da suka fi tsada a duniya.

5. Goldvish Le Million:

Kudinta N469,950,000 ($1.3 million USD)

Ita wannan wayar da hannu Goldvish suka kirkire ta kuma suka saka mata 18 karat na zinari sannan karat 120 na wani irin daimon VVS-1 diamons. Saboda irin zubi mai kyau da aka yi mata ya sanya wayar ta yi tsada matuka da kudinta ya haura dalar Amurka sama da Miliyan daya.

4. iPhone 3G Kings Button:

Kudinta N903,750,000 ($2.5 million USD)

Ita wannan wayar an yi amfani da wayar iPhone ne wurin canza mata zubi da tsari kuma wannan Peter Aloisson ne ya yi ta dukkan maballan amfani da ita da zinari aki yu sannan ya saka mata tsararrun daimon 130

3. iPhone 3GS Supreme Goldstriker Advanced:

Kudinta N1,135,110,000 ($3.14 million USD)

Wayar data zo na 3 a cikin wayoyi 10 mafi tsada a Duniya waya ce da Stuart Hughes wani dattijo kwararre dan kasar Birtaniya, wannan wayar tayi wannan tsadar ne saboda gaba dayanta yayi mata jiki na zinari ne, sannan yayi amfani da iPhone 3GS tare da 7.1 karat na daimon a jikinta

2. iPhone 4 Diamond Rose Edition:

Kudinta N2,892,000,000 ($8 million USD)

Itama waya ce da Stuart Hughes suka kirkiro sun yi amfani da iPhone 4 ne amma kuma sun yi amfani wani irin zinari sannan suka yi amfani da daimon 500 suka kewaye wayar baki dayanta da shi, sannan ajikin maballin suka yi amfani da wani daimon wanda nauyinsa yakai karat 1000, sannan aka yi amfani da wadansu kananan daimon guda 53 aka kewaye logo ita wayar sannan maballin tsakiya kuma aka yi amfani da diamond rose mai karfin karat 7.4.

1. Falcon Supernova iPhone 6 Pink Diamond:

Kudinta N17,532,750,000 ($48.5 million USD)

Wannan wayar data fi kowacce waya tsada wayar wata mata ce dake kasar Indiya Nita Ambani matar wani dan kasuwa Muskesh Ambani ita wannan wayar an yi amfani da zinari mai karat 24 da kuma wani katon daimon a bayan shi da amfani da wani irin karfe da ake kiran shi da platium.

Amma wani abin ban haushi ga dukkan wadannan wayoyi shine abinda wayarka take yi ita tasu shi take yi, tun daga amsa kira, shigowar sakon sms, browsing, chatting da dai makamantansu, iyakar abin da zamu ce shine wannan wayoyi na ta’adin kudi ne da alfahari da almubazzaranci.

Allah Ya sawake.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *