Categories
Tsaro

Wayar Hannunka na yin zafi? Ga dalilai dayadda za ka magance matsalar.

Wani abu da ya ke yawan damun masu amfani da wayoyin hannu musamman irin wadannan wayoyin komai da ruwanki wato Smartphones shi ne yawan yin zafi kamar zata kona hannu ko kuma dimi da mutum bai samun kwanciyar hankali da shi. Wani lokaci a wurin maza sai su ce idan suka saka ta a cikin […]

Wani abu da ya ke yawan damun masu amfani da wayoyin hannu musamman irin wadannan wayoyin komai da ruwanki wato Smartphones shi ne yawan yin zafi kamar zata kona hannu ko kuma dimi da mutum bai samun kwanciyar hankali da shi. Wani lokaci a wurin maza sai su ce idan suka saka ta a cikin aljihunsu sai ta dau zafi, wani lokaci ma sai da ka dauko ka duba kawai sai ka ga ai ta mutu saboda da irin wannan zafi.

A wannan darasi da zamu yi zamu fada muku abubuwan da ke kawo waya ta rika yin zafi da kuma hanyoyin da zamu kiyaye domin mu hana ita wannan wayar yin zafi.

Masu yawan sauraron labarai sun sami labarin kiranye da janye wayar kamfanin Samsong suka yi a ‘yan kwanakin baya kasancewar sabuwar wayar da ta shigo kasuwa haka nan kawai sai ta kama da wuta saboda matsala da aka samu wurin gina batirin ta. Wannan ya sanya muka ga ya dace muyi muku bayani game da irin zafin da idan kaji wayarka tana yi ka gane cewar akwai matsala.

Waya Na Yin Dumi

Baki ko sabon shigar amfani da wayoyin smartphone su sani cewar irin wannan wayar tana yi dumi wanda ya sha banban da irin kananan wayoyin da suke amfani da su a baya. Mu sani smartphones kayan wutan lantarki ne, saboda haka don kaji tayi dumi ka sani ba wani matsala ba ne.

Amma kuma idan kaji tayi zafi wanda kake jin tsoron zai iya lalata ta, ko kuma ta yi zafin da kake jin tsoron za ta iya fashewa ko ma ta la’anta masu amfani da ita to lallai ka na inda ya dace, domin abin da zamu tattauna ke nan.

Duk da cewar mafi yawan abin da zan fada sun fi karfi ga wayoyi masu amfani da fasahar wayar Android domin kusan su aka fi amfani da su a wannan nahiya tamu ta Afirka musamman Najeriya ta Arewa.

Ta wane wuri waya ke yin zafi?

Abu na farko da ya kamata mu fara kiyayewa shi ne ta wani wuri wayar take fara yin zafi? Duk da cewar nasan ba kuwa ba ne zai iya lura ko kiyayewa ba, amma dai zai iya yiwuwa ta batir ne ko kuma cajar wayar ita take haifarwa.

To amma bari mu mu fadi wuraren da waya zata iya daukar zafi ko kuma ta inda ake iya gane cewar waya tana zafi ba dumi ba.

Bayan wayar ke yin zafi

Duk lokacin da ka ji wayarka idan zata yi zafi ba inda yake yin zafi sai bayan wayar wato inda batirinta yake, to ka sani ba wayar bace ke da matsala batirin wayar shine ke kawo zafi a wayar. To idan ka tabbatar da haka ka samo wani batiri irin nata a saka a gwada idan ka ji wannan batirin baya zafi to sai ka je ka sayo wani sabo ka canza.

Zafin ta kasan wurin caji ne

nexus-6p-640x360

Wani lokaci zaka samu wayar bata yin zafi ko fara yin dumi sai bayan ka saka ta a jikin wuta domin yi mata caji, wannan matsalar tafi faruwa a lokacin da mutum ya ke amfani da wata cajar da ba ta asalin da wayar ta zo da shi ba. Domin mutane da yawa basa fahimtar cewar ba kowace irin caja ba ce ke yiwa kowace irin waya caji koda kuwa bakin su iri daya ne ko da kuwa kamfani daya ne da wayar mutukar ba irin na wayar bane.

Ita waya tana karbar wuta ne wanda aka kira da Direct Current domin ajiyar wutar lantarki cikin batirin waya ko laptop da dai makamantan kayan na’ura da suke amfani da batir domin su yi aiki. Kowace waya tana da nata karfin wutar da ake son ya caza ta. Shi yasa zaka samu wata wayar idan aka aro mata caja sai yayi awanni bai iya yin cajin wayar ba, wani kuma cikin dan kankanin lokaci sai ya cika maka wayar ka. To wannan matsalace sosai domin yin amfani da cajar wayar da ya ke sata tayi caji da wuri yana bata batir shi kanshi ga kuma bata injin da yake lura da karfin shigar wuta a cikin wayar.

To wannan ya ke nuna mana cewar idan muka tsinci wayarmu na yin zafi daga bakin caja mu sami wata caja irin ta wayar ko muce follow come kamar muke fadi, idan muka gwada muka ga bata zafin ko dimi to kunga mun gane matsala, idan kuwa muka gawa muka ga har yanzu dai tana zafi ya nuna kodai batir din shi ke dawo da wutar da ke shiga cikinsa, ko kuma daga charging point ne.

Yin zafi ta baya amma saman batiri

Idan kuma ka duba kaga wayar tana yin zafi ta baya amma kuma sai ka lura da cewar ba daga wurin zaman batirin ba ne, to zai iya yuwuwa ita karan kanta wayar ce ke yin zafi. Idan kuwa haka ne to bari in dan lissafo wasu wuraren da zamu taba ko lura domin mu gane ta ina zafin ke farawa?

Wayar na zafi ta wurin sauraron magana (Speaker)

Wani lokaci za ka ji idan kana waya sai kaji kunnen ka ya dau zafi ta wurin speaker to irin wannan matalar ba wai zafi da konewar kunnan naka a ke ji ba wannan zafi zai iya shafar lafiyar kwakwalwarka saboda haka duk lokacin da ka ke amsa waya kunneka na zafi to ka canza wayar ko kuma na nemi headphone mai kyau ka siya ka rika amfani da shi.

Fuskar wayar ke yin zafi Screen?

Wani lokaci zaka samu idan kana amsa waya fuskar wayar ne ke yin zafi, to idan haka na faruwa akwai abubuwa da zamu lissafo wadanda ya kamata mu yi domin hana wayar tamu yin wannan zafi ta fuska.

Boyayyun Abubuwan da ke sa waya yin zafi

Tun da mun fado wadansu hanyoyi da ake iya gane waya na yin zafi a zahiri, to bari mu fado wadansu abubuwa da suke sanya ita wayar ta rika yin zafi wanda ba kasafai mutane suke fahimta ba.

Application da yawa suna aiki lokaci guda

Wani lokaci ba wadancan abubuwan da muka lissafo su suke sa yawa ta rika yin zafi kodawane lokaci ba, yawan kunna application na wayar da kuma barinsu a kunne kodawane lokaci shima yana sa waya ta rika yin zafi. Saboda haka yake da kyau duk lokacin da mutum yaji wayarsa na yawan yin zafi ya rike bude Application Manager din sa yana gobe budaddun application wannan zai taimaka masa sosai.

Akwa wadansu application na musaman wadanda suke yin irin wannan aiki kodayake suna da tasu matsalar suma amma dai mu sami application da yake irin wannan aikin domin taimakawa wayar ta mu.

Abu mai nauyi da tsawo da cin lokaci

Ba mai shakkar cewar wayoyin Android akwai dadi wurin yin amfani da su musamman idan muka yi la’akari da irin abubuwan da ake iya yi da su, kamar daura musu bidiyo mai nauyi, ko kuma kallon bidiyo mai tsawo, ko daura game mai nauyi da kuma amfani da shi, ga sauraron sauti na karatu ku nishadi, ga yadda muke shiga intanet da duba imel da dai makamantansu dukkansu kuma akan wannan ‘yar karamar wayar da bata wuce ta zauna a tafin hannunka ba.

Saboda haka mu sani kallo ko sauraron abu mai nauyi zai iya sanya waya tayi zafi musamman idan tana rike a hannunmu ne domin ga zafin hannu ga na riko ga kuma nata zafin na kanta, saboda haka yaka da kyau mu guji matsawa wayoyin mu da kallon bidiyo masu tsawo ko kuma buga game masu nauyi musamman irin wadanda suke bukatar higher configuration wurin amfani da su ko kuma daura su a jikin wayoyinmu.

Lalataccen Batiri

kumburin-batirin-waya

Batiri mara kyau ko lalatacce yana kawo zafi sosai a wayoyinmu wanda shima wannan matsala ce mai zaman kanta. Idan ka tabbatar da cewar batir dinka ya fara lalacewa ta wurin ganin yana zubar da ruwa ko kuma yana dan kumbura to kana bukatar ka cireshi a jikin wayarka ka canza shi. Mu sani  yin amfani da kumburarren batiri akwai hatsari sosai domin zai iya yin bidiga ko kamawa da wuta kodawane lokaci, kuma wannan yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Rashin Iska

Daya daga cikin abin da zai iya sa waya ta yi zafi akwai karancin isaka wanda ya kawo wadansu dalilai da zamu lissafa wadanda suma suna taimakawa wurin sa waya tayi zafi, ga kadan daga ciki.

Sakata a Aljihu

waya-a-aljihu

Wani lokacin wayoyinmu suna yi zafi idan suna cikin aljihu musamman idan suka dade a cikin aljihun. Mu kan mu lokacin sanyi idan muka fito waje muna tafiya sai sanyi ya dame mu mukan saka hannunmu a cikin aljihu domin muji dimi. To yana da kyau duk lokacin da ka saka waya a cikin aljihu sannan ka ji ta fara zafi to ka cirota na wani dan lokaci domin ta dan numfasa. Wannan zai taimaka wurin hana wayar lalacewa ko kamawa da wuta.

Rigar Waya

Rigunan da ake sakawa waya wato jacket suna taimaka mana wurin kiyaye wayar daga fashewa ko kuma zubar wani abu mai ruwa a jikinta amma kuma idan ba mun samu rigar wayar da ta dace da wayarba zai iya taimakawa wurin sa wayar ta yi zafi.

Akwai wuraren da waya take amfani da shi domin ta numfasa ko kuma samun iska to idan ba an sami rigar da aka yi ta musamman domin ita wayar ba za a iya samun matsala.

Wasu abubuwan da zasu iya sa waya yin zafi

Haduwarta da Ruwa

Idan ka san wani lokaci kana shiga wanka da waya, ko kuma irin ruwan sama ya doke ka kuma wayar na tare da kai, ko kuma aka yi rashin sa a ta fada cikin wani abu mai ruwa, to koda ka gyara wayar zai iya yuwuwa wayar ta rika yin zafi, domin haduwar ruwa da kayan lantarki ka iya haifar da matsaloli masu yawa.

Akwai wata ‘yar karamar takarda dake boye a kasan wurin batir ko idan ka bude murfin waya wacce ake kira da LDI wato Liquid Damage Indicator. Amfanin wannan yar takarda tana zuwa ne a fara idan har ruwa  ya shiga wayar ka zai canza zuwa wani kalan.

Rashin Hutun Waya

Mu sani waya tana bukatar hutu ko da na ‘yan mintuna ne, idan kana daga cikin wadanda suke kunnan waya basa kashewa kodawane lokaci tana kunne, idan batir dinta ya kusa karewa sai ka jona mata caji to wani lokaci rashin hutunta zai iya kawo matsalar zafi.

Cire tsarin da ba a da bukatarsa

Wannan yana daga cikin matsalar da mutane da dama basu fahimta ba wurin yin amfani da wayoyin hannu, akwai wadansu tsare –tsaren da suke cikin waya wadanda ba kodawane lokaci muke amfani da su ba.

Misali irin su hotunan fuskar waya masu motsi, ko kuma irin karin agogon jikin waya na musamman mai zama a fuskar waya, ko irin manhajojin duba yanayi wato weather app da dai makamantansu. To ire iren irin wadannan manhajoji yana da kyau idan ba amfani da su za mu yi ba mu rika dakatar da su wato disabling din su.

Tsohon Manhaja

Barin tsohon manhaja a jikin waya yana iya cin karo da sabon tsari a jikin wayar wanda zai iya haifar da sanya waya ta yi zafi. Shi yasa kashi 60% na wayoyin ‘yan Afirka musamman Hausawan mu suna amfani da application ne da wani ya saukar a wayarsa ba zuwa suke yi kai tsaye su saukar ba.

Wani lokaci ma zaka samu wani yana mafani da application amma kuma wani ne ya saka mishi bai kuma taba hawa intanet ba ballantana ya sabunta wannan manhajar.

To barin tsofaffin manhajoji ko application a cikin waya zai kawo matsalar sanya wayar ta rika yin zafi.

Hardaware

Wani lokaci kuma hardware wato kayan da ake iya gani a taba a jikin waya suma idan suka fara samun matsala suna iya haifar da waya ta rika yin zafi.

Abubuwan da ba ayi idan waya ta yi zafi

Kada don kaji wayar ka tayi zafi kamar zata kone ko zata kama da wuta ka ce zaka saka ta a cikin firij ko gidan kankara. Bama bada shawara yin haka domin kun san dai waya da ruwa sai a hankali, kuma sanyi da zata dauka daga kankara ruwa zai koma, kuma zai yi wa wayar lahani.

Wayar dai taki dai na zafi

To idan duk abin da muka lissafo maka a wannan darasi ka gwada amma wayar ba ta dena zafi ba, to idan kasan wayar ka saye ta sabuwa ce ko kuma lasisin garantin ta bai shekara ba zaka iya mayar da ita kamfanin wayar.

Shi yasa yake da kyau mutum ya rika siyan irin wadannan kayan a wurin manyan diloli domin zai taimaka wurin idan wayar ta samu matsala za su iya karba su canza maka wata sabuwa.

Amma da sharadin ba ka yi ganganci wurin lalata ta ba, ko baka kaiwa injiniyoyin gyara samun sa a ba, ko kuma kai baka ce zaka koyi gyara akan ta ba.

Rufewa

Lallai zafin da waya ta ke yi hatsari ne ga remu da jama’a da kuma wadanda suke tare da su, ya sa yake da kyau kodawane lokaci mu rika lura da yanayin da wayoyinmu suke shiga domin kare lafiyar mu.

2 replies on “Wayar Hannunka na yin zafi? Ga dalilai dayadda za ka magance matsalar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *