VLC DINA YANA DA MATSALA

Assalam, malam VLC DINA YANA DA MATSALA, YANA FITOMIN DA “DEBUG REPORT” IDAN INA AMFANI DA SHI. YAYA ZAN YI?      

Kasan VLC player daya ne daga cikin Public-Domian-Software wato shi software ne da ake rabashi kyauta, kuma software da ake baiwa kowa damar ya yi canji a cikin shi, domin idan kana da ilimin programming za ka samu bayan shi VLC Player kuma harda code da aka yi shi program din. Idan har ka samu irin wannan matsala a binda za ka yi sai ka shiga internet ka nemo kamfanin da suke yin shi wannan program na VLC za ka samu sun saki wani sabo sai ka sauko da shi domin amfaninka. Amma kuma me ke kawa irin wannan matsala, wani sa’in za ka samu cewar Virus ya kama ita na’urar mutum har ya taba wani shashe na program din to sai ka samu idan ka tashi program din yana baka matsala. wani lokaci kuma ita player dince take samun matsala wajen bude wani file kafin ta nemo matsalar sai ta kasa ci gaba da aiki wani lokaci kuma matsalar ba ta player din ba ce, na operating system ne. da fatan ka gamsu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *