Video Editing a Ilmance (1)

Kasancewar kimiyya da fasahar kera-kere ta yawaita a wannan lokaci da kuma saukin samun kaya wutar lantarki da muke yi a saukake ya zamanto muna yin mu’amala da abubuwa masu yawa amma ba mu san ya suke yin aiki ba.

daya daga cikin irin wannan abubuwa zamu iya cewar hotuna masu motsi wato video wadanda muke ganinsu a akwatunan talabijin din mu ko kuma ta hanyar amfani da na’urar kallon faya-fayan CD ko DVD ko kuma ta kamo wata tasha daga satilite ko kuma yanzu da muke amfani da wayoyin da ke hannunmu domin dauka ko kuma kallon irin wadannan hotunan masu motsi.

daya daga cikin tambayoyin da muke yawan samu a nan Duniyar Computer shi ne wai ya ake iya daukar hoto mai motsi kuma a gyara shi ya zama bidiyo.

Sunnan Ahmad Umar daya daga cikin dalibai a Duniyar Computer ina karatu a bangaren Graphics da Multimedia.

Zan yi mana magana akan abubuwan da ya kamata mu sansu idan muna son mu koyi gyaran hotuna masu motsi wato video editing.

  1. Mene ne Video editing

abu na farko da ya kamata mutane su sani shi ne idan aka ce video editing me ake nufi? Video Editing hanya ce da ake amfani da ita wurin shirya hotuna masu motsi ko marasa motsi tare da hada musu sauti da abubuwan bukata domin su zama curarren bidiyo guda daya.

shi wannan gyara ana kiranshi da post production process wanda ake hada take a cikin bidiyon (Title) ko gyaran kalan hotun bidiyon (color correction) ko kuma cakudawar sauti a cikin shi.

Sau tari mutane suna amfani da kalmar editing domin misalta irin wannan ayyuka da suke yi wanda wani lokaci gyaran bidiyon nasu ba za mu kirashi da post production ba.

  1. Dalilin yin Video Editing

akwai dalilai da yawa da za su sa ka ce zaka gyara bidiyo domin kai ko mutane su yi amfani da shi, wannan dalili kuma ya danganta daga gare ka, amma kafin mu ji naka dalilai ba ri mu ambata kadan daga cikin wadansu dalilai kamar haka:-

  1. a) Bana son wani bangare:- wannan shi ne dalili mafi sauki wanda yafi zama dalili kasancewar ba komai da ka sauko kake bukatar kowa ya gani a cikin bidiyon ba.
  2. b) Zabar inda ya yi maka:- da yake ana daukar abubuwa da dama lokacin da ake amfani da kamera wurin daukar bidiyo yin editing yana baka dama ka zabi wuraren da suka fi baka sha’awa a cikin bidiyon da ka dauka kafin ka saki kowa ya gani.
  3. c) Shirya shi yadda kake so:- Mafi yawan daukar video da ake yi karshen al’amarin ya isar da wani sako ne, ko na labari ko tarihi ko karantarwa da nishadantarwa hakan ya sanya gyara shi da shirya shi domin komai ya tafi daidai ya zama dalili mai amfani.

3) Karkasuwar Video Editing

Duk da cewar wannan darasi ne mai fadi kuma wanda yake bukatar yalwatacce bayani amma zan yi kokarin wurin fadin kasuwar gyaran bidiyo. Wannan kasawa da zamu yi ba shi ke nufin su ke nan ba amma kuma zamu fadi guda hudu wadanda su suka fi shara daga ciki

  1. a) Film Splicing – Daddatsa Shiri:- Duk da cewar Film Splicing ba a kiranshi da Video Editing amma ya cancanci a kawoshi a cikin domin shi ne hanyar da ake bi domin daukar gutsattsarin bidiyo domin shirya film wanda daga bisani ayi amfani da shi bidiyon ko kuma a watsar da shi.
  2. b) Kaset zuwa Kaset – Linear Editing:- Wannan itace tsohuwar hanya da ake amfani da ita da da domin gyaran bidiyo. A da lokacin da technology bai bunkasa ba, ana amfani da kaset na bidiyo ne domin a gyaran bidiyon da a aka dauka. Mutum na bukatar Camera guda biyu ko injin da ke kallon bidiyo guda biyu sai ya saka kaset din da ya dauko ya kuma saka sabon kaset yana sake dauka idan ya zon inda baya so sai ya dakatar da cancan daukar sai idan ya wuce sai ya ci gaba da dauka wannan shi ake kira da Linear Editing
  3. c) Gyaran Bidiyo da Computer – Non Linear Editing:- Wannan wani tsari ne an yin amfani kayan kwamfuta da kuma manhajoji wurin diba da gyaran hotuna masu mosti. Da yake ita computer tana amfani da tsari na Digital ne shi yasa ake kiran wannan gyaran da non-linear editing.

A darasi na gaba In Sha Allah zamu ji sauran bayanai game da video editing da kuma abubuwan da ake amfani da su wurin yin.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Salam, duniyar computer ina maku jinjina, a gaskiya kuna burgeni. Don Allah nasan dai ku mazauna garin kaduna ne. Don Allah a kaduna a`ina kuke da office? Nagode

  2. salamu alaikum yan uwa ya kk ina fatan kuna chikin koshin lfy da aminchi kamar da yadda nasan makasudin ku shine ku koyawa dan nageria abubuwa ko ku samar mana da aikinyi . kuma muxamo masu ido akan harkar cumputer .to nima dai ina daya daga chikin yara masu tasowa kuma wanda allah ya nufesu da son suga suna da ido akan wadanan harkoki naku to dan allah ni mutumin kano ne karamar hukumar dambatta amman yanxu ina karatu asudan to dan allah ina so ku bani shawar wari akan yanda zan koyi cumputer da duk abu da kukaga zai tai makeni ga whatsopp number ta nan minfadilikum +249111044876