Categories
Tsaro

TSOHUWAR WAYA KO MASIFA: YANZU BA DA BANE

Akwai rashin hankali sosai a wannan lokacin mutum ya sayi waya ko kayan computer a wurin mutumin da ba amintacce ko ba shine asalin wanda ya mai ita ba.

Kada ka yi mamakin wayar daka siyeta a wurin wani mutum ta sata ce ko kuma fashi aka yi kuma jami’ai suna nan suna tracking dinta.

Ina baiwa jama’a shawara da duk wanda zai sa yi waya ko kayan kwamfuta ya tabbatar ya sayi sababbi ko kuma yaje kasuwa shagon sayar da wannan kaya ya saya su bashi receipt.

Yanzu ba da bane domin akwai kayan tracking na waya na zamani a hannun jami’ai kuma ina tabbatar muku idan mutum bai yi taka tsantsan ba wata rana zaiji a jikinsa.

Abubuwan da na gani a kwanan nan gaskiya abin ya bani tsoro matuka, domin har ofis dina jami’ai masu binciken wayoyin sata suka zo da zimmar suna neman wani wanda ni ko sunansa ma ban sani ba.

Na yi mamaki da jimami gami da ta ajjubi da na samu labarin irin mutane masu matukar mutunci da siyan waya ta hannu ta jefasu a cikin bala’i, wanda wadansu daga cikinsu har zuwa yau ba su iya fita daga cikin wannan matsalar ba.

Akwai cikin abokaina da har yanzu suna zuwa ofishin ‘yan sanda domin kanin matarsa ya bata waya kyauta, shi kuma ya siyeta a kasuwa wurin wani mai sayar da waya da bashi da shago, ashe wannan wayar a Abuja aka yi fashi har da kisan rai.

Shi kanin nata da ya baka kyautar wayar a N3000 ya siya, (daman kudinta haka yake) yanzu haka sun kashe kudi yafi N250,000 kuma har yanzu ana kotu.

Ni kaina akwai kwanwar matata da aka shiga gidanta da daddare watannin baya da suka wuce aka dauke mata wayoyi guda biyu da N80,000 wanda ajiya ake kawo mata. Abinda ya daurewa kowa kai bayan da muka je Police station muka rubuta bayanai suka tura mu bangaren da ake bincikar wayar da ta bace bayan kwana biyu sai labari ya canza.

Domin lokacin da aka kiramu domin muga wanda aka kama da wayar sai ga wani dalibin mu kuma ladani a wani babban masallaci, wanda tabbas bai ma san gidan da ita kwanwar matata take ba ballantana a ce shi ya sata.

Amma yadda abin ya faru da shi, shi ne yake kasuwa ne ya siya wayar a wurin irin masu sayar da wayar da basu da shago, haka taja masa asarar N30,000 wanda a masallaci aka nemi taimako.

Idan kuka duba wannan labari guda biyu da na baku da wanda nasa wasu zasu kara a kasa wurin yin comment hakika yanzu siyan waya ko kayan wuta ba tare da tantancewa a wurin mai siyarwa ba, mutum zai iya fadawa cikin musibar da zai dade bai fita ba.

Bamu labarin irin wannan daga wurinka

3 replies on “TSOHUWAR WAYA KO MASIFA: YANZU BA DA BANE”

Za ka iya yi mutukar zaka danganta cewar mu ke da wannan rubutu kuma ka saka link din da ka dauko don masu bibiyarka su sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *