Categories
Tambayoyi

Ina son amfani da WLAN a Laptop ya zan yi?

Ina da laptop HP kuma ina so in yi ammafi da wlan idan naje cafee to amma na duba bata da shi ya ya zan yi mata?

Malam Adam A Adam, amfanin WLAN shi ne ya baka damar samun connection na network ba tare da ka hada da waya ba. kusan duk computer da aka yi su kusan shekaru biyar da suke wuce suna da WIFI technology wanda shi ne ke baka damar samun network a jikin laptop, zai iya yuwuwa a cikin taka laptop din akwai wlan amma baka kunna shi ba, sautari yana kashe ne, idan kuwa kana son ka gane cewar akwai wireless network a laptop dinka za ka duba jikin functions key (F1 zuwa F12) a jiki idan ka ga alamar raga ko signa to sai ka danna Fn key da ke kusa da Ctrl key, tare da shi key da yake kunna WLAN, wani lokaci za ka samu akwai a cikin computer amma ba a yi installing din driver dinshi ba ne, za ka iya gane haka idan ka shiga device manager. Idan kuwa ita computer da ka ke amfani da ita babu WLAN ne, to a wannan lokaci ana siyar da kalakalan kayan computer da za su iya baka WLAN a Kwamfutarka, kamar (USB Adapter + Wlan Laptop Antenna) wanda a USB PORT ake hada shi, kuma baya wuce dubu N8000 zuwa N10000 da fatar ka gamsu.