Categories
Duniyar Waya

ME YA SA WAYOYIN ANDROID SUKA FI WAYOYI KIRAR SYMBIAN

Symbian ta samu karbuwa ga mutane da dama, amma yanzu abin ba haka bane. Ayanzu na’uran Android suka ji  ana yawan magana a kansu. Me karatu na iya tambaya me yasa haka? Meye dalilin da zai sa na sayi Android? Nakan ga irin wannan tambayoyin daga mutane daban-daban a yawancin lokuta. Amma har yanzu ban ji ko ganin wata kwakkwarar amsa ba da ta yi cikakken bayani game dalilin da ya sa Android suks fi Simbian.

Zan karfafa kan abubuwa guda biyu

a)      Cewar akwai na’urorin Android Iri daban-daban a Kasuwa, amma ni zan yi magana ne akan irin waɗanda ake kiran su da suna High-end phones.

b)      Su ma Symbian suna da nasu dalilan da za su iya bayarwa game da darajar wayoyin nasu da suka tura a dandalin su.

Saboda haka a nawa ra’ayin ga hujjojin da na ga Android na da shi.

 1. Saurin sarrafa kanta, saboda abin sarrafawa na zamani suke da shi (modern processor). Android tana amafani da processor Cortex- A8 wanda ya fi irin wanda Symbian ke dauke da shi wato Arm11 CPUs. Misalin hakan ana iya gani ga HTC snapdragons da kuma  Samsung Humming birds,dukkansu na amfani da 1 GHz wajen  saurain sarrafa bayanai akan na Synbian da ke tafiya a kan 680MHz. Kuma wannan tazaran nasu yama karo a kan irin Android da aka yi yanzu masu dual-core CPUs mai Cortex-A9 na wayar Motorola Atrix. Hakan ya sa suka bar Symbian a baya.
 2. Fitar da launi (screen resolution) Android na ammfani da 800(854)x480 idan ka haɗa da na Symbian wanda ke amfani da (640×540). Wannan yana sa ka iya jin ɗaɗin browsing da ganin bayanai da hotuna da kyau. Fitowar Atrix sai ta zo da karin hakan wato qHD resolution (960×540). Tana zitan kala fiye da Symbian sau ninki 2.25 (pixels.
 3. Yawan Kwakwalwa (Memory (RAM). Sau da yawa akan damu idan ka nishadu da browsing sai wayar ta ce maka low memory lokacin da Android ke zuwa 512MB RAM Symbian kuwa na dauke da 256MB ne. Duk da cewa Nokia na ta ƙoƙarin fadada nasu memory hakan ya ci tura a Symbian domin wasu Androids har sun kai ga suna zuwa da RAM(768MB in Desire HD, 1GB a Artrix).
 4. Graphics (zane) da kuma Games. Symbian na dauke da Broadcom BCM2727 GPU, da ake ganin ci gaba a kan shi a kan Andreno 200 chips (Nexus one) iran da amma ta koma baya saboda  zuwan Android GPUs, da kuma irin na  zamanin, wato Adreno 205 (Desire HD) ko kuma powerVR SGX540 cores.Nvidia Tegra 2 ta zo da fage (zone ) inda masu anfani da Nvidia da ake kira Tegra kan iya buga games.
 5. Mabudin Yanar gizo (Web browser) da yawa an fi ji da bowser na Android saboda ta fi sauri da kuma bada abin da ake so. Misali Android 2.2 da ke iya daukan Adobe 10.1  da ake amfani da shi a  yawancin websites. Yana baka damar kallon video da games daga websites mai nauyi kamar Kongregate. Amma Symbian  sai ta sa maka ciwon kai kafin ta buɗe. Idan ma ta iyakenan, a inda ya sa yawancin mutane sun fi so su yi amfani da Opera duk da ita ma ba ta iya ɗauka.
 6.   Nishaɗi (Multimedia). Maraba da applications na nishaɗin wakoki na sauti da na hotuna (music and videos). Kalon video, jin sauti  ko sarrafa hotuna (pictures) abin nishaɗi ne a Androids device. Faɗin fuska (screen 4.3”) karfin  kala da haske (super Amoleds), samun media players cikin sauƙi da ke taimakawa waje buɗe kowanne irin video/ sauti, shiga yanar gizo ta HDMI (connectivity) sauko da hotu ko sauti da DLNA media streming duk na daga cikin fifita Andorids a kan Symbian.
 7. Tarin application (application store) lokacin da Symbian Ovi store ya kai (258% a shekarar 2010) tuni Androids ta keta ta a kasuwa da (544% a shekarar 2010). Ta ɓangaren applications ma abin ya wuce yadda ake tsammani. Android na da (200,000) ya yin da Ovi ke da (40,000).  Kodayake mukan duba shine yadda waɗannan applications ɗin ke tafiyar da wayoyin mu. Inda Ovi ke gazawa wajen saukar da abubuwa (downloading) ita ko Android takan gaya maka idan sabon updates ya fito kai tama yi maka updates idan ka so. Applicaion kamar AppBrain zai iya baka damar ka haɗa na’urar taka da kwanfutar ka domin ka yi installing bayan ka dirje irin wanda kaka so.
 8. Game da maganar application da na yi a sama ina mai tabbatar maka cewar akwai applications da dama na Android fiye da na Symbian a cikin kasuwanni. Kai ita kana iya yin abubuwa da dama da baka iya yi da Symbian. Alal misali ina amfani da 5 Dutch Android apps wanda babu irin kwatankwacinsa da za ka iya haɗawa da Symbian. A Android akwai applications na sautuka (music kai har ma da na kiwon lafiya (medical).Idan ma kadu ba abin ta wata fuskar, daban ba ma ta application store ba, za ka ga cewar applications na Symbian ba su da dadi ko saurin shiga (installing) kamar na Androids.
 9. Custom ROMS and Modding (tsangayar wayarka). Wannan tafarki na musamman inda Android ta keta kowa (platforms). Gwanayen irin wannan tsangayar kamar usuCyanogen, XDA-world ko kuma Modaco sun yi fice wajen yin amfani da sabo ko kuma tsohon OS (firmware) da kuma iya yin updates a kan lokaci. A gaskiya Androids ta wuce yadda ake tsammani.
 10. OS updates. A takaice duk wata shida (6) za ka ga sabon OS na Androids ya fito. Makera wayoyi aya yin da suke tunanin yadda za su yi updating nasu, za ka samu tuni HTC sun wuce wannan wurin ta hanyar amfani da custom ROMS da na bayyana a sama.
 11. Juyin-juya halin kasuwanci, ana iya ganin hakan ta yadda kasuwar Symbian ke kara yin kasa kullum, amma ta Android sai kara tashi take yi da samun karbuwa. Wasu da yawa masu kera wayoyi suna ta barin Symbian gaba ɗaya (Kamar Samsung da SE) kai abin ya zama kamr tsakinin mutun ɗaya da sauran, inda Symbian take ita kaɗai (Nokia) tana fama da taron dangi (Google, Samsung, HTC, Motorola, SE, LG da sauran su).  A watan Janairu ya yin da CES a 2011 suka fito da bayanai game da ci gaban da aka samu ba ma a maganan Symbian a wajen. Hakan ya faru saboda fitowar wato Tablets da ta ci kasuwa da yaki. Daukar lokaci mai tsawo wajen bayyana sabuwar waya da fito da ita na daya daga cikin abubuwan da suka ja ma Symbian ta kara komawa baya (misali Nokia N8 da E7). Sabanin haka ga Androids   da suke nasu tsakanin wata ɗaya zuwa uku ( 1- 3 months). ( ka duba DHD ko Nexus S ko kuma LG Optimus 2x)

 

Categories
Duniyar Waya

Akwai Virus a Wayar ka KA SANI KUWA?

Virus Na Waya (Phones)

Virus na wayar-tafi-da-gidanka kamar virus na computer ne, abin da ake nufi da virus shine wani file ne da yake yin aiki musamman domin ya bata ko lalata wani bangare na computer ka ko kuma wayarka. Ko da yake computer virus yana yaduwane a sanadiyar email da kuma downloading daga internet, shima virus na waya yana yaduwa ne ta downloading daga internet ko kuma ta karbar sakon na MMS (Multimedia Messaging Service) ko kuma ta turo sako daga bluetooth. Sau tari a wannan lokaci virus da suke shiga wayoyin hannu suna shiga ne ta wajen turo maka wani abu daga computer. Ko da yake virus da yake shiga daga wata waya zuwa wata har yanzu bai gama shaharaba.

Virus na waya da zai iya shiga ta wata waya yafi yawane ga masu amfani wayar da take amfani da tsari na Symbian, ko da yake wadanda suke rubuta shi wannan virus na waya basu wani samu karbuwa ba a duniyar kamfanonin da suke yin waya ballantana su sami wani karfi, dalilin haka yakasance ko da anyi wani virus na waya zaka samu bai cika bata wayar ba gaba daya.

 

Ya aka yi suka yadu?

Duk wanda yake amfani da wayar da kawai sai dai a kira shi ko kuma ya amsa waya ko kuma ya kira ya aika da sakon SMS ya kwantar da hankalinshi babu wani virus da zai sami wayar shi.

Amma dukkanin wata waya da take da Bluetooth sannan kuma zaka iya karbar sakon MMS ko kuma kayi browsing da wayarka zata iya kamuwa da virus na waya. Waya tana da virus da dama wadanda suke iya yaduwa ta hanyoyi guda uku

·        Downloading a Internet – virus na waya yana yaduwa ta internet kamar yadda aka sani virus na computer yana yaduwa. Mutum zai shiga internet da wayarshi yaga wani file ko game ko kuma hoto ko kuma theme yayi mishi ya saukar da shi zuwa wayarshi ashe yana tattare da virus bai sani ba.

·        Karbar sako ta Bluetooth – virus na waya yana iya yaduwa a sakamakon Bluetooth din wayarka da ka bude domin wani ya aiko maka da sako, sai aka yi rashin sa’a ita wayar tashi akwai virus a ciki to duk sakon da ya aiko maka da shi zai taho tare da virus.

·        Multimedia Messaging Service (MMS) – wannan wani dama ce da wayar ka take baka idan kana son ka aika da sokon hoto ko kuma sakon video ga wani abokin ka ko kuma wata waya ba tare da Bluetooth ba ko kuma internet, kamfanin da kake amfani da layinsu su suke da alhakin baka wannan dama ko da wayar  tana supporting MMS, wanda shi virus da ya shigo a sakamakon MMS yafi hadari sabo da zai shiga cikin contacts dinka ne kai tsaye ya rinka aikawa sauran mutanen ka wannan virus din.

Kada ka manta dukkanin wani virus na waya ko na computer mataki daya suke bi shine dole sai ka yi installing dinsu a cikin wayar ko kuma computer zasu iya yin aiki, da wannan dalili ne ya kasance mafi wayan virus sun fi zuwa tare da games ko kuma wani program da za a ce idan ka sakashi zai iya tsare ka daga wani abu.

Commwarrior Virus an samu bullowar shi a Junairun 2005 kuma shine virus na farko da ya fara shiga wayar tafi da gidan ka har ya iya yin ta adi, kuma wani abun mamaki zai iya watsa kanshi a dan kankanin lokaci ga kusan duk mutumin dake da waya kuma yabar wayar a bude kusa da wanda yake da wannan virus din. Yadda yake yada kanshi shine ta hanya ta Bluetooth da MMS, da zarar ka sami sakon wannan virus sannan kuma kayi installing dinshi, kai tsaye zai fara neman wata wayar da Bluetooth dinta yake a kunne, da zarar ya samu zai aika da wannan virus ga wannan wayar. Haka shi wannan virus na Commwarrior zai kuma shiga cikin contact list dinka ya tura musu sakon MMS da shi wannan virus. (ya kake ganin idan kaga sako daga webmaster zaka karba ko zaka ki karba?). shi yasa commwarrior virus ya zama shahararren virus da ya damu mutane a wancan lokacin tunda yana amfani da hanyoyi biyu ne wajen yada kanshi.

Sabo da haka ya virus din yake yi idan har ya shiga wayar ka?

Barnar da yake yi.

Virus na waya na farko da aka sani shine Cabir duk da yake ba ya wani cutarwa ko kada, a binda kawai yake yi shine zai shiga wayar ka ne kawai yayi ta kokarin yada kanshi. Ko da yake daman mafi yawan virus na waya basu cika cutarwa ba. sosai

Kadan daga cikin abinda virus na waya ke iya yi shine ya shiga ya share dukkan wani contact da kake da su, ko kuma ya goge wani calendar da ka shirya a wayarka da makamanta haka, sannan kuma zai iya kwashe sunayen mutanen da suke cikin yawar ka gaba daya ya dauki wani hoto a cikin wannan wayar taka ta dauka virus a cikin shi ya kuma aikawa kowa da yake cikin contacts naka. Wani abin haushi da irin wannan MMS virus shine baya da watsa kanshi da yake yi, haka kuma yana yin amfani da kudin da kake da shi a waya tunda shi MMS ba kamar SMS bane, ana cire kud da dan dama. Abu kuma mafi muni shine zai iya neman wani application dake cikin wayarka ya lalata shi, ko kuma ya lalata wayar gaba dayan ta ta zamanto bata da amfani.

Ga wasu daga cikin virus na waya guda biyar da bayani game da su.

Sunan Virus: Cabir.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: June 2004
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phone
 • Hanyar da yake yada kanshi: updating
 • Irin cutarwar da yake yi: Baya cutar wa
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/cabir.shtml

 

Sunan Virus: Skulls.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: November 2004
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading a Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana hana ka komai a wayar illa kira da amsa kira
 • Karin bayani: http://www.f-secure.com/v-descs/skulls.shtml

Sunan Virus: Commwarrior.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: January 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Bluetooth da MMS
 • Irin cutarwar da yake yi: yana aikawa da sako MMS ga duk wanda yake cikin contact
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/commwarrior.shtml

Sunan Virus: Locknut.B

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: March 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading ta Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana lalata system ROM, sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware acikin wayar ka
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/locknut_b.shtml

 

Sunan Virus: Fontal.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: April 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading ta Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana hana ta tashi, idan kuma an samu ta tashin sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware acikin wayar ka
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/fontal_a.shtml

 

Yadda zaka tsare wayar ka

Babbar hanyar da zaka iya tare wayar ka daga kamuwa da wani virus tayi daidai da hanyar da ake tsare computer daga kamuwa da virus, wannan ba wata hanya bace illa kada ka bude wani abu ba ka san daga inda yake ba ko kuma baka da garantin waye ya aiko maka da shi

 • Matakin farko ka kashe Bluetooth, ka saka ta a ‘hidden’ wato kada kowa ya ganta.
 • Mataki na biyu shine ko da wani lokaci ka rinka shiga kamfanin da suka yi wayar ka kana dubawa idan sun yi wani sabon program (update) na wayar ka ka saka domin da yin haka ne suke toshe dukkan wata kafa da masu rubuta virus suka samu suke cutarwar.
 • Mataki na uku Kayi installing wani anti-virus ko kuma wani program da zai tsare maka ita wayar taka daga shigowar virus

Daga karshe nake kira ga dukkan wanda yasan yana amfani da waya musamman wayar da take da dan tsada ya rinka yin software update na wayar domin mahimman cin sa, da fatan wannan rubutu zai anfanar.