Categories
Programming Software

ALBASHIN PROGRAMERS 8 MAFI TSOKA

Shi dai programming language a Hausance ka iya kiranshi da yaren da ake iya yiwa kwamfuta magana dashi har ta fahimci me kake son tayi. Shi wannan yare ba irin yaren mu bane saidai mu mutane mu muka zauna muka shirya mata yadda zata rika fahimtar umarni da ake son ta gabatar da kuma yadda ake son ta gabatar baki daya.

Abinda zai baka mamaki shine yadda irin wadannan yaruka kullum ake kara kirkirosu sannan kuma ka samu irin wadannan sababbin su danne tsofaffi duk da cewar akwai wadansu yarukan da suka dade sun shahara kuma har zuwa wannan lokacin su jan zarensu bai kuma tsinke ban.

Duk da cewar zaka iya samu dalibi ya mayar da hankalinshi akan wani yaren kwamfuta wanda yake tsammanin zai iya biya masa bukata amma a zahiri yakasance ko kadan wannan yaren bashi da wani amfani a wurinshi.

Idan ana maganar biyan kudin aiki ko albashi da kuma wane programming language zan koya don in samu kudi sosai to ya danganta da shekarar da ake amfani da wannan programing din, da kuma irin abin da ake yi dashi na kawo kudi. Duk da cewar ba dole bane ace kamfanin da suka dauke ka aiki duk da iyawarka a daya daga cikin yarukan nan ace su iya biyanka albashin da wani kamfani ke biyan ma’aikatansa.

A wannan darasi zamu kawo muku programming language guda 8 wadanda aka fi samun kudi da su a shekarar 2018 da ta gabata.

Go Programming Language

Wannan programming Language ana biyan wanda ya koye shi ya samu aiki a babban kamfani suna biyan karancin albashi a shekara $110,000 (N39,710,000.00). shi wannan programming language na Go yaren wanda al’umma suka taru suka kirkireshi (open source programming language) wanda ake iya kirkirar manhajoji (software) masu sauki da masu nagarta sosai. Dalilin shaharar wannan programming language na Go saboda kamfanin Google da Facebook da Netflix da SoudCloud da Adobe da Dropbox duk suna amfani da shi wurin kirkirar manhajojin da zasu iya aiki a software dinsu. Wadannan kamfanoni suna son wannan yaren ne saboda sauki gabatar da aiki, saurin tashi, amfai da memory a lokacin da ake son ayi aiki da shi. A takaice dai wadansu ma suna ganin wannan yaren shi zai zama yaren server a nan gaba.

Objective-C

Matsakaicin albashin da ake iya biyan wanda ya koyi wannan programming language din Obhective-C shine $108,000 (N38,988,000.00) Shi wannan yaren ana amfani da shine wajen kirkiran manhajoji da suke iya in aiki a Mac OS X da kuma iOS. Wannan programming language na daga cikin yaren da yake baiwa yan kasar Amurka aiki yi da duka samun riba.

Python

Babban ma’aikacin da ya iya Phython Programming Language yana daukar albashi $105,000 (N37,905,000.00). Python yaren kwamfuta ne wanda aka fi mayar da hankali game da kirkiran manhajojin da suke iya sarrafa bayanai na data analysis, lissafe-lissafe, fahimtar ilimin karafan kwamfuta (machine learning), kirkirar shafukan intanet da dai makamantansu. Manyan kamfanonin da suke daukar masu ilimin Python sune kamfai NASA da Google. Ana kuma saka wannan yaren na python na daya a mafi shaharar yaren kwamfuta a duniya da kuma shine na biyar a neman sanin yadda ake koya a duk programing da ake da su.

Ruby on Rails

Matsakaicin albashin da wanda ya koyi yaren Ruby on Rails kuma ya samu aiki shine $89,774 (32,408,414.00) kamar yadda kamfani Glassdoor ya fada. Ruby ya samu daukaka ne bayan da ya shahara wurin amfani da shi a shafukan intanet domin kirkirar manhajoji na intanet. Ana amfani da Ruby wurin yin application masu matukar muhimmanci da kuma amfani.

C#

Kamar yadda kamfanin Quartz Media suka fada, matsakaicin albashin da ake biyan wanda ya iya C# shi ne $89,000 (N32,129,000.00). C# ya shahara kuma ya samu karbuwa tun a lokaci da kamfanin Microsoft suka kirkiro shi. Shi wannan yaren ana amfani da shi domin kirkirar application da zasu yi aiki a Desktop Computer ko a Intanet. Idan kana son ka rika kirkirar application da suyi Microsoft to ka koyi C#.

Java

Java yana daga cikin programing language da aka fi nema kuma ake biyan albashin sa daga $74,000 (N26,714,000.00) zuwa (N46,930,000.00) $130,000 ga Senior Java Developer. Baya da cewar shi yare ne da ake yin manhajoji na wayar android, haka ana kuma amfani da shi wurin kirkirar manhajoji da ake saka su a cikin motocinmu da kuma bankunan mu. Java programming language ne mai kyau da ya kamata mutum ya koya.

Swift

Kamar yadda Payscale suka ce, wanda ya iya yaren Swift yana iya samun albashi matsakaici na $78,933 (N28,494,813.00). Shi wannan yaren na Swift da shi ake amfani ake kirkiran manhajojin MacOS da iOS da watchOS da tvOS wanda dukkansu kayan kamfanin Apple suke amfani da su.

Kotlin

A fadin kamfanin Paysa, wanda ya iya yaren Kotlin yana samun matsakaicin albashin da ya kai $66,186 (N23,893,146.00) a shekara. Wannan yare Jetbrains ne ya kirkiroshi kuma yanzu haka shine halattacen yare da ake amfani da shi domin kirkirar manhajoji da zasu yi aiki a wayoyin Android.

A shekarar 2017 ne aka kirkiri wannan yaren kuma ya samu karbuwa sosai domin yana aiki tare da Java, sannan kamfanin Google ke taimaka wurin lura da gyaranshi sa, sannan samun karbuwarsa a wurin jama’a ya sa ya zama yare wanda ya kamata mutum ya koya.

Rufewa

Yana da kyau mai karatu ya sani, ba kamar yadda muka fada ba, wannan albashi ya danganci wasu irin ma’aikata ne da kuma ma’aikatar da mutum ya samu aiki, kada wani dan karamin kamfani ya dauke ka aiki ka ce ka iya wadannan programming din kuma kana bukatar sai an biyaka wannan albashi. Hasali ma manyan ma’aikata Senior Developer su ake magana a wannan mukalar.

Categories
Software

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (2)

Fashin baki ga kowane ra’ayi guda cikin shidan nan

1                Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming ba.

Ga waɗanda suka tsinci kansu a cikin karatun kwamfuta kuma suka dace da shiga bangaren Programing Language to shawarar da zamu basu ita ce su koyi Python.

2                Domin amfani yara.

Duk wanda yake son ya koyin yaren kwamfuta domin ya kirkiri wata manhaja domin kanan yara ko kuma ya koyi yaren da yake son ya koyawa yaransa suma a fara damawa da su a kan abin da ya shafi Programing Language to ya koyi Python.

3                Domin jin dadi da nishadantarwa

Wanda yake da ra’ayin yin Programing Language  amma kuma yana yin shi domin jin dadi da debe kewa, da nishadantarwa, to akwai tambayoyi da za ayi masa, irin amsar da ya bada ita ce sakamakon idan ya kamata ya kai kanshi wurin abin da ya cancanta ya koya.

Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ba shi da shi, kawai shi dai ya son a koya mishi wanda zai fara to yana da zabi guda hudu.

 1. Yana son ya koyi programmin language cikin ruwan sanya – to ka koyi Python.
 2. Idan kuma kana son ka koyi Programing Language da ya fi cancanta da kyau wurin koya – to ka kuyi Python
 • Idan kuma kana son ka koyi Programing Language amma ta yare mai dan wahala to a nan zamu baka zabi ka koyi yaren da ake amfani da shi wurin sarrafa moto ta hawa waɗanda suke da tsarin manu’al da Idan ka na son zaka koyi yaren da zaka rika yin manhajoji da zasu rika yin aiki a motoci na manu’al sai muce ka koyi yaren C Programming. Idan kuma kana son ka koyi yaren da zaka rika yin manhajojin da zasu rika yin aiki a cikin motoci auto sai muce ka koyi JAVA Programming.
 1. Idan kuwa yana son ya koyi Programing Language ta hanyar da tafi kowacce wahala wacce zai samu sauki idan yana son nan gaba ya koyi wani yare sai muce ya koyi C++ Programming.

4.      Yana da ra’ayin yin programming

Shima wanda yake da ra’ayin yin Programing Language , shima za a tambaye shi Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi. Sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma bangaren me? A wannan wurin yana da zabi guda hudu (4).

a)    Ina son in rika yin webdesign.

Ka na son web site da zai rika yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta zama e sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, zamu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta bangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi baka sha’awa. Idan yace lego sai muce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai muce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa yace shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma yace yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na dai sai muce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiyya da fasaha, zamu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e to sai muce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin dadi da nishadi ne sai muce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language ina son in rika yin manhajojin da zasu rika aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya kirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi kirar Android. Idan yace ya son ya yi aiki da wayoyi kirar Apple sai muce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi kirar Android sai muce ya koyi yare JAVA.

d)   Domin hada kayan Games

Idan kuwa yace yana son bayan ya iya programming ɗin sa ya rika yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin game kamar playstation da irinsu Nitando da dai makamantansu sai muce ya koyi C++  amma sai dai yana dan wahalar koya.

5.      Yana son karawa kanshi sani a cikin Programing Language

Ga wanda daman ya dan san programming kuma yana son kawai ya karawa kanshi sani ne ko kuma sanin madogara shima za a tambaye shi Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi. Sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma bangaren me? A wannan wurin yana da zabi guda hudu (4).

a)    Ina son in rika yin webdesign.

Ka na son web site da zai rika yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta zama e sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, zamu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta bangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi baka sha’awa. Idan yace lego sai muce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai muce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa yace shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma yace yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na dai sai muce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiyya da fasaha, zamu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e to sai muce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin dadi da nishadi ne sai muce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language ina son in rika yin manhajojin da zasu rika aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya kirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi kirar Android. Idan yace ya son ya yi aiki da wayoyi kirar Apple sai muce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi kirar Android sai muce ya koyi yare JAVA.

d)   Domin hada kayan Games

Idan kuwa yace yana son bayan ya iya programming ɗin sa ya rika yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin game kamar playstation da irinsu Nitando da dai makamantansu sai muce ya koyi C++  amma sai dai yana dan wahalar koya.

A darasin mu na gaba da yardar Allah za mu yi cikakken bayani a kan mataki na karshe wato IDAN MUTUM NA SON YA SAMI KUDI A BANGAREN PROGRAMMING LANGUAGE ME ZAI KARANTA.

Mu yi karatu lafiya

Categories
Daga Edita

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (1)

Mene ne Programing Language ?

Wani tsararren rubutu ne da ake yi domin kurman mashin, amma kuma ya sanya shi ya kasance mai ji kamar mai kunne.

Daga ina ya kamata ka fara?

Mene ne dalilin da ya sa ka ke son ka fara yin Programing Language ? Wannan ita tambayar da ya kamata ka fara yi wa kanka da kanka, kasancewar kowane Programing Language  akwai abin da ya ke yi, da kuma abin da ake iya yi da shi, da kuma irin mashin ɗin da ya ke iya sarrafawa, da kuma alaƙar da take tsakanin sa da sauran Programing Language da ake da su.

Programing Language nawa ne a duniya?

Programing Language suna da matuƙar yawa, tun daga wanda ake amfani da shi a cikin ƙananan na’urori da kuma manya, da waɗanda ake amfani da su a cikin gida da kuma ma’aikatu da kuma waɗanda ake amfani da su a harkokin mu na yau da kullum. Sai dai a cikin waɗannan Programing Language  ɗin akwai waɗanda suka sami karɓuwa akwai waɗanda ko sunan su ma ba mutane da yawa ba su san su ba.

A wannan muƙalar zamu ɗauki yaren Kwamfuta waɗanda su ka fi shahara guda tara (9) a wannan zamani, waɗanda kuma da su ne duniya ke taƙama kuma kusan duk wani abu da za ka gani a wannan lokaci idan dai na’ura ce, tun daga kayan wasan yara (games) da na’urorin da manya suke amfani da su kamar wayoyin tafi-da-gidanka, da ma manya da ƙananan manhajoji dukkaninsu ba sa wuce ɗaya daga cikin waɗannan Programing Language  ɗin.

Wadannan programming guda tara ne, waɗanda suka hada da

 • Python
 • JAVA
 • C
 • PHP
 • C++
 • JavaScript
 • C#
 • Ruby
 • Objective-C

Mene ne dalilin ya zai sa na koyi Programing Language ?

Akwai ra’ayin mabambanta ga masu koyon yaran kwamfuta. Waɗannan dalilai sun sha bambam, sai dai daga baya ra’ayin yana komawa ga mataki na karshe amma kuma dukkansu babu matsala ga wanda mutum ya ɗauka.

An tattara ra’ayoyin jama’a masu koyon Computer Programming har gida shida (6), ta hayar la’akari da ta ina mutum ya ɓullo da kuma ina yake son ya ɓulla a wannan harkar.

 • Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming
 • Domin amfani yara.
 • Domin jin daɗi da nishadantar wa
 • Yana da ra’ayin yin programming
 • Yana son ƙarawa kanshi sani a cikin Programing Language
 • Domin ya sami kudi.

A darasin mu na gaba za mu ɗauki kowane ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi mu bada shawara ingantacciya ga duk mutumin da yake son ya koyi programmig language cikin wadannan ra’ayoyi shida.

In Sha Allah.