Categories
Duniyar Waya

CIKAKKEN BAYANAI AKAN YADDA AKE AMFANI DA PLAN B DOMIN GANO WAYAR ANDROID DA TA BACE

Ma’aikatar lura da tsaron lafiyar wayoyin hannu game da abinda ya shafi Virus na waya mai suna Lookout sune suka kirkiri wani application na Android  suka kuma sake shi kyau ta mai suna Plan B.

Plan B application da aka yi shi musamman domin wayoyin zamani masu tsarin Android, wanda wannan application yake taimakawa matuka wajen gano inda wayar take a lokacin da ta bace ko kuma aka sace ta.

Yadda ake amfani da wannan application shien lokacin da ka nemi wayarka ta Android ka rasa, kuma ka tabbatar da cewar ta bace, ko kuma kana da yakinin cewar sace ta aka yi, sai ka shiga Internet kayi downloading din wannan software sannan kayi installing din shi akan internet din. Amma kafin ka saka shi wannan application a wayar taka da ta bace kana bukatar ka shiga shafinnan na Android Market ta hanyar amfani da email na google (gmail). Da zarar shi application din y agama downloading a cikin wannan shin na Android Market zai yi kokarin binciken inda wannan wayar take ta hanyar aiko da sakon email zuwa wannan akwatin da ka shike wannan shafi da shi (gmail), bayan wasu yan lokuta kuma zai ci gaba da aiko maka da hotunan taswirar wurin da wayar ake amfani da ita a halin yanzu. Haka zai ci gaba a duk tsawon mintina goma.

Idan kuwa bayan mintina goma baka sakon email cikin akwatin k aba, to sai ka aikawa kanka sakon SMS zuwa wayar taka da kalmar “locate”, yin hakan zai baiwa shi wannan application damar ya fara aiki kai tsaye. Shi kanshi Plan B yak an aika da sakon SMS zuwa ga wayar ka ta hanyar neman ta “GPS” ko da kuwa ba a kunna GPS din wayar ba.

Ko da yake shi wannan application a lokacin da muke tattara wannan bayanai yan aiki ne kawai a kasar Amurka ga masu amfani da AT&T da masu amfani da Sprint, da kuma masu amfani da Verizon da kuma masu amfani da T-Mobile. Sannan shi wannan application na Plan B baya aiki sai akan Android 2.0, haka kuma ba zai yi aiki ba idan an kashe waya, ko kuma an cire SIM ko kuma wurin da babu network.

Yadda ake yin amfani da Plan B a takaice

1)   Ka shiga shafi na Android Market da Gmail account.

2)   Ka rubuta Plan B a wurin bincike, ko kuma ka shiga shafin Plan B Market

3)   Kayi installing Plan B a wayar da kake son ka gano ta ta internet (wato zai fito maka da jikin wayar ta internet sai ka saka wayar ka a ciki).

4)   Da zarar ka gama installation din shi zai aiko da sakon email cikin akwatinka nag mail yana fada maka wurin da zaka samu wayar ka.

5)   Da zarar Plan B ya gano wayar taka, sai ka sake duba cikin akwatinka zaka gay a turo maka da taswirar wurin da wayar taka take ta amfani da Google Map yana kuma nuna maka daidai wurin da wayar take. Haka zai ta aikawa bayan minti goma goma.

6)   Idan bayan minti goma da downloading baka iya samun bayanan inda wayar take ba, sai ka aika da sakon SMS a wata waya zuwa ga wayar taka ka rubuta “locate”.

7)   Bayan ka gano wayar taka yana da kyau ka yi downloading cikakken application din Lookout Mobile Security, domin samun ingantacce tsaro.