Categories
Hardware

PORT: Mahada a Computer

Port

Port wuri ne da yake baka damar hada kayan computer da suke wajen system unit kamar printer da scanner da makamantansu. To shi ramin da ake hada wannan wayar da ta fito daga jikin shi wancan hardware zuwa jikin system unit shi ake kira da port, ko da yake wajen da ake hada wadannan hardware sun kasu kashi biyu.

1.      Serial Port

2.      Parallel Port

Serial Port

Shi serial port daya ne daga cikin port da ake hada kayan computer da system unit amma ana amfani da serial port a irin kayan computer wadanda ba sa bukatar sauri wajen isar da sako ko kuma fitar da sako. Domin serial port yana aikawa da sakon data  daya ne a kowanne dakika daya. Kayayyakin da suke zuwa da mahada irin ta serial port su ne mouse da keyboard da kuma modem. Sannan serial port yana amfani da RS-232 ko RS422 wanda shi ke tabbatar da yawan hakora da yake da shi, kusan serial port da ake amfani da su guda biyu male 25-pin (mai hakora 25) da kuma male 9-pin (mai hakora 9)

Ba kamar serial port ba, shi parallel port mahada ce da zata iya turo da sakon data fiye da bit daya a dakika daya, dalilin kirkiran paralle port shine domin magance matsala da za a iya samu a wajen kayan hardware da suke bukatar sauri wajen isar da sako.

 Parallel Port

Mafi yawancin Printer da ake da su suna amfani da mahadar Parallel port ne, wanda ya ke da zubin hakora 25 (famale 25-pin). Shi parallel port yana iya karba ko aiko da sako da ya kai bit 8 a ko wane dakika ta layi guda takwas a lokaci guda. Wani lokaci ana kiran Parallel Port da Centronics bayan da kamfanin da suka fara kirkiran shi su ka fitar da tsari da kuma dalilai da yasa computer za ta samu alaka tsakaninta da printer. Kamar Serial Port suma Parallel sun kasu kashi biyu, akwai Parallel port da ake kira da EPP (Enhanced Parallel Port) da kuma ECP (Extended Capabilities Port) suna amfani da mahada irin ta Centronics port, amma sun fi centronics port saurin aikawa da data har sau goma.