Categories
Duniyar Waya

Wayoyin da zasu daina aiki da WhatsApp

Cikin kokarin da kamfanin da yake ginawa da lura da Mahnajar aikawa da sako na WhatsApp suke yin na ganin sun inganta wannan manhajar ta su domin jin dadin masu mu’amala da ita suka fitar da sunayen wadansu wayoyin komai da ruwanki (Smart Phones) wadanda daga karshen wannan shekarar manhajar ta WhatsApp ba zata sake yin aiki ba.

Duk da kamfanin yace wannan ba karamar barazana ba ce gare su amma kuma sun ce sun dauki wannan mataki ne domin su inganta wannan manhaja.

Manhajar WhatsApp dai ita ce manhajar aikawa da sako da aka fi amfani da ita a duniya domin kusan kashi casa’in na wayoyin hannu suna amfani da wannan manhaja ta WhatsApp.

Idan aka tsinci wayarka a cikin jerin wadannan wayoyin to ka sani cewar daga karshen watan Disamba na 2016 WhatsApp din wayar ka zai daina aiki.

Dukkanin wayoyin blackberry har da Blackberry 10, su Blackberry sune da kansu za su cire wannan manhajar daga wayarsu domin suna kokarin fito sa ta su manhajar.

Dukkan wayoyin da suke amfani da Manhajar Symbian wanda ya hada da Nokia 500, Nokia E6, Nokia 5228, Nokia 5230, Nokia E63, Nokia 5233, Nokia E66, Nokia 5235, Nokia 5250, Nokia E7, Nokia 5320, Nokia E71, Nokia 5530, Nokia E72, Nokia 5630, Nokia E73, Nokia 5700, Nokia E75, Nokia 5730, Nokia E90 Communicator, Nokia 5800, Nokia N76, Nokia 600, Nokia N78, Nokia 603, Nokia N79, Nokia 6110, Nokia N8, Nokia 6120, Nokia N81, Nokia 6121, Nokia N81 8 GB, Nokia 6124,Nokia N82,Nokia 6210,Nokia N85, Nokia 6220, Nokia N86 8 MP, Nokia 6290, Nokia N95, Nokia 6650 Fold, Nokia N95 8 GB, Nokia 6700, Nokia 6710 Navigator, Nokia N96, Nokia 6720, Nokia N97, Nokia 6730, Nokia N97 mini, Nokia 6760 Slide, Nokia X5-01, Nokia 6790 Surge, Nokia X6, Nokia 700, Nokia X7, Nokia 701, Samsung GT-i8510, Nokia 808 PureView, Samsung GT-l7110, Nokia C5, Samsung i8910 Omnia HD, Nokia C5-03, Samsung SGH-G810, Nokia C6, Samsung SGH-iNNN, Nokia C7, Samsung SGH-L870, Nokia E5, Sony Ericsson Satio, Nokia E51, Sony Ericsson Vivaz, Nokia E52, Sony Ericsson Vivaz Pro da kuma Nokia E55.

Dukkan wayoyin Nokia S40 wadanda suka hada da Nokia Asha 201, Nokia Asha 300, Nokia Asha 302, okia Asha 303, Nokia Asha 306, Nokia Asha 311,Nokia C3-00, Nokia C3-01, Nokia X2-00, Nokia X2-01 and Nokia X3-02,Window phones 7.1,iPhone 3GS/iOS 6, Andriod 2.1 da Andriod 2.2