Categories
Hannunka mai sanda

AN KUWA SAMU CANJIN? (1)

Kila kafin mutum ya amsa wannan tambaya, abin da ya dace ya fara aunawa shi ne, mene ne canjin da ake nema tukunna? Canjin mulki daga wata jam’iyya zuwa wata ko daga wani mutum zuwa wani? Ko kuwa canjin lamurran rayuwa daga lalatattu zuwa kyawawa? Ko canji daga tsofaffin yanaye-yanayen rayuwa zuwa ga sababbi? Ko kuwa dai canji daga munanan halaye zuwa ingantattu, domin samun ci gaba? Idan ba wadannan ake bukata ba, to ko kuwa dai canjin da ake sa ran gani shi ne na daga tsarin mulkin danniya da babakere zuwa ga na salama? Ko kuwa wane irin canjin ne ake magana?

A Nijeriya dai tun daga lokacin da aka kada kugen siyasa da neman kuri’a, canjin da ake ta kururutawa bai wuce na abubuwa uku ba:

  1. Canjin siyasar da ke mulki, wato PDP zuwa wata daban, musamman APC.
  2. Canjin tsarin mulkin da aka kwana ana ta yi tun daga 1999 zuwa yau, wanda bisa ga dukkan alamu, bai yi wa yawancin al’ummar kasar dadi ba.
  3. Canza halayen al’ummar kasar na cin hanci da rashin bin doka da oda da yin awon gaba da muggan halaye da ke wa cigaban kasar nan tarnaki a cikin tsawon zamani.

Idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a cikin mako biyu da suka wuce za mu iya cewa ba ko tantama an samu canji, don ko ba komi an kayar da jam’iyyar da ke mulki ta PDP a zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya, wanda kuma shi ne yawancin al’ummar kasar nan suka dinga zugugutawa da nema a cikin watannin da suka wuce, sai dai kila ba nan ne canjin ya kamata ya tsaya ba, bisa la’akari da nau’o’in canjin da muka lissafo a sama.

Abin da kila ya rage shi ne canji a salon mulki da tsarin manufofin tattalin arziki da siyasa da zamantakewa, wanda shi kuma bai samuwa har sai gwamnatin Buhari ta hau mulki daga ranar 29 ga watan Mayu, 2015. Kenan, ba za a ga wani haske ba a wannan bangare har sai mai wuka da nama ya kama aiki, rigi-rigi.

Shi kuwa canji na munanan halayen al’ummar kasa da ya zame wa kasar kadangaren bakin tulu a tsawon shekaru, ya kamata a ce mun fara ganin sonsomin sa tun yanzu, ba wai nan gaba ba. Me ya sa?

Mu dubi batun da kyau. Cin hanci da almundahana a tsakanin yawancin ma’aikatan gwamnati a kowane mataki a cikin kasar nan, ba abu ne da sai an jira Buhari ya hau karaga ba, in da gaske muke na neman canjin. Haka kuma rashin bin doka da oda, ba na tsammanin sai mun jira Buhari da mukarrabansa sun zaune kujerar Aso Rock za mu ga canji.

Haka sauran muggan halaye da suka hada da sata da fashi da makami da karuwanci da luwadanci da tauye awo da cin yadi a wajen madunka da satar jarabawa a wajen dalibai da sayar da maki daga malamai da gulma da zunde da ashararanci da banga da shan kwaya da sauran abubuwa irin wadannan ba na tsammanin muna jiran sai Buhari ya hau ne, ya yi doka, sa’annan canji a wannan bangare zai tabbata a cikin kasa.

Daga wannan hasashe za mu iya cewa canjin da ke da muhimmanci ya samu a cikin kasar nan, Buhari ya ci zabe, amma canjin da ya fi wannan muhimmanci, na gyara lamurran kasa da inganta ta da ciyar da ita gaba ba na Buharin ba ne kawai, ba kuma sai an jira Buhari ya haye bisa karagar mulki ba. Abu ne da ni da kai da ku da su, mu duka baki daya za mu iya kawo shi domin daidaita lamurra. Ta yaya?

Me ya sa da Buhari ya ci zabe darajar kasuwancin hannun jari ta karu, ta yi armashi har ta kai matsayin da aka dade ba a ga irin sa ba a tsawon zamani? Buhari ne ya ce wa kasuwar ta gyaru ko ta ingantu? Ko alama, kanshin canjin ne da kasuwar ta ji, ya sa ta farfado. To za ta kara ingantuwa da bunkasa idan ‘yan kasuwar sun yi abin da ya dace, ban da shigo wa kasuwar ta bayan fage da zurmuke da saye da sayarwar karya don samun kazamar riba. Kenan canjin a fagen kasuwancin hannun jari da tattalin arziki zai iya samuwa kafin Buhari ya kai ga hayewa kujerar mulki.

Haka kuma da darajar Naira ta inganta bayan ta yi faduwar rimi, shi ma ai ba a ko fara mulkin Buharin ba, me ya nuna mana kenan? Sai fa cewa ai dukkan lalacewar lamurra na hannun ‘yan Nijeriya, in har gwamnati mai ci na da laifi, to ‘yan kasuwar mu da masu kula da lamurran tattalin arzikinmu, su ma suna cikin lalacewar dumu-dumu. Shin su wa suka saye dala suka boye kafin zaben Buhari, gwamnatin PDP? Ko alama, mu din ne dai da muggan halayenmu na ko-in-kula da kuma halin dan kaza da suka yi mana katutu, mu ke da laifi. Shi ya sa bayan Buhari ya ci zabe, ba wanda ya ce mana kanzil, sai ga shi mun fiddo dalolin da muka kimshe a gidaje, nan take darajar Naira ta daga a ‘yan kwanakin nan. Kenan muna da hannu wajen lalacewar lamurra. Ba Buhari ne canji ba. Buhari zai kasance ne kurum a matsayin madafar da za a dafa don ci gaba daga inda ake.

Me ke nan ya dace a ce yanzu ana yi ko za a iya yi domin kawo canji na hakika a cikin kasa, har kafin jagoran canjin ya hau?

Za mu ci gaba.