Categories
Software

TSARIN RABA DATA/MB A LAYIKAN MTN: Yadda mutum zai iya samma wani data ko MB din sa a layin shi na MTN

Idan mutum ya sayi MB kuma yana son ya raba shi ko samma wani data ko MB domin shima ya ci moriyar shi to zai iya bi ta wannan hanyoyi da zamu fada kamar haka.

  1. Ba kowane tsarin data bane yake baka damar samma wani MB, dole sai idan ka mallaki data ta hanyar da zamu numa a kasa idan baka da daya daga cikin wannan tsari to ba zaka iya samma wani MB’n ba.
  2. Domin yi rigista zaka dannan *123*2*1# ko kuma ka aika da sakon REG zuwa Da zarar kayi daya daga cikin wannan, kamfanin MTN zasu aiko maka da sakon wata lamba ta musamman wacce itace lambar sirrinka da zaka yi amfani da ita wurin raba shi wannan MB.
  3. Ana bukatar ka canza wannan lambobi guda hudu da suka turo maka domin kusan da farko kowa suna aiko mishi da 0000 ne, saboda haka ya zama wajibi ka canza zuwa wanda ranka yake so ta hanyar danna *123*2*5# ko kuma aikawa da sako sms kamar haka Change Tsohon_PIN Sabon_PIN Sabon_PIN misali kamar haka 0000 1234 1234. Yadda abin yake kuwa shine 0000 sune lambar da MTN suka aiko maka 1234 sune lambar da kake son suyi amfani da ita. Sake saka 1234 yana nunawa MTN cewar kasan abin da kake son a canza maka. (1234 da muka yi amfani da shi misali ne kawai, zaku iya canza naku)
  4. Bayan ka canza wadannan lambobi na sirri to kana bukatar ka saka wadanda kake son su zasu amfana da wannan tsari na bayar da MB, domin yin haka shi zai hana wani koda ya san lambobin sirrinka ya iya aikawa da kansa MB. Idan kana son ka saka wani a cikin wannan tsari kawai sai ka danna *131*2*2# ko kuma ka aika da sakon Add lambar wayar mutum lambar sirrinka zuwa 131 misali Add 08000000000 1234 zuwa Wannan tsarin yana ba mutum damar ya saka har mutne biyar (5) da zasu rika samun garabasar MB daga wurinshi.
  5. Da zarar ka saka wanda kake bukatar ya rika samun kyautar MB, duk lokacin da zaka sammishi MB sai ka danna *131*2*3# ko kuma aika da sakon SMS da Share Lambar Sirrinka zuwa ga 131

Tsarin da ake iya transfer na MB ga layukan MTN

Duk wanda yake son ya samma wani DATA ko MB sai ya sayi daya daga cikin wadannan tsarin

Data da zaka iya siya Kari ko yauta da MTN zata bada Kudin Data (=N=) Yadda ake siyan wannan tsari
250MB 125MB N1,300 *109#
500MB 250MB N2,000 *110#
1GB 500MB N3,500 *111#
3GB 1.5GB N6,500 *129#
5GB 2.5GB N8,000 *101#

 

Wannan shie

Idan mutum ya sayi MB kuma yana son ya raba shi ko samma wani data ko MB domin shima ya ci moriyar shi to zai iya bi ta wannan hanyoyi da zamu fada kamar haka.

  1. Ba kowane tsarin data bane yake baka damar samma wani MB dole sai idan ka mallaki data ta hanyar da zamu numa a kasa idan baka da daya daga cikin wannan tsari to ba damar samma wani MB naka.
  2. Domin yi rigista zaka dannan *123*2*1# ko kuma ka aika da sakon REG zuwa Da zarar kayi daya daga cikin wannan, kamfanin MTN zasu aiko maka da sakon wata lamba ta musamman wacce itace lambar sirrinka da zaka yi amfani da ita wurin raba shi wannan MB.
  3. Ana bukatar ka canza wannan lambobi guda hudu da suka turo maka domin kusan da farko kowa suna aiko mishi da 0000 ne, saboda haka ya zama wajibi ka canza zuwa wanda ranka yake so ta hanyar danna *123*2*5# ko kuma aikawa da sako sms kamar haka Change Tsohon_PIN Sabon_PIN Sabon_PIN misali kamar haka 0000 1234 1234. Yadda abin yake kuwa shine 0000 sune lambar da MTN suka aiko maka 1234 sune lambar da kake son suyi amfani da ita. Sake saka 1234 yana nunawa MTN cewar kasan abin da kake son a canza maka. (1234 da muka yi amfani da shi misali ne kawai, zaku iya canza naku)
  4. Bayan ka canza wadannan lambobi na sirri to kana bukatar ka saka wadanda kake son su zasu amfana da wannan tsari na bayar da MB, domin yin haka shi zai hana wani koda ya san lambobin sirrinka ya iya aikawa da kansa MB. Idan kana son ka saka wani a cikin wannan tsari kawai sai ka danna *131*2*2# ko kuma ka aika da sakon Add lambar wayar mutum lambar sirrinka zuwa 131 misali Add 08000000000 1234 zuwa Wannan tsarin yana ba mutum damar ya saka har mutne biyar (5) da zasu rika samun garabasar MB daga wurinshi.
  5. Da zarar ka saka wanda kake bukatar ya rika samun kyautar MB, duk lokacin da zaka sammishi MB sai ka danna *131*2*3# ko kuma aika da sakon SMS da Share Lambar Sirrinka zuwa ga 131

Tsarin da ake iya transfer na MB ga layukan MTN

Data da zaka iya siya Kari ko yauta da MTN zata bada Kudin Data (=N=) Yadda ake siyan wannan tsari
250MB 125MB N1,300 *109#
500MB 250MB N2,000 *110#
1GB 500MB N3,500 *111#
3GB 1.5GB N6,500 *129#
5GB 2.5GB N8,000 *101#
Categories
Duniyar Waya

Yadda Ake Sa Wayar “CHINA PHONE” Ta Dinga Shiga Intanet Da Layukan Najeriya

A yanzu kana iya sa wayarka da ake kira “China Phone” ta yi maka browsing ta hanyar amfani da kowanne ɗaya daga cikin layukan sadarwa na Nijeriya wato MTN, GLO, AIRTEL, ko kuma ETISALAT. Nigeria tafi fice a cikin ƙasashen dake amfani da wayoyin salula ƙirar China. Kana iya cewa ma mafi yawan kayayyakin da ake amfani da su ƙirar China a wannan ƙasar tamu babu kamar wayar hannu ta salula. Sauƙin su da kuma samun a kowanne saƙo da lungunan kasuwanni ya sa suka samu karɓuwa A yawan lokaci mafi akasarin mutane na son sayan wayoyi ƙirar China ne saboda kyawunsu da daɗin ko sauƙin sha’anin su. Hakan ya sa ma har suke iya gogayya da sauran kamfononin waya kamar su Nokia, Samsung, LG da dai sauransu. Kai hatta wayoyin dake da ake kira da komai da ruwanki (smart phone) kamar su Blackberry, iphones da kuma Andriod su kansu ba ƙaramin gogayya suke fuskanta ba daga wayoyi ƙirar China. Kamar yadda aka sani ne cikin kowane da daɗi akwai rashin sa. Domin wani abin takaici da waɗannan wayoyin shi ne yadda kamfononin sadarwan mu ba sa iya turo maka da tsarin shiga intanet’ (Automatic Settings) kai tsaye kamar yadda suke turo wa wayoyi saɓaninsu. Duk wayar da ba ta da GPRS to fa ba ta iya shiga Intanet, domin ba ka da damar kaima ka iya yin bincike da kuma ninƙaya a sarari na Intanet. Shiga cikin irin wannan matsalar ya sa ni bincike har na gano yadda ake iya canza wannan tsarin: 1. Shiga “menu” sannan ka hau” Service/Intanet access” 2. Ka taɓa “service/Intanet Access” sannan ka zaɓi “wap Browser” 3. Buɗe ‘Wap browser’ sai kuma ka shiga “settings” 4. Buɗe “Edit profile” sai ka zaɓi wanda kake so 5. Zaɓi “Edit profile” sai ka shigar da ɗaya daga cikin bayanan da za mu jero a ƙasa wanda ya yi daidai da layin wayarka. Homepage: MTN: GLO: AIRTEL: Wap.ng.airtel.com@ ETISALAT: Wap.etisalat.com.ng@ 6. Sai ka shiga “Data Account” ka zaɓi wanda kake so misali China Mobile GPRS 7. Wajen da ake rubuta “Connection type” sai ka rubuta “WAP 8. WAJEN “Proxy/IP Address sai ka zaɓi irin layinka ka rubuta waɗannan lambobi kamar haka: MTN: 010.199.212.002 AIRTEL: 072.018.254.002 GLO: 190.129.010.245 ETISALAT:072.055.142.251 9. Sai wajen da aka rubuta “Security” sai ka sa “off” 10. Username: Wap. Password: Wap (idan ka gama sai ka danna “yes” sannan kai amfani da hanyar fita ta baya “back button”) ka fita. 11. Ka buɗe “Data Account” ka zaɓi “GPRS” 12. Ka buɗe “Data Account” ka zaɓi, zaɓin ka na shida a sama. 13. Sai gyara ‘account’ ɗin ka kamar haka: APN: MTN: web.gprs.mtnnigeria.net GLO: wap.gloworld.com AIRTEL: wap.ng .airtel.com ETISALAT: wap.etisalat.com.ng 14. Wajen “Username” sai ka rubuta “ wap. Password: shima ka rubuta wap. Kana kammala wa sai ka fito da ga wajen. Ina mai tabbatar maka cewa kana yin haka to wayarka ƙirar China ka za ta fara aiki wato browsing. Idan ka gwada ya yi to sai ka samma abokai da suke da irin waɗannan wayoyin kuma suna sha’awar su shiga wannan tsarin, amma basu san yadda ake yi ba. Abdullahi Muhammad Jime (Shugaban Makarantar Diligence School Kaduna)

Categories
Duniyar Waya

YA AKE YIN FILASHING NA WAYA?

Da zaka tara masu amfani da waya, ka tambaye su mene ne filashing? Zasu gaya maka cewar filashing shine idan wayarka ta sami matsala a kai ta wajen gyara a gyarata. To haka abin yake a ilmance ko ba haka ba?

Anan kasar tamu ta Najeriya idan kace ayi maka filashing ko kace wayar ka ta sami matsalar OS nata, kana ganin masana suna hada ta da wata ‘yar bakar waya, su kuma hada ta da Computer, sannan su kuma yi wasu ‘yan siddabaru, sannan su baka ita ka gani ta dawo dai dai kamar babu abinda ya taba samunta.

To Me Ake Nufi Da Filashing Na Waya?

Gaskiya mu a Najeriya da kuma sauran makwabtamu dake Afirka zaka samu bamu da tsari irin tsarin da sauran kasahen da suka cigaba su keyi, a kasa irin su America ko England irin su Saudi Arabia da dai makamantansu suna da wani tsari da, zaka sayi wayane da kuma layi a hade . Amma kuma filashing shine ka canza tsarin da waya ta zo da shi na amfani da  service zuwa amfani da wani wani service.

ABIN DA SAUKI?

Yi wa waya Flashing ba wai  abi bane da kawai zaka shiga nan take domin ka karanta mukala kawai kace za kayi, Kana bukatar a kalla ace kasan computer a dan mataki na tsakiya, misali kamar kasan yadda ake daura program ko kuma kasan yadda ake cireshi, kuma a kalla kasan yadda ake shiga a gano wane driver ne babu a jikin computer kuma zaka iya yin wasu abubuwa fiye da haka.

Saboda yiwa waya filashing yana da nasaba da misalai dana kawo, domin dai dole farko kayi amfani da program na musamman da ake yiwa waya Flashing sannan kuma ace kana da wayar da ake kira da USB. Nasan mai karatu zai iya cewa wadannan abu guda biyar kacal mutum zai yi amfani da su wajen yin Flashing, wannan haka yake akwai program masu matukar yawa a internet wanda zaka iya saukar dasu a na’urarka kuma su taimaka maka wajen yin Flashing din wayarka.

Sabo da haka duk wanda yake da ilmin computer, kuma yana da program na Flashing sannan kuma yana da USB Cable lallai zai iya yin Flashing na waya. Da farko, sai ka fara saukar da shi program din idan baka da shi a computer ka, ko kuma kayi amfani da program na YOUR CELLULAR daga http://www.yourcellular.net/need help.htm Idan ka rubuta wannan adreshin internet  zai kai ka zuwa ga shafin da zaka saukar da wannan program din da zai baka damar kayi Flashing na waya.

Da zarar File din ya sauko za a ganshi a zuge zai zo (zipped) sai a warware shi, idan kabi wannan tsari da zamu nuna maka tare da vedio da zamu saka nan gaba kdan zaka iya Flashing din waya cikin mintina ashirin (20).

Daga cikin abinda ya kamata da take tsaro CDMA wanda bayanin sa zai zo nan gaba.

ME ZAN BUKATA DOMIN INYI FLASHING DIN WAYATA?

1.      Software na Flashing (wanda zaka sauko da shi daga internet).

2.      USB cable wanda zaka hada wayarka da computer domin yin Flashing.

3.      Computer wacce take da a kalla OS Windows 2000 zuwa sama sannan ta zamanto tare da USB port a jikinta sannan kuma ya zama tana da a kalla 256 RAM, da kuma saurin 800Mhtz.

4.      Ya zama CDMA ce.

SHI NETWORK DIN ME YE AMFANIN SHI A FLASHING NA WAYA

Dangane da abubuwan da muka lissafa a baya na abubuwa guda hudu da ake bukatar ka mallaka kafin ka iya yin Flashing na waya sannan kuma dolene ya zamanto kana da account tare da daya daga cikin Alaro guda biyu wadanda a ke anfani da su a harkar sadarwar waya. Idan kuwa baka da su kana bukatar kayi rijista dasu don samun wannan dama. Wadannan manya manya alaro (carrier) da na fadi guda biyu cewar su suke bada network na waya, sune: Global System For Mobile Communication (GSM), sune kamar AT&T da T-mobile. Sannan Alaro na biyun shine CDMA ko kuma kace Code Division Multiple Access, misalinsu shine Quest da Metro da Sprint da kuma Verizon. wadannan sune tsari da ake da su na harkar sadarwa na Wayar-Tafi-Da-Gidanka, wanda wayar ka in ba GSM bace to dole ta zama CDMA wanda so da yawa ba mai iya banbancewa tsakanin su.

Sabo da haka wadannan sune hanyoyin fasaha da ake dasu guda biyar wadanda suke bayar da dama a samu network a wayoyin tafi da gidanka ko da yake a yanzu ana samun wayoyi masu karbar network  biyu a lokaci guda.

Wannan shine a takaice abinda ake nufi da Flashing na Wayar-Tafi-Da-Gidanka a ilmance. ta daga wani tsari na kamfani. Misali ace ka sayi wayar MTN wadda dole sai da layin MTN ko kuma bata ma zo da shi ba kawai tana karbar service dinta kai tsaye daga MTN, sai aka wayi gari kana son ka yi amfani da wannan wayar amma kuma ba tare da ka canza waya ba, shine sai ka bi wannan tsarin, wanda idan kaje ka saukar da program da ake Flashing din waya ko dai GSM ce ko CDMA ce to zaka samu cewar idan ka sauko da file din akwai bayani dalla-dalla da zai nuna maka hanyar da zaka bi ka canza wayar ka ta koma tana amfani da ko wane layin waya, ko kuma ko wane irin service wanda a najeriyance ake kiran shi da cracking wanda a ilimi na computer a ke kiran shi da  Flashing.

Zamu da kata a nan tukunna kafin fitowar mujallarmu ta gaba idan mai kowa da komai ya kai mu lokacin, zamuji yadda ake yin Flashing a Najeriya da kuma wasu ilmomi da suka shafi wayar tafi da gidan ka.