Categories
Duniyar Waya

Yadda ake gyara wayar hannu idan ta jike da ruwa.

Ka dauka  ruwa zaka yi anfa ni dashi sai wayar ta fada cikin ruwan, kayi maza maza ka dauko ta, a daidai lokacin da ka dauko ta ta riga ta jike sharkaf da ruwa. Mataki na farko da zaka dauka shina sai ka cire batir din ta sanan ka tabbatar ba ka kunnata ba domin idan ka kunnata a wannan lokacin lallai za ka yi damejinta.

Ita kowa matsala ta fadawar waya cikin ruwa wannan ku san ruwan dara ne wanda ke gama da duniya, kusan wannan matsalan ta na damun mutane da dama, sannan kuma kowa da irin mataki da ya ke dauka, kusan rabin mutane da wannan matsalan ta ke shafansu kokari suke yi su bi hanyan da za su bi su iya tsane ita wayar tasu. Saura kuma ta ke kawai ta ke mutuwa, saboda wasu ganganci da su ke yi bayan sun fito da ita wayar ta su a cikin ruwa. Saboda haka duk wanda wayar shi ta fada cikin ruwa ya yi hanzari ya stamo ta nan take ya cire murfin wayar ya kuma zare batir din ta, zai iya saka batidin a fili ko kuma wayar da batir din a fili yanda rana za ta gasa su. Sanan kuma ya da kyau a lokacin da ya bude wayar ya cire batir ya sake dubawa ya gani shin ruwan ya riga ya shiga har cikin injin wayar ko kuwa bai shiga? To idan har ka lura cewar ai ruwan ya shiga ciki zaka iya daukanta ka rike gefenta ta rika yarfeta kamar yadda ka ke yarfar da kaya idan an wanke su, za ka ci gaba da yin haka har sai ka tabbatar cewar wayar babu sauran ruwa a cikin ta sannan ka sake mayar da ita cikin rana, ka kuma kifa bayanta a kasa, wato fuskanta yana kallon kasa bayanta na kallon sama saboda kada rana ta bata screen din wayar.

To idan kuwa ka fuskanci cewa lallai wayar ta jike sharkaf to abu na biyu shine ka sakata a cikin danyar shinkafa? Shinkafa? Na san da yawa za su ji abun banbarakwai me ya kawo kuma shinkafa a maganar tsane waya? Wannan haka ya ke, lallai shinkafa za ta iya tsane maka dukkanin ruwan da wayar ka ta debo a cikinta.

Yadda zaka yi shine, za ka samu wani kwano mai girma wanda zai iya daukar wayar ka saka ta da batirin ta a gefe sai ka cika wannan kwanon da danyar shinkafar ka sami murfi ka rufeta ruf, sai ka barta har tsawon awowi shida, daga nan sai ka daukota ka mayar da batirinta, idan ka kunna ta zata tashi da yardar Allah. (Wannan an jarabta kuma yayi aiki)

Haka kuma mutum zai iya amfani da abin hura gashi wanda mata ke amfani da shi idan suka jika gashin kansu (Dryer) domin ya bushe. Amma shima idan za ayi anfani dashi dole a lura da wani irin dryer za ayi amfani da shi, domin a lokacin da ka fuskanci cewar lallai wayar ka ta jike sosai har kana ganin cewa idan kayi anfani da danyar shinkafa ba zai yi tsane ruwan ciki ba,  ka ga a nan kana bukatar amfani da dryer. Da farko dai zaka cire batirin wayar sannan ka rike wayar ha hannun ka sosai sannan ka fara yarfed da ita kamar yadda ake yarfar da kaya da suka jike, bayan ka gama yarfarwa ka tabbatar da babu sauran ruwa a jikin ta sai ka ciro ko kuma ka je shagon da ake yiwa mata gyaran gashi su baka karamin dryer sannan kuma ka yi amfani da mai sanyi ba mai zafi ba, domin idan ka yi amfani da mai zafi to zaka karawa wayar ka wata matsala ta daban, haka zaka ci gaba da busa mata iskar har sai ka tabbatar da wayar ta bushe sosai, sannan ka mayar da batirin sannan ka saka ta a caji baya wani tsawon lokaci sai ka kunnata .

Shi ya sa yana da matukar kyau idan ka na da waya kuma ta na da tsada ko kuma halin gyara to yana da kyau ka rika saka mata irin rigunan ruwa da kuma abubuwan da zasu hanat lalacewa.

Wannan shine a takaice hanyoyin da zamu iya bi domin muga mun dawo da hayyacin wayarmu a lokacin da ta fada a cikin ruwa. A karshe nake cewar ayi hattara!