Categories
Hannunka mai sanda

Ga Amsoshin Jarabawar JAMB 2016

Yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya ni in bayar da waɗannan amsoshi ba domin komai ba sai domin in taimakawa al’ummata don ta sami nasarar lashe wannan jarabawa ta JAMB wacce ake son fara ta nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, amma dai ina bukatar Naira Dubu Daya kacal a wurinku. Wannan shi ne abin da naji wani mutum yana faɗawa waɗansu yara waɗanda suke son su rubuta jarabawar JAMB  wacce ake amfani da kwamfuta wurin rututa ta wato (Computer Based Test).

Wannan zance hankalina bai kawo gare shi ba, sai bayan da na ke samun saƙwanni ta hanyoyi mabanbanta ana roƙo na ni ma idan har ina da wata hanya da zan taimaka to in taimaki al’umma tunda wani yanzu haka yana ƙoƙarin rubuta jarabawar ta wurin Huɗu ko Biyar, amma kuma bai sami sakamakon da yake buƙata ba.

To, gaskiya jama’a ina son mu sani cewar garɓatattun mutane za su iya sato takardun jarabawa a ofishi JAMB ko kuma a hada baki da ma’aikatan da suke ajiyar waɗannan takardu su kwaso su rabawa mutane da kudi mai tsada.

Waɗannan mutane da muke gani, suna daga cikin mutanen da suka sanya darajar ilimi da kuma mayar da hankali domin fahimtar karatu ta yi karanci a wurin mu, musamman ‘yan Arewa kasancear tun Fil-Azal ɗan Arewa bai san wani abu satan amsa ba, ba mu da wannan dabi’a ba mu santa ba, sai bayan da muka fara samun makarantu masu zaman kansu waɗanda ake musu laƙabi da Miracle Center wato makarantu waɗanda idan ka rubuta jarabawa a cikinsu, to tabbas za ka sami sakamako mai kyau.

Wannan ya kawo tawaya a wurin dalibai da suke yin karatu a kowane ɓangare da ke cikin wannan yanki na mu na Arewa. Dalilin haka ya sanya tun daga Sakandare za ka samu yara suna faɗa maka cewar ai duk karatunka sai ka nemi satan amsa ko kuma malamai sai sun taimaka maka kafin ka sami fitowa da sakamako na gari. Haka idan dalibi yana karatu a Jami’a ko a wata babbar kwaleji za ka samu ɗalibai sun fi amanna da cewar duk wanda ya ke matsawa a yi karatu kuma a gane, shi ne mugun malami, wanda kuma zai cewa duk wanda ya sayi littafinsa ko ya ganshi da ‘yan tamame to shi ne zai samu maki mai yawa. Waɗansu malamai ma za su faɗa muku cewar za su baiwa dalibai kaza Carry Over, dai dai irin malamai da suke saka dalibai su ga cewar mayar da hankali wurin yin karatu ba shi da wani muhimmanci, iya kuɗinka iya shagalinka.

To a  wurin rubuta jarabawa ta hanyar kwamfuta waato (CBT) kada wani ya yaudareku, domin an fito da irin wannan tsarin ne domin ganin an kaucewa duk wata hanya da dalibai za su bi domin satan amsa. Da kuma ganin dalibai sun mayar da hankali sosai domin fahimtar karatu mai inganci.

SHI ANA IYA BAKA AMSAR JARABAWA TA KWAMFUTA?

A gaskiya kamar yadda na ambata a farko cewar wannan abu ba zai yiwuba, haka abin yake, domin yadda aka tsara kwamfuta ta riƙa fito da tambayoyi da amsoshi ba kamar yadda ake amfani da takardu ba ne wurin shirya jarabawa.

Duk mutumin da ya san yadda ake amfani da kwamfuta ake yin walan-keluwa da rubutu ya san cewar a rina wai an yi yamma da Kare. Domin idan aka ce an sami dalibai dubu ɗaya sun biya kuɗi domin rubuta jarabawa to ita hukumar dake lura da wannan jarabawar zata bi duk wata hanya domin ganin an kiyaye waɗannan jarabawar ba tare da an sami bayyanar amsar ba kafin ranar, shi yasa wani lokaci sai ka samu hukuma ta shirya jarawaba mabanbanta domin magance irin wannan matsalar.

Amma a kwamfuta yadda aka shirya jarawabar ya canza daga yadda mutane suka sani, domin idan mutum dubu za su rubuta jarabawa a cikin darussa hudu, misali Ingilishi da Lissafa da Tsimi da Tanadi da Hausa, shi Ingilishi za a bashi tambayoyi guda ɗari, sauran kuma a basu tambayoyi guda hamsin waɗanda yake nuna kowane mai rubuta jarabawar zai amsa tambayoyi guda dari biyu da hamsin.

To idan aka tashi shigar da tambayoyin za a shigarwa da Ingilishi kamar tambayoyi ɗari biyar ko fiye da  haka, haka suma sauran darussan za a shigar musu da tambayoyin wanda zai kasance za a iya samun tambayoyi kamar dubu ko fiye da haka ga kowane dalibi zai amsa.

Wani zai iya faɗin cewake nan duk wanda shi ne ya shigar da tambayoyin a cikin kwamfutar, misali ma’aikatan hukumar, ke nan yasan amsoshin tambayoyin da za su fito, saboda haka idan na sanshi zai iya ba da amsar tambayoyin da ake bukatar su. Wannan ba haka yake ba, domin dalilin sanya waɗanda nan tambayoyi masu yawa, domin ita wannan jaraba da ake amfani da kwamfuta wurin rubuta ta, ita kwamfutar ce take zaɓar tambayar da za ta fito a daidai lokacin da kake ƙoƙarin rubuta jarabawar.

Misali da za a samu a cikin ɗakin jarabawa a sami mutane ɗari da zasu rubuta jarawa ta hanyar kwamfuta, to duk su ɗarin nan babu wanda tambayar shi za ta yi daidai da ta ɗan uwansa, zai kasance idan dukkan su a lokacin za su rubuta jarabawar Lissafi ne, za ka samu tambayoyin duk an jirkita su, wanda ya ke kan kwamfuta ta farko wataƙila tambaya ta ɗari uku ce a matsayin ta farko a ta shi kwamfutar, wanda kuma ya ke kwamfuta ta sittin wataƙila tambaya ta ɗaya ce a tashi kwamfuta.

Kuma wani abin mamaki da wannan jarabawa ta kwamfuta ita ke sanya lambobi a jikin kowace tambaya, a lokacin da ka ga tambaya ta ɗaya a cikin kwamfutarka haka shima an rubuta tambaya ɗaya ne a cikin kwamfutar sauran, sai dai dukkanku tambayoyinku sun banbanta.

Kuma wani abin mamaki shi ne, ita kwamfutar tana sauya mazaunin amsoshin kowace tambaya. Misali idan wanda ya tsara jarabawar ya zaɓi amsar tambaya ta farko shi ne harafin (A) to ita kwamfutar za ta iya canzawa zuwa (C) ko kuma sabanin haka, amma kuma amsar daidai ne. Saboda haka, koda an yi sa a an samu a cikin dakin jarabawa, tambaya ta goma ta yi daidai da kwamfutoci biyar to yadda abin zai kasance shi ne, zai iya yuwuwa a kwamfuta ta farko amsar ta kasance (A) na biyu (D) na uku (B) na hudu (E) na biyar (C), wanda idan muka lura babu yadda za ayi wani ya iya baka amsa.

MENE NE ABIN YI?

Gaskiya abin yi shi ne mu ƙara yin karatu, sosai da sosai, mu sani cewar wannan ɗabi’ar ta ƙoƙarin cin jarabawa ta hanyar satan amsa ita ce hanya mafi sharri da lalacewar al’ummar mu, idan muka saurari yadda iyayenmu da kakanninmu suke yin turanci, irin su Sardaunan Sokoto, Tafawa Balewa, Maitama Sule, Farfesa Ango Abdullahi da dai makamantansu za mu tabbatar cewar ba satan amsa suka yi ba. Mu duba tarihi irin sakamakon da iyayenmu suke fita da shi da kuma irin yadda suka mayar da karatu ya zama dabi’unsu shi yasa suka zama fice a cikin abin da suke nema.

Wannan shi ne satan amsa da zan bamu na wannan jaraba ta JAMB, da cewar Allah Ya bada sa a kuma ina kira ga ɗalibai ‘yan uwana da su mayar da hankali lokacin da suke yin karatu da kuma sanya kwazo a cikin darrusanmu.

ABUBUWAN KIYAYEWA LOKACIN RUBUTA JARABAWAR

 • Abu na farko shi ne ka rubuta Jamb Registration Number dinka.
 • Duk abin da ka gani sabanin abin da yake naka ne, ko ka yi kuskure kada ka fara bada amsa, sai ka nemi agaji daga wakilan JAMB na wannan center din.
 • Ka sani cewar ana bayar da awanni uku ne domin amsa dukkan jarabawar. Ba kamar yadda wadansu ke tsammanin cewar kowane darasi ana bashi awa uku bane.
 • Darasin Use of English yana da tambayoyi ɗari, sauran darussan uku suna da tambayoyi hamsin – hamsin.
 • Ba a son ka bata minti daya wurin amsa kowane tambya domin yin haka zai sa ka manta kasa amsa tambayoyin saba’in
 • Ana amfani da browser wurin amsa wannan tambayoyin wanda yake nuna ba zaka iya amfani da maballin Next ko Back ko Referesh ba.
 • Ba dole sai ka fara amsa tambayoyin darasin farko ba, zaka ita shiga darasin da ka fi ganin ka fi saninsu kafin ka shiga masu wahala.
 • Duk tambayar da baka santa ba, kada ka yi shaci-faɗi wurin bayar da amsarta, za ka iya wuce ta gabanta, bayan ka gama amsa dukkan tambayin sai ka dawo baya wurin wadanda baka amsa su ba ka sake dubawa idan akwai sauran lokaci.
 • Duk tambayar da ka amsa ta zata saka maka alamar ruwan Ganye, wacce kuma ka tsallake ta zata nuna maka alamar ruwan lemu.
 • Bayan ka kammala komai sai ka taba maballin finish wanda ya ke nuna cewer lallai ka kammala wannan jarabawa.
 • Kada a manta da yin addu’a domin neman taimako daga Mahallici, a kuma dage da nazari.

Allah Ya basa nasara, amin.