Categories
Communication

Li-Fi: Kwan Lantarki Mai Saukar da Gig 224 a Dakika Guda

A wani sabon gaji da aka gabatar a garin Tallin an samu nasarar aikawa da sakon data mai nauyin Gibabait 1 a cikin dakika guda. Wannan wata sabuwar hanya ce da ake ganin zata kawo gagarumin nasara a fagen aikawa da sakwonni masu nauyi da girma nan ba da jimawa ba ta hanyar amfani da tsarin Wireless.

Wi-Fi wacce ita ce hanyar da ake amfani da ita a wannan lokaci wacce ake ganin tana da matukar sauri wurin aikawa da sakon data, a sabuwar hanya da ake da ita wacce take tafiya ta 5GHz ana iya aikawa da data mai nauyi Megabait 600 a cikin dakika guda. Wannan sabon tsari na Li-Fi ana sa ran zai iya aikawa da data wacce takai nauyi Gigabait 224 a cikin dakika guda.

Yanayin yadda ake sa ran aiki da haske wurin aikawa da data ta fasahar Li-Fi
Yanayin yadda ake sa ran aiki da haske wurin aikawa da data ta fasahar Li-Fi

Li-Fi wanda za ka iya kira cewar kwan lantarki ne irin wanda muke amfani da shi a gidajenmu, ko kuma irin wanda ake samun kananan kwai na Tocilar zamani mai kananan fararan kwayaye sai dai shi an dan kara mishi wani sinadari da kuma saka mishi wayoyi wadanda za ayi amfani da su wurin aikawa da data. Haka shi wannan Li-Fi yana bukatar wata na’ura ta musamman wacce zata rika fassara sakon da wannan kwan zai rika aikowa kasancewar shi wannan kwai zai rika yin amfani da tsarin Binary ne kai tsaye shi kuma wannan na’urar ta na fassara shi zuwa data da mutum zai yi amfani da shi wurin bude intanet.

light-emitting diode
Irin wadannan kwayaye su aka fi kira da LED light-emitting diode da shi ake amfani wurin fasahar Li-Fi.

Idan hakan ta tabbata ana sa ran mutum zai iya sauke DVD namu na gida mai nauyi Gigabait 4.7 daga intanet ta hanyar wireless har guda 29 a cikin dakika guda.

Wannan ba karamin nasara ba ce idan aka yi la’akari da hasashe da ake da shi idan shekarar 2019 ta zo ana sa ran a kowane wata za a rika yin amfani da kimanin Gigabait Billion 37 na data, wanda hakan yana nuna bukatar wannan fasahar kasancewar Wi-Fi ba zai iya bayar da wannan ba.

Wi-Fi wanda ya ke amfani da tsarin aikawa da sako ta hanyar Radio Frequency yana da iyaka da kuma wadansu matsaloli wanda ya dangance shi, da wannan dalili ne ya sanya ake tunanin cewar a watan wata rana za a wayi gari ba za a iya amfani da Wi-Fi ba.

Matsalar Wi-Fi ba a nan ta tsaya ba, domin idan mutum na tunanin aikawa da sako ta hanyar Wi-Fi ita wannan hanyar tana samun wahalar hanyar da za ta bi domin ta kai sakon da ake turawa. Wannan ba ana magana da irin sakon da mutum zai amfani da wayarsa ko kwamfuta da kwamfuta ya aika ba. A nan ana maganar aikawa da sako na Wireless da ake amfani da shi domin samarwa da mutane Intanet a wurare mai fadi.

Shi wannan sako da ake amfani da wireless a aika shi, yana fama da matsalolin na bango ko kofofi da suke iya kare mishi hanya da zai yi amfani da ita wurin kaiwa zuwa ga na’urar da aka aike shi. Idan kuwa aka zo ga maganar aikawa ba baban data to Wi-Fi sai a hankali.

Li-Fi wanda ake kiranshi da Light Fidelity shi kuwa yana bangaren fasahar Electromagnetic Spectrum wanda ake amfani da Radio Waves, sai dai shi Li-Fi yana amfani da fasahar tafiyan haske ne fiye da radio wave sau 10,000.

Yadda fasahar Electromagnetic Spectrum ta ke yin aiki wurin aikawa da sako
Yadda fasahar Electromagnetic Spectrum ta ke yin aiki wurin aikawa da sako

Wannan ya ke nuna cewar Li-Fi yana iya amfani da hanya mara iyaka wurin aikawa da sakwanni. Maimakon ace zai yi amfani da hanya guda kamar Wi-Fi wurin aikawa da sako, wannan fasahar tana amfani da siririyar hanya wacce ta fi na Wi-Fi sirantaka, sannan kuma za ta kuma raba kanta har sama da gida dubunnai domin isar da wannan sako.

Haka ita wannan fasahar ta Li-Fi za ta yi amfani da tsari ne na LED Light wato kwan lantarki da muke amfani da shi domin haskaka dakunan mu. Domin kwan lantarki idan ka kunnashi kana ganin haske ne, amma a zahiri wutar bata tsayawa, tana kashe kanta ta kunna kanta cikin sauri ta yadda ido baya iya ganin mutuwar wannan wutar.

Wannan fasahar dai ta fara bayyana ne ta hannun wani Farfesa dan asalin Kasar Jamus mai suna Harald Haas, Malami a Jami’ar Edinburgh da ke kasar Amura wanda ya bayyana yadda ita wannan sabuwar fasahar za ta rika yin aiki. Tun a cikin shekara 2011 ya gabatar da gwaji na farko a wani babban taro da ake yi domin nuna bunkasar fasaha a kowane bangare a duniya TED.

Herald Haas wanda ake ganin shi ne mutumin da ya kirkiro da wannan fasaha ta Li-Fi
Herald Haas wanda ake ganin shi ne mutumin da ya kirkiro da wannan fasaha ta Li-Fi

Haas ya ce abin da ake bukata dan kadan ne domin ganin samun saukin aikawa da data. Domin ya ce ya lura da amfani da Radio Mars da sama da miliyan 10 da ake da su a kasar Amurka da kuma amfani da kamanan wayoyin hannu fiye da biliyan 8. Sannna kuma yaga yadda kodawane lokaci bunkasar fasaha da kimiyar kera-kere kullum kara gaba ta ke yi, ya sanya ya yi tunanin yadda zai mayar da hasken wutar lantarki zuwa wata hanya da za ayi amfani da ita wurin aikawa da sakon data.

Ya ce mutane suna bukatar wannan dan kwai wanda za a iya kara sinadarinsa a cikin kwan lantarki da muke amfani da shi yau da kullum sannan kai kuma ka sani yar karamar na’ura wacce take iya fahimtar sakon da wannan haske ya ke aikawa domin kai kuma ka yi amfani da shi a matsayin data na shiga intanet.

Yanzu dai haka tuni an fara kera su irin wadannan kwayaye domin ci gaba da gwajin da ake yi na ganin tabbatuwar wannan fasaha. Sai dai Farfesa Haas ya ce wannan fasahar ko kadan ba tana neman kashewa Wi-Fi ka suwa ba ne. In da masana suke ganin idan har wannan fasahar ta tabbata to babu wani abu da za ayi da Wi-Fi.

Categories
Duniyar Internet YouTube

Yadda ake saukar da video daga YouTube (1)

Wannan darasin sabo da tsawon shi mun raba shi gida biyu

Matashiya

Kafin mu yi bayanin hanyoyi da ake bi domin a saukar da bidiyo daga dandalin zumunta na YouTube, ya na da kyau mu fahimci wadansu ka’idoji da dokokin saukar da abu daga shi wannan zaure na YouTube.

Su dai wannan kamfani na YouTube mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, a hanlin da muke ciki a yanzu babu wani daki ko shafi a duniyan nan da ya ajiye hotuna masu motsi kamar YouTube, haka kuma shi ne shafi wanda aka fi ziyarta domin kallon hotuna masu mosti, kuma shi ne shafi na uku a ziyarta a duk shafukan da suke intanet.

Domin an ƙiyasta sama da mutane biliyan daya (1 billion) suke amfani da wannan shafi na YouTube haka kuma a shekarar 2014 kamfanin ya sami ribar kudi zunzurutun dalar Amurka biliyon 4 (4 Billion USD), haka kuma kamar yadda kamfanin dubawa da yin hasashe na DMR (Digital Marketing Statistics) su ka fadi cewar a kullum ana kallon bidiyo biliyan 4 a kowace rana.

A wuraren Satumbar 2011, kamfanin yayi wani alkawari da har yau bai cika ba, na cewar za su saki wata manhaja wacce zata ba mutane masu amfani da wayar komai da ruwanka damar kallon bidiyo a YouTube ba tare da amfani da fasahar intanet ba, matuƙar ka bude shi bidiyon kafin ka kashe intanet din. Wannan yunƙuri na su, har yanzu bai tabbata ba.

Amma kuma idan ka dubi mafi yawancin bidiyon da yake cikin kwamfutocin mutane da wayoyinsu za ka samu cewar ana samun su ne daga YouTube. To, haka abin yake, domin kusan kafin a fara samun makarantu masu zaman kansu a intanet, mutane da dama suna daura karatukansu a shafin YouTube domin jama’a su kalle su. Shi yasa YouTube ya zama wani dausayin alheri da kuma tsibiri na sharri. Domin kusan dukkanin wani ilimi da mutum yake son ya koya zai yi wahala a shiga cikin shafin YouTube bai same shi ba. Wani lokaci ma shi wannan shafin manyan gidajen jaridu da gidajen yada labarai na talabijin suna amfani da shi wurin daura shirye-shirye domin jama’a su yi amfani da shi ko kuma su sake kallonsa.

Shi yasa kowane irin bidiyo ake samun shi a YouTube, kama tun daga na karatu, wasanni, nishadi, fadakarwa da dai makamantansu, kuma dukkaninsu ana samun masu tsawo da matsakaita. A wani lokaci zaka samu mutum daya ya daura bidiyo sama da dubu biyu a shafinsa, kuma ka samu yana da mabiya ko masu kallo sama da miliyoyin adadi.

Takaitaccen tarihin kafa YouTube

YouTube na daya daga cikin shafu a Intanet irin wadanda ake kiran su da video-sharing website, wato shafukan da ake saka bidiyo domin wadansu su kalla, ya na da Hedkwata a San Bruno da Jihar California ta kasar Amurka. Wadansu matasa su uku Steve Chen, Chad Hurley da kuma Jawed Karim su ne suka kiriro shafin a 14 ga watan Fabrairu 2005 bayan da suka bar aiki a wani kamfanin hada-hadar kudi a intanet mai suna PayPal. Tun daga shekarar 2005 zuwa 2006 su ne suke da alhakin mallakar komai a shafin YouTube har zuwa lokacin da kamfanin Google ya ga muhimmancin wannan shafi da yadda ya sami karbuwa a wurin mutane, ya siye shi da kudi wuri na gugar wuri har dalar Amurka Bilyan 1 da Miliyan 650 ($1.65 billion) a watan Satumba 2006.

 Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim
Daga dama: Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim

Shafin wanda yake ba mutane damar su daura bidiyo domin mutane su kalla ko domin su yada shi a shafukan intanet ko kuma lika shi a shafukan zumunta. Ana amfani da zarin abin kallo na kwamfuta da wayoyin domin iya kallon su, kamar tsarin WebM da H.264 da MPEG-4 da AVC da kuma Adobe Flash Player.

Ana samu bidiyo daban-daban kamar na wasanni, shirye-shiryen gidajen yada labarai, bidiyon wakoki, fina-finai, karatuka, bidiyo domin ilmantar da dai makamantansu.

Mafi yawancin bidiyon da suke YouTube gama garin mutane ne suka daura shi, amma kuma ana samun gidanjen yada labarai manya sanannu suna amfani da shi, kamar irin su CBS, BBC da VOA da dai makamantansu.

Wanda bai yi rigista da YouTube ba zai iya kallo ne kawai, amma wanda yayi rijista zai iya kallo, zai iya daura shima na shi bidiyon domin wadansu su kalla, zai iya kulla alaka da wani mai daki a YouTube duk lokacin da ya daura wani sabon bidiyo a sanar da shi kai tsaye (Subcribe), sannan zai iya yin tsokaci (comment) ga bidiyon da aka bayar da damar yin tsokaci a kai.

Dukkan bidiyon da yake YouTube babu matsala wurin kallonsa matukar bai dauki hotuna na tsaraici ko na wanda yake dauke da hotuna masu hatsari, kamar kisa ko kuma abin da bai kamata masu karamin kwakwalsu kalla ba. To irin wadannan bidiyo dole sai ka fadawa YouTube cewar kai ka wuce shekaru 18 kafin ka ga irin wadannan bidiyoyin.

Shafin na YouTube yana samun kudaden shigar shi ta hanyar saka talla da yake yi a kan bidiyo da mutane su kallo, kuma sun ba masu bidiyon damar mallakar kashi 55% na kudin da ake biyansu. Misali a shekarar 2013 kamfanonin da suke ba YouTube talla su na biyan su dalar Amurka $6.60, idan aka kalli bidiyo ko kuma tallansu har sau 1000, wanda yake nuna cewar duk wanda ya amince da YouTube su saka talla a kan bidiyon da ya daura a shafinsu zai iya samun 0.5x$7.60×55%=N2.09 wannan tsarin an yi amfani da shi a shekarar 2013.

Shafin na YouTube yana iya kokarin ya ga ya hana mutane daura bidiyon da baka da hakkin mallaka, wato irin na satan safage wanda kusan da yawa daga cikin bidiyoyin da suke YouTube wadanda suka daura shi ba su suke da hakkin mallakar shi ba.

Shin daidai ne mutum ya saukar da Video a YouTube?

Babu laifi idan mutum ya saukar da bidiyo daga YouTube domin yayi amfani don karan-kansa ba tare da juyashi ba ko kuma ya canza shi zuwa wata hanya. Amma laifi shi mutum ya saukar da kowane irin bidiyo a YouTube sannan ya yi amfani da shi a wani gidan talabijin ko kuma ya gurza shi ko kuma domin sayarwa.

Kamar yadda kamfanin na google ya fadi a shafin shi na sharadin amfani da bidiyon YouTube sun rubuta kamar haka, “Ba a yarda kayi amfani da Video nan ba sai domin amfanin kanka, ba na neman kudi bane, ba za a diba ba (copy), ba sake gurzashi, ba rabashi, ba nuna shi a gidajen talabijin, ba yin kasuwanci da shi, kada ayi amfani da wani bangare nashi sai da izini rubutacce zuwa ga YouTube”. Daga jin irin wannan sharadi yake nuna mana cewar idan mutum zai saukar da bidiyo daga YouTube kuma yana son yayi amfani domin nishadantar da kansa ko kuma ilmantan da kansa, to babu laifi.

Haka idan muka dubi zuwa ga amfani da shi ta wadansu kafafe, sai muga hatta yadda mutanen mu suke saukar da bidiyo daga wannan gida kuma suyi ta gurzashi, wannan kai tsaye laifi ne. Shi ya sanya daga cikin dokokin amfani da shi, sun fadi cewar idan mutum ba zai yi amfani da intanet ba ne, ya kalla kai tsaye, to shima ba su yarda ya saukar da shi ba domin kallo.

Saukar da bidiyo daga YouTube yana kawo wa wannan kamfani cikas ga harkokin kasuwancin su. Mutane da dama su na yawan tambayar mu shin, irin waɗannan shafuka kamar google, ko facebook, ko YouTube mene ne ribarsu? Sai mu fada musu cewar shigar da muke yi suna amfani da shafukan su, shi ne ribar su, domin manyan kamfanoni na duniya suna yin la’akari da yawan mutanen da suke shiga dakuna a intanet, kuma wannan dalilin yake sanyawa a basu talla.

Mene ne dalilin da yasa ba maballin saukar da bidiyo kai tsaye a shafin YouTube?

Kamar yadda muka fadi cewar a shekarar 2014 kamfanin google ya sami ribar dalar Amurka biliyan 4 wanda yake daidai da Naira Biliyan Dari Tara (900,000,000,000) ta su bidiyoyin da ake kallo a shafin YouTube. Wannan ribar ta samu ne saboda talla da yake bayyana a jikin bidiyo lokacin da mutum yake kallo.

Wannan shi ne ma dalilin da ya sanya wani lokaci idan mutum yana son kallo a YouTube sai ya jira na ‘yan dakikoki biya domin kallon talla kafin ya baka zaɓin ko ka ci gaba da kallo ko kuma ka wuce zuwa ga shi bidiyon da ka nemi ka kalle shi. Matsalar nan ita ce, idan mutane suka sauke shi bidiyon kun ga babu yadda za ayi kamfanin su sami kudi, dalilin haka ya sanya su kamfanin basa so mutum ya ce zai saukar da shi.

Ko ba mu yi dogon bayani ba, kasan cewar da dukkanin bidiyoyin da suke cikin wayoyinmu za a barsu a shafukan da suke sai dai kawai mukalla a sama da kudaden da za su samu sai ya ninka wanda suka samu a shekarar 2014. Amma dai duk da haka mutane da yawa suna ta ƙoƙarin su ga yadda za ayi su saukar da wadannan bidiyoyi a kwamfutocinsu da wayoyin domin su iya amfana da su a wani lokaci.

Mene ne ya sa bidiyo yake da cin MB?

Dalili kuwa shi ne domin bidiyo hotuna ne aka tara su a wuri guda. Yadda abin ya ke shi ne, duk wani bidiyo da mutum ya gani tun daga dakika daya zuwa awanni daga hoto daya ne zuwa hotuna 25 zuwa hotuna 60. Idan ka duba na’urar daukan hoto misali Camera ta wayarka, zaka ga daga bayan an rubuta lamba a gaban lambar an rubata Pixel, misali 2 Mega Pixel. Wannan megapixel sinadari ne da ake auna kyau da girman da Kamara zata iya daukar hoto da shi.

Idan aka ce kamarar wayar ka ta na da 5-megapixel to ana son ka sani cewar wayar ka zata iya daukan hoto guda wanda sai an sami digo miliyan biyar a jikinshi. Shi daman Pixel a ilimin daukan hoto na nufin digo duga ko kuma rami guda da kala zai iya zama na hoto a cikinsa. Saboda haka, idan aka ce wayar mutum ko kuma kamarar shi tana daukar hoto mara motsi guda daya wanda ya kai nauyin 2Mb, to idan zata dauki bidiyon dakika guda sai ka hada 2mb x 25 = 120mb.

A takaice duk mafi yawan bidiyon da muke kallo suna da zubu iri biyu ne, PAL da NTSC, bidiyon da aka daukeshi da fasahar PAL a kwane dakika ana samun hotuna 25 ne, wanda kuma aka yi amfani da fasahar NTSC ana samun hotuna 29 zuwa 30 a kowane dakika guda. Ba a maganar cewar lokacin da kamarar take daukan hotunan tana kuna hadawa tare da sauti wanda shima yana da nasa nauyi.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya bidiyo ya ke nauyi kasancewar tarin hotuna ne da sauti a hade a wuri guda.

KARANTA DARASI NA GABA