Categories
Duniyar Waya

REMINDER APPLICATAION! Amfaninsa yafi a wurin Musulmi

A cikin wayar hannu da computer akwai wani abu mai amfani ga mutane mai suna Reminder musammama Musulmi wajen tabbatar dakai a cikin sahun da addini yake bukata. Da kuma fitar dakai daga abinda Allah da Manzonsa suka suffanta a matsayin munafurci. Malam bature ya kirkiri reminder ne dan tunatar da ‘yan uwansa wasu abubuwa na rayuwa, amma kuma amfanin reminder ga Musulmi yafi masa amfani.

Duba da yadda Allah ya fada da kansa cewa “KU CIKA ALKAWARI. DOMIN LALLE SHI ALKAWARI ABIN TAMBAYAWANE” (Isra’ 17:34).

Cikin hikimar Allah, ya kawo mana wannan abu mai amfani dan tabbatar da alkawari da sauran Uzirori na rayuwa.

 

AMFANIN REMINDER A WAYA

  • Yana taimakawa wajen cika alkawari tsakanin al’umma.
  • Yana tabbatar da kamalar mutum ta cika alkwari.
  • Yana hada kan al’umma ta wajen halattar taro.
  • Yana tunatar da mutum kana nun aiyuka ds.

 

SIFFOFIN REMINDER

  • Yana dauke da kwanan wata,
  • Yana dauke da watanni goma sha biyu, da kwanakin cikin mako,
  • Yana dauke da lokaci da kalanda dan tabbatar da lokaci
  • Yana dauke da setin kararrawa wato (alarm)
  • Yana dauke da wurin rubuta abinda yake ranka na daga abinda zaka yi.

 

YADDA AKE SETA REMINDER

Ana seta reminder ta hanyar zaban rana da lokaci da wata da kuma suna abinda zaka yi ko zaka je a wannan lokacin. Wanda da zarar lokacinsa yayi na bugawa da kansa zai aiwatar da abinda aka umarceshi, yayi.  Yana dauke da alarm da sunan abinda zaka aiwatar akan waya ko computer. Yana tuni kafin lokacinsa ya cika ta hanyar alarm.