Categories
Software

SHIN KANA SO KA ZAMA ANIMATOR?

A mujallar da ta gabata na yi bayani a game da mene ne animation da kuma karkasuwarsa, a yau kuma da izinin Allah za mu yi bayani ne a kan ya ya za ka fara yin animation da kanka ka zamo animator kuma da irin fa’idojin da animation kan gabatar ga animator.

Wanne ne Animator?

Animator dai shi ne wanda yake da ilimin yadda ake yin animation kuma yana yin sa don nishaɗi ko don samun kuɗi ko kuma don duka biyun, kuma a wani lokacin ma, animators ba cartoon kaɗai suke yi ba har da wasu siddabarun cikin fina-finai (visual effects) kamar su tashi sama, mutum ya bace, tashin bom da dai sauransu, kuma suna haɗa Kwamfuta ‘games’ (wasanin Kwamfuta) da video game (da wasani da ake haɗawa da talabijin).

Shin waɗanne irin fa’ida animators kan samu a yin animation?

          Gaskiya haƙiƙa animators kan samu fa’idoji da yawa ta hanyar aikinsu na animation, domin animator kan iya yin aiki a kamfunan shirya fina-finai (film industry) tallace-tallacen talabijin, shafukan intanet da dai sauransu wanda zai yauƙaƙa hanyar cin abincinsa. Kuma har wa yau zai iya haɗuwa da wasu animators, su haɗa shirin fim wanda tun daga farkonsa zuwa ƙarshensa hotuna ne masu motsi zalla (animated movie) wanda shi ma zai iya kawo musu kuɗaɗen shiga, bayan fa’idar kuɗi, animation zai iya sa animator ya zama tauraro (celebrity) ko ina a duniya a san da shi, misali kamar yadda aka san su Jeff Lew, Walt Disney, William Hanna da Joseph Barbera, Len Lye, Norman McLaren, Matt Groening, Hank Azaria da dai sauransu suka shahara a fagen animation ko ina an san da su.

To tun da haka ne ya ya za a yi in zama animator?

A gaskiya dai, akasari idan ka tambayi animators musamman ma na kasarmu Nijeriya  ya ya za a yi kai ma ka zamo animator? Za su fara baka amsa da cewa ai ka zo gidan sauƙi. Bayan haka sai su danƙara maka wasu faya-fayen CD da takardun karatu na Kwamfuta (PDF) na wani animation software ka koya, alhali ba su sanar da kai wasu ƙa’idoji da hukunce-hukuncen da suke cikin animation ba ko kuma ba kayan da su sanar da kai cikin sauƙi.

Ni a nan shawara ta ga mai karatu idan kana so ka zamo animator sai ka yi la’akari da waɗannan abubuwan:

  • Sa kai
  • Karatu/Neman ilimi
  • Kwarewa

Da izinin Allah za a ga bayanan waɗannan a mujalla ta gaba.

Categories
Software

ANIMATION YADDA AKE MOTSA HOTUNA A COMPUTER

Rubutawa: Tukur Kwaironga

Mene ne Animation?

Animation dai hotunane daukakku, tsararru, ko zanannu  masu motsi. Wandanda motsin da suke yi ya samo asali ne ta hanyar jera su da aka yi daki daki.  Bayyanarsu hotunan da kuma motsin da ake gani yana faruwa ne a sabili da saurin da ake ginin wucewar hotunan ne, wanda yake  kayyadajje ta hanyar amfani da computer ko akasin haka.                               

Karkasuwar  Animtion

Animation ya kasu kashi daban-daban, wadanda aka dunkule su aka kuma raba su zuwa gida uku kamar haka :

1.            Traditional Animation

2.            Stop motion Animation

3.            Computer Animation

Traditional Animation

Traditional animation , animation ne wanda ake yin shi ba tare da amfani da computer ba, shi ne irin animation na farko da aka fara a duniya.

Traditional animation ana yin shi ne ta hanyar zana hotunan (frames) da ake son motsa su da hannu ba tare da wata na’ura ba, sannan sai a kwafe su ko kuma a yi tracing(sake bin zanen da abin zanen)din su a kan wata fallen roba mara kauri mara launi(wato transparent) mai sunaCels sannan a  daura su a zanannen hoton bango(background image) mai launi, bayan haka sai a dauko wani irin abin daukar hoto mai suna Rostrum Camera  a dauki zanannun hotunnan a rika jera su a kan hoton bangonsu mai launi(background image) daya bayan daya. To bayan an wanke hotunan daga abin daukar hoton, sai a jera su a kan  majigi (projector) a bayyanar da su da sauri, to a nan ne hotunan za su zama masu motsi (Animated movie),  fina-finan zane masu motsin (Animated movies) da aka yi amfani da irin wannan tsari su ne;  The Lion King, Spirited Away, Les Triplettes de Belleville, Snow White da dai sauransu

A karkashin Traditional Animation za a iya karkasashi shi ma kamar haka:

Full Animation:

A irin wannan salon, ana yin zanen da kuma sa shi motsin ya yi kamanni da dabi’un na dan Adam na  gaskiya,  yawancin Animations din Disney (kamfanin animations ne) suna  amfani da irin wannan salon, The Secret of NIMH, The Iron Giant da dai sauransu an yi amfani da zane.

Limited Animation:

wannan kashin yafi sauki, domin wajen zanen da kuma hanyar zana shi ba a cika lura da na kwaikwayon don misalan irin wannan kashi su ne kamar The Flintstones, Yellow Submarine da dai sauransu.

Rubber Hose:

A irin wannan tsari, akasarin zanen mutumin ko abin da ake a sawa motsi, ana zana su gwai-gwai (cartoony) wato ba kamar mutanen gaskiya ba, a wannan salon mai zane na da ‘yancin yin zanen kowane iri ba tare da la’akari ko ya yi kama da abin da yake kwaikwayar zanawa ba, haka ma kuma a wajen sa shi motsi(animating), misalan irin wannan animations din da aka yi amfani da su ne sun hada da Mickey Mouse din da aka fara a farko, Ren and Stimpy, Popeye da dai sauransu.

Stop Motion Animation

Stop Animination, Animination ne da ake amfani da abin daukar hoto a rinka daukar shi hotunan daya bayan daya, wanda ta yadda ba za a iya amfani da hannu ba wajen motsa shi. Daga karshe a zo a jera su a rinka motsa su a jere su zama animation movie , ga kadan kamar haka:

Cutout Animation:

A irin wannan tsarin animator(mai yin animation) yakan  yayyanka zanen da ya yi ya dinga motsa su yana daukar hoton su, sannan ya sa masu motsi ta hanyar bayyana su da sauri, misalan animationsdin da aka yi da irin wannan salon su ne; Monty Python’s Flying Circus, Tale of Tales da dai sauransu.

Puppet Animation: 

A irin wannan animation din animator ya kan  yi amfani da abu kamar bebin roba(puppets) wato wanda aka yi mai hannuwa da kai da kafafuwa, da dai sauransu, amma wanda zai iya tsayuwa da kan shi(armature), wato mai waige, yana motsa shi yana daukar hotonsa, kowane motsi hoto daya, wanda idan aka bayyana shi da Sauri sai ya zama hoto mai motsi(animated movie). Misalan animations din da aka yi da wannan salon su ne:  The Nightmare Before Christmas, Robot Chicken, The Tale of the Fox, da dai sauransu.

Clay Animation:

A irin wannan salon animator na amfani da yumbu ko wani abu mai kama da  yumbun ya gina abin da yake so ya sa wa motsi, ta hanyar yi masa waigi(armature)yana motsa su yana daukar hotonansu kamar  yadda animator mai bin salon Puppet Animation yake yi, abin da ya bambanta Clay Animation da Puppet Animation shi ne amfani da yumbu,  animations din da aka yi da wannan salon su ne; Creature Comforts, Dimensions of Dialogue Na Jan Švankmajer, The Amazing Mr. Bickford, Chicken Run, Wallace & Gromit, da dai sauransu

Computer Animation

Computer Animation, animation ne wanda ake yin shi ta hanyar amfani da computer, a irin wannan  Animation din ana zana hotunan da ake so a sawa motsi da tsara su da sanya masu motsi duk  ta hanyar amfani da computer, irin wannan animation din da shi aka fi amfani a wannan zamanin da muke ciki yanzu . Computer Animation ya kasu kashi biyu kamar haka:

1.            2D Animation

2.            3D Animation

2D Animation:

A irin wannan animationdin ana amfani da hotuna wadanda suke da kusurwa biyu 2D wajen yin animation, Traditional animation shi ma a wannan yanayin yake, amma shi ba da computer ake yin shi ba, a yau akwai software da dama da ake amfani da su wajen yin 2D animation kamar su; Flash, Corel Rave, Anime Studio, SwishMax da dai sauransu. Misalan fina finan  da aka yi da 2D animation su ne kamar:  SpongeBob SquarePants, Ben10, Naruto da dai sauransu.

3D  Animation:

A irin wannan animation din animator yakan yi amfani da hotuna wadanda suke a kusurwa uku 3D wajen hada animation, irin wannan animation din ne idan aka hada sai ka ga tamkar ba zane ba ne, za ka dauka komai gaske ne, shi ma 3D Animation yana software da yawa da ake amfani wajen yin 3D Animation kamar haka;  Maya, 3D max, Anim8or, Poser, iClone, Light Wave, Blender, da dai sauransu. Shima 3D Animation an yi amfani da shi wajen hada fina finan hotuna masu motsi masu yawa ga kadan daga ciki; Shrek, Toy Story, The Incredibles, ice age,Rio da dai sauransu.

Categories
Software

ANIMATION – Yadda ake MOTSA HOTUNA a Computer

Mene ne Animation?

Animation dai hotunane daukakku, tsararru, ko zanannu  masu motsi. Wandanda motsin da suke yi ya samo asaline ta hanyar jera su da aka yi daki daki.  Bayyanarsu hotunan da kuma motsin da ake gani yana faruwane a sabili da saurin da ake ginin wucewar hotunan ne, wanda yake  kayyadajje ta hanyar amfani da computer ko akasin haka.

Karkasuwar  Animtion

Animation ya kasu kashi daban daban, wadanda aka dunkule su aka kuma raba su zuwa gida uku kamar haka :

1.      Traditional Animation

2.      Stop motion Animation

3.      Computer Animation

Traditional Animation

Traditional animation , animation ne wanda ake yin shi ba tare da amfani da computer ba, shi ne irin animation na farko da aka fara a duniya.

Traditional animation ana yin shi ne ta hanyar zana hotunan (frames) da ake son motsa su da hannu ba tare da wata na’ura ba, sannan sai a kwafe su ko kuma ayi tracing(sake bin zanen da abun zanen)din su akan wata fellen roba mara kauri mara launi(wato transparent) mai sunaCels sannan a  daura su a zanannen hoton bango(background image) mai launi, bayan haka sai a dauko wani irin abun daukan hoto mai suna Rostrum Camera  a dauki zanannun hotunnan a rika jera su akan hoton bangonsu mai launi(background image) daya bayan daya. To bayan an wanke hotunan daga abun daukan hoton, sai a jera su akan  majigi (projector) a bayyanar da su da sauri, to a nan ne hotunan za su zama masu motsi (Animated movie),  fina-finan zane masu motsin (Animated movies) da aka yi amfani da irin wannan tsari sune;  The Lion King, Spirited Away, Les Triplettes de Belleville, Snow White da dai sauransu
A karkashin Traditional Animation za a iya karkasashi shima kamar haka:

Full Animation:

A irin wannan salon, ana yin zanen da kuma sa shi motsin yayi kamanni da dabi’un na dan adam na  gaskiya,  yawancin Animations din Disney ( kamfanin animations ne) suna  amfani da irin wannan salon, The Secret of NIMH, The Iron Giant da dai sauransu.anyi anfani da tsane.

Limited Animation:

wannan kashin yafi sauki, domin wajen zanen da kuma hanyar zana shi ba a cika lura da na kwaikwayon don misalan irin wannan kashi sune kamar The Flintstones, Yellow Submarine da dai sauransu.

Rubber Hose:

A irin wannan tsari, akasarin zanen mutumin ko abin da ake a sawa motsi, ana zana su gwai-gwai (cartoony) wato ba kamar mutanen gaskiya ba, a wannan salon mai zane na da ‘yancin yin zanen kowane iri ba tare da la’akari ko yayi kama da abinda yake kwaikwayar zanawa ba, haka ma kuma a wajen sa shi motsi(animating), misalan irin wannan animations din da aka yi amfani da sune sun hada da Mickey Mouse din da aka fara a farko, Ren and Stimpy, Popeye da dai sauransu.

Stop Motion Animation

Stop Animination, Animination ne da ake anfani da abin daukan hoto a rinka daukan shi hotunan daya bayan daya, wanda ta yadda ba za’aiya anfani da hannu ba wajen motsa shi Daga karshe a zo a jerasu a rinka motsa su a jere su zama animation movie , ga kadan kamar haka:

Cutout Animation:

A irin wannan tsarin animator(mai yin animation) ya kan  yayyanka zanen da yayi ya dinga motsa su yana daukan hoton su, sannan ya sa musu motsi ta hanyar bayyana su da sauri, misalan animationsdin da aka yi da irin wannan salon sune; Monty Python’s Flying Circus, Tale of Tales da dai sauransu.

Puppet Animation:

A irin wannan animation din animator ya kan  yi amfani da abu kamar bebin roba(puppets) wato wanda aka yi mai hannuwa da kai da kafafuwa, da dai sauransu, amma wanda zai iya tsayuwa da kanshi(armature), wato mai waige, ya na motsa shi yana daukan hotonsa, kowane motsi hoto daya, wanda idan aka bayyana shi da Sauri sai ya zama hoto mai motsi(animated movie). Misalan animations din da aka yi da wannan salon sune:  The Nightmare Before Christmas, Robot Chicken, The Tale of the Fox, da dai sauransu.

Clay Animation:

A irin wannan salon animator na amfani da yumbu ko wani abu mai kama da  yumbun ya gina abinda yake so ya sa wa motsi, ta hanyar yi masa waigi(armature)yana motsa su yana daukan hotonansu kamar  yadda animator mai bin salon Puppet Animation yake yi, abinda ya bambanta Clay Animation da Puppet Animation shi ne amfani da yumbu,  animations din da aka yi da wannan salon sune; Creature Comforts, Dimensions of Dialogue Na Jan Švankmajer, The Amazing Mr. Bickford, Chicken Run, Wallace & Gromit, da dai sauransu

Computer Animation

Computer Animation, animation ne wanda ake yin shi ta hanyar amfani da computer, a irin wannan  Animation din ana zana hotunan da ake so a sawa motsi da tsara su da sanya musu motsi duk  ta hanyar amfani da computer, irin wannan animation din da shi aka fi amfani a wannan zamanin da muke ciki yanzu . Computer Animation ya kasu kashi biyu kamar haka:

1.      2D Animation

2.      3D Animation

2D Animation:

A irin wannan animationdin ana amfani da hotuna wadanda suke da kusurwa biyu 2D wajen yin animation, Traditional animation shi ma a wannan yanayin yake, amma shi ba da computer ake yinshi ba, a yau akwai software da dama da ake amfani da su wajen yin 2D animation kamar su; Flash, Corel Rave, Anime Studio, SwishMax da dai sauransu. Misalan fina finan  da aka yi da 2D animation sune kamar:  SpongeBob SquarePants, Ben10, Naruto da dai sauransu.

3D  Animation:

A irin wannan animation din animator yakan yi amfani da hotuna wadanda suke a kusurwa uku 3D wajen hada animation, irin wannan animation din ne idan aka hada sai kaga tamkar ba zane bane, zaka dauka komai gaske ne, shima 3D Animation yana software da yawa da ake amfani wajen yin 3D Animation kamar haka;  Maya, 3D max, Anim8or, Poser, iClone, Light Wave, Blender, da dai sauransu. Shima 3D Animation an yi amfani da shi wajen hada fina finan hotuna masu motsi masu yawa ga kadan daga ciki; Shrek, Toy Story, The Incredibles, ice age,Rio da dai sauransu.