Categories
Software

Adobe Acrobat da Adobe Reader: Banbancin da ke Tsakaninsu

A cikin ƙoƙari da kamfaninn Adobe da ke kasar Amurka ya yi shi ne na ganin ya fitar da wani tsari da za a riƙa yin amfani da shi wajen yin musayar takardu na kwamfuta ta hanyar da kowo zai iya yin amfani da shi ko kuma ya karanta ba tare da ya yi amfani da asalin manhajar da aka ƙirƙiri waɗannan shafuka ba.
Kamfanin na Adobe wanda ake furta shi da yadda ake rubuta shi wato ‘adobe’ ba kamar yadda wadansu suke kiransa ba da ‘adob’ ya fitar da wani tsarin buɗe takardun kwamfuta mai suna PDF wanda cikakken ma’anarsa yake nufin Portable Document Format. Shi wannan tsari ne da ake musayar takardun da ake buƙatar a karanta su a cikin kwamfuta ba tare da an yi amfani da asalin manhajar da aka rubuta su ba. Wannan tsari ya sauƙaƙa matuƙa domin shi wannan tsari dai ya kawo wani irin sauyi matuƙa a sakamakon daidaitawa da aka samu saboda kusan kowane mutum a wannan lokaci yana amfani da wannan tsari na PDF sai dai in da gizo ke saka mutane da yawa suna samun ruɗani matuɗa wajen banbacewa tsakanin Adobe Reader da kuma Adobe Acrobat mene ne banbancin da ke tsakanin su.
Da farko ya kamata mai karatu ya fahimci cewar Adobe Reader manhaja ce da take kyauta da kamfanin ya ƙirƙira kuma aikin ta shi ne ta baka damar ka iya buɓe dukkan wani takardun kwamfuta da ƙarshensu ya kare da PDF. Sannan kuma shi wannan manhaja kyauta ake samun ta, kuma kamfanin koda wane lokaci ya na ƙoƙarin inganta ta ta hanyar canza mata tsare-tsare da kuma gyaran dukkan wani abu da zai iya zama barazana ga takardun mutane masu amfani da ita.
Wani kuma ƙarin jin daɗi a kan wannan tsari shi ne mutumin da ya yi aiki a wani irin manhaja da take da wahalar samu kuma yana son ya aika da wannan takarda ko aiki da yayi domin wasu su gani kuma su karanta to hanya ɗaya ita ce ya mayar da wannan aiki na shi ya koma PDF hakan kuwa ba za ta yuwu ba sai idan kana da Adobe Acrobat.
Ke nan Adobe Acrobat shi ne manhajar da ake yin amfani da ita a ƙirƙiri takardun da Adobe Reader zai yi amfani da shi, wannan kuwa haka abin yake sai dai kuma wani ƙari a kan haka shi ne shi kanshi Adobe Acrobat ya na buɗe dukkanin takardun PDF sannan kuma kana iya yin ‘yan gyare-gyare a kansu.
Da na yi maganar gyara-gyare a kan takardun PDF sai na ga ya dace in yi takaitaccen bayani game da abubuwan da ake iya yi da Adobe Acrobat wanda ba ya yuwuwa a yi shi da Adobe Reader.

1. Bude PDF

Dukkanin su su biyu Acrobat da Reader suna buɓe PDF sai dai shi Acrobat yana da wani irin ƙarin ƙarfi wajen buɓewa da dubawa. Domin Reader shi kawai zai baka dama ka duɓa shi ne kawai, amma kuma ba zai baka dama ka yi waɗansu ‘yan abubuwa, wanda duk wanda yake da Acrobat kamar yin jawabi ƙarƙashinsa da makantansu.

2. Ƙirƙirar PDF

Kodayake wajen ƙirƙirar takardun PDF Acrobat kaɗai yake iya yi, saboda haka a lokutan baya duk mutumin da yake da buƙatar ya canza aikin da ya yi daga asalin manhajarsa zuwa takardun PDF dole sai ya sayi Adobe Acrobat, wanda a wancan lokutan ƙirƙiran takardun PDF ya na da matuƙar wahala. Amma a wannan lokacin an ɗan samu sauƙi kusan manyan kamfanonin da suke yin manhajoji kamar Microsoft, Corel Inc, da irin su CAD dukkan su sun sayi wannan tsari a wurin Adobe sun sayi tsarin sun saka shi a cikin manhajojinsu, wanda duk sanda ka yi wani aiki a ɗaya daga cikin manhajojinsu za ka iya canza shi zuwa ga takardun PDF, waɗanda su wadanna takardu suna zuwa ma mutane a matsayin takardu kawai. Amma duk da haka akwai abubuwa da Adobe Acrobat yake iya yi wanda babu wata manhaja da za ta iya yi.
Misali bayan canza ko wane irin takardar kwamfuta zuwa PDF sannan kuma da Acrobat za ka iya saka wadansu abubuwa a jikin shi PDF ɗin kamar ya bayar da damar a yi jawabi ko ‘comment’ a Turance, sannan kuma mutum zai iya saka majigi ko kuma hotuna masu motsi ‘video’ haka mutum zai iya saka sauti ko amo a cikin shi takardar wanda duk waɗannan abubuwan da ma waɗansu babu wata manhaja da za ta iya sai Acrobat.
Kodayake su kansu kamfanin Adobe suna da Acrobat iri uku waɗanda suke da ayyuka mabanbanta, suna da Adobe Acrobat Standard sannan akwai Adobe Acrobat Professional, sannan akwai Adobe Acrobat Professional Extended.

3. Yin gyara a cikin PDF

Saboda haƙiƙanin dalilin ƙirƙiran PDF domin kiyayewar lalacewar asalin aikin da mutum ya yi ko kuma canzawa, misali a lokacin da ka yi rubutu a MS Word sannan ka aika da shi wani wuri domin karantawa to za a iya canza wani abu wanda ba kai ne ka yi hakan ba. Amma idan ka aika da aikin ka a tsarin rubutu na PDF to dole kowa sai dai ya karanta shi kawai ya bar shi yadda ya gan shi. Saboda haka, a yanzu wannan maƙasudi yana nan a hakan, sai dai wanda yake da Acrobat shi a lokacin da yake canza document zuwa PDF zai iya bada damar da mutum zai iya cika Fom da a ka tsara ko kuma mutum ya yi sharhi ko jawabi kamar comment. Shima wannan damar sai idan mai ƙirƙiran PDF ɗin ya bayar da ita, idan bai bayar ba mutum ba zai iya yi ba. Sai dai dukkanin nau’o’i na Acrobat suna iya baka damar da zaka iya haɗa PDF da yawa su koma guda ɗaya. Amma dai maganar canza rubutu da aka yi shi da PDF abu ne da kamar wuya, amma kuma idan mutum yana da Acrobat zai iya sake mayar da PDF ya koma wani tsarin rubutu na kwamfuta.

4. Fom a PDF

Wani abu kuma shi ne ana iya yin amfani da Acrobat a ƙirƙiri fom domin karɓar bayanai a wurin mutane, kamar yadda mutane suka sani cewar a wasu shafuka na intanet ana amfani da fom a amsa tambayoyi sannan kuma a aika da amsar zuwa ga waɗanda ya dace? Haka shi ma Acrobat ya na da tsari na musamman wanda yake ba mutane damar ƙirƙiran shafuka waɗanda za a iya saka tambayoyi da za a amsa a cikinsa sannan a aika ko kuma a ɗaba’anta shi.

5. Kudin Manhaja

Lallai kamar yadda muka yi bayani a kan cewar kamfanin Adobe suna bayar da manhajar buɓe takardun PDF kyauta wannan haka yake, a daidai lokacin da muke rubuta wannan maƙalar kamfanin na Adobe yana da Adobe Reader ta 11 wanda ya kira da Adobe Reader XI wanda za a iya saukar da ita a babban shafinsu da yake http://www.adobe.com sannan kuma saukar da wannan manhaja a wannan shafi shi ya fi ko’ina inganci kamar yadda muka yi bayanin hatsarin da yake cikin saukar da wani manhaja ba a asalin shafin da a ka yi ba.
Amma shi Adobe Acrobat shi ba kyauta ba ne, kasantuwar yana da abubuwa da zaka iya yi da shi ba kamar Reader ba. Shi Adobe Acrobat Pro kuɗinsa yana farawa daga Dalar Amurka $500 sannan shi kuma Acrobat Standard yana farawa daga Dalar Amurka $300.
Da fatan yanzu mun fahimci banbancin da ke tsakanin Adobe Reader da Adobe Acrobat.