Categories
Duniyar Internet

Yadda za ka iya canza Username a 2go

Abin ya na da ban haushi a ce baka yi aune ba sai bayan da ka gama yin rigista da 2go sannan ka fahimci cewar ai ka yi kuskure a wajen saka sunan da zai rika wakiltarka. Saboda haka da zarar mutum ya ga haka zai yi ƙoƙari ya ga cewar ya canza wannan Username amma abin ba zai yiwu ba da application na 2go.

Zaka iya cimma wannan nasara ne da farko idan ka shiga shafinsu kai tsaye wanda za su baka doguwar takarda da zaka cika domin samun damar canza sunan ka. Wannan kuwa akwai ɗaukan dogon lokaci da wahala a kan haka.

Saboda haka idan har ka tsinci kanka a irin wannan hali sannan kuma ka faɗo cikin wannan shafi to sai muce alasan barka, domin wannan shafi zai warware maka wannan matsala cikin ruwan sauƙi ba tare da ka samu damuwa.

Da farko dai yana da kyau ka sani cewar dole ne layin da ka ke amfani da shi na 2go ya kasance akwai kuɗi a cikinsa. Domin kwamfanin 2go za su gutsiri ‘yan kuɗi ƙalilan da ba zasu wuci N30 zuwa N50 domin biya maka wannan buƙata.

YADDA ZAKA KA CANZA PROFILE NA KA

Mataki 1: Ka aika da ƙaramin saƙo da kalmar UPDATE zuwa 32120. Za su cire maka wannan kuɗi da muka faɗa, sai ka jira za su aiko ma ka da saƙon SMS su ma. A cikin saƙon za ka ga link (wani dogon rubutu mai launi shuɗi) sai ka hau kansa ka latsashi zai kai ka kai tsaye zuwa in da za ka canza kusan duk abinda ka ke son ka canza game da 2go.

Mataki 2: Idan kuwa ba ka ga wannan saƙon ba to sai ka buɗe browsar ka tsaye sai ka gangara ƙasa sai ka kai inda aka rubuta service option a nan ne za ka ga shi link ɗin sai ka latsa shi zai shigar da kai inda zaka gyara username ɗin ka.

Da fatan wannan dan takaitacciyar muƙalar za ta wadatar.