SHIN KANA SO KA ZAMA ANIMATOR?

A mujallar da ta gabata na yi bayani a game da mene ne animation da kuma karkasuwarsa, a yau kuma da izinin Allah za mu yi bayani ne a kan ya ya za ka fara yin animation da kanka ka zamo animator kuma da irin fa’idojin da animation kan gabatar ga animator.

Wanne ne Animator?

Animator dai shi ne wanda yake da ilimin yadda ake yin animation kuma yana yin sa don nishaɗi ko don samun kuɗi ko kuma don duka biyun, kuma a wani lokacin ma, animators ba cartoon kaɗai suke yi ba har da wasu siddabarun cikin fina-finai (visual effects) kamar su tashi sama, mutum ya bace, tashin bom da dai sauransu, kuma suna haɗa Kwamfuta ‘games’ (wasanin Kwamfuta) da video game (da wasani da ake haɗawa da talabijin).

Shin waɗanne irin fa’ida animators kan samu a yin animation?

          Gaskiya haƙiƙa animators kan samu fa’idoji da yawa ta hanyar aikinsu na animation, domin animator kan iya yin aiki a kamfunan shirya fina-finai (film industry) tallace-tallacen talabijin, shafukan intanet da dai sauransu wanda zai yauƙaƙa hanyar cin abincinsa. Kuma har wa yau zai iya haɗuwa da wasu animators, su haɗa shirin fim wanda tun daga farkonsa zuwa ƙarshensa hotuna ne masu motsi zalla (animated movie) wanda shi ma zai iya kawo musu kuɗaɗen shiga, bayan fa’idar kuɗi, animation zai iya sa animator ya zama tauraro (celebrity) ko ina a duniya a san da shi, misali kamar yadda aka san su Jeff Lew, Walt Disney, William Hanna da Joseph Barbera, Len Lye, Norman McLaren, Matt Groening, Hank Azaria da dai sauransu suka shahara a fagen animation ko ina an san da su.

To tun da haka ne ya ya za a yi in zama animator?

A gaskiya dai, akasari idan ka tambayi animators musamman ma na kasarmu Nijeriya  ya ya za a yi kai ma ka zamo animator? Za su fara baka amsa da cewa ai ka zo gidan sauƙi. Bayan haka sai su danƙara maka wasu faya-fayen CD da takardun karatu na Kwamfuta (PDF) na wani animation software ka koya, alhali ba su sanar da kai wasu ƙa’idoji da hukunce-hukuncen da suke cikin animation ba ko kuma ba kayan da su sanar da kai cikin sauƙi.

Ni a nan shawara ta ga mai karatu idan kana so ka zamo animator sai ka yi la’akari da waɗannan abubuwan:

  • Sa kai
  • Karatu/Neman ilimi
  • Kwarewa

Da izinin Allah za a ga bayanan waɗannan a mujalla ta gaba.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *