SHIN ANA IYA LEKEN ASIRIN KA TA WAYA (Smartphone)

Amsa ita ‘ei’ ana iyawa.domin mafi yawancin mutane dake amfani da manyan wayoyi (smartphone) irin su Android, iPad, iPod da dai sauransu makamantansu tamakar kusan tsirara suke. Akwai mutane da kan iya ganin tsirrin ka ta cikin wayar taka daga nesa. Babban abu ma shine akwai wadansu Apps da idan kasake kasa su a wayan ka zasu fara aiki aboye (background) kai tsaye harma da ansa kowar din wayar ka ( microphone) ta daukan maganganu ka tana aika dasu. Karami daga cikin irin wadannan Apps din shine stealthGenie (spyware) yakan zama abinda ake cema Trojan kuma yan iya aiki da IOS dinka, kai hasali ma yakan yi amfani da Android da blackberry ya aika taswirar (geolocate) dinka ya kuma saurari maganganun ka, sakunan rubut (text  messages)da hotunan ka ya aika dasu kulla yaumun.

Wani Kamfani yin wadannan Apps sun tabayin alfaharin cewan suna da mutane (customers) sama da dubu dari (100,000) duk da dai hukumar tsaro a Amurak ta cafke shi shugaban wannan kamfanin.

Zamu iya tunawa da maganganu da dan leken asirin nan na Amurka wato Edward Snowden da yayi cewan gwabnatin Amurka tana leken asirin waya, sakonnin e-mail da sauransu al’amuran internet na mutane da yawa a cikin duniya. Wannan magana ta tsohon jami’in CIA’s ta tabbatar mana cewan ai lallai NSA na anfani da hanyoyi daban- daban wajen neman sirrin mutane.

Akwai wane Apps da ake kira dasuna Angry birds shima yana daya daga cikin Apps da ake amfani da shi wajen leken asirin.

Saboda haka nake ganin ma cewan ka kikiyaye zuwa bandaki da wayar (smartphone) domin tana iya maka tonan silili.

Masu bincike a jai’ar Stanford sun gwada wani Apps (Gyrophone) domin tabbatar da irin wannan zargin kuma sun ta gano cewan lallai amsa kuwar waya ( microphone) kan iya aika sautin ka, kai harma da gano wanda ke yin magana. Wannan Apps na da karfin tafiya a iska na 80 – 250 Hz akan iska.

Sun gano da tabbatar ma duniya cewan aamfani da wannan Apps (Gyrophone) za’a iya gano mai magana dama mai amsa maganar. Sun gwada akan wayar Android yayi aiki yanzu ma har sun fara gwadawa akan iPhone.

Wasu jami’o I ma kamr Citizen lab a jami’ar Toronto sun yi wannan gajinda gano masu leken asiri ta irin wannan hanyara akasar Italia. An tabbatar cewan masu leken asirin suna amfani da GP’s tracker na amsa kuwar ka da zaran ka hau yanar gizo (internet) ta Wi-fi.

Binciken ya nuna cewan akwai na’urorin leken sirri (servers) guda 350 akasa shen duniya guda 40 da ake amfani dasu. Abin tambaya anan shine, gwabnatocin sun san dahaka kuwa? Idan ko sun sani kenan suma suna leken asirin wayan mutanensu.

Saboda haka kalura domin waya ka ta smartphone da kake tunkaho da ita kake makale da ita kullun da guije ma kadai ci mai ton amka asiri ce. Saboda haka abin sai addu’a.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *