Sabon Virus ‘Internet Doomsday’ yau zai bayyana zai kuma kwace ragamar Internet

A yau 9/7/2012 a ke sa ran bayyanar daya daga cikin mabannacin Computer Virus mai suna ‘Internet Doomsday’. Shi dai wannan virus kamar yadda hukumar lura da bincike ta Amurka “Federal Berue of Investigate” suka fadi a lokacin da suka cafke wanda ya kirkiri shi wannan virus din.
wannan virus wanda aka ce a watan Nuwanban 2011 ya lalata sama da Kwamputoci miliyan hudu (4 Million), a na sa rai zai yiwa masu shiga internet ta’adi ta hanyar chanza musu gidajen internet da suka nemi shi, wannan shine kadai abinda ake tunanin zai iya yi amma kuma sauran barnar ba a santa ba. Shi dai wannan virus wanda zai rika kai mutane masu shiga internet gidajen da basu nemi shigansu ba yana nuna cewar computoci a yau 9/7/2012 zasu kamu da wasu cututtuka wanda basu san da su ba.
sabo da haka ba wai kayi wayau bane idan baka shiga internet a yau ba, hanya mafi dacewa shine ka yi kokarin duba Kwamfutarka idan akwai wannan virus din ko kuwa babu. Zaka iya cimma nasarar haka ta hanyar dubu ita Kwamfutar taka da wadansu program da kungiyar hadin gwiwa domin kare wannan virus (DNS Changer Working Group) suka yi da kuma hukumar tsaro ta FBI (FBI itself) wadannan kananan software wanda ba zasu wuce mintina hudu zuwa bakwai ba ka gama duba wa ko akwai wannan virus a Kwamfutarka ko kuma babu.
Haka a sa ran duk wanda yake amfani da Anti Virus mai kyau mai kuma lasisi idan har yayi updating din shi zai kare kanshi daga wannan kazamin virus din, wadannan anti-virus sune kamar Kerspasky da kuma Norton da makamantan su.
ko da yake wanda ya duba Kwamfutarshi yaga cewar ta kamu da wannan virus mataki na farko da zai dauka shine yayi kokarin kwashe mahimman abubuwanshi daga cikin Kwamfutar sannan kuma ya sami daya daga cikin su wadancan antivirus software yayi updating din su, yin hakan zai taimaka wajen cire wannan virus.

Related Articles

Ya kamata in damu da Hackers kuwa?

Zaka ji da zarar mutum ya san computer ko kuma ya iya sarrafata sosai sai kaji a na kiran shi da kalmar harcker. A gaskiya kalmar “hacker” tana da ma’anoni da dama da kuma fassara iri-iri, amma idan aka dawo akan harkar da ta shafi computer kuma kana son ka yi maganar hackers da computer to bai wuce ta basu ma’ana guda biyu ba wadanda su wadannan ma’anoni biyun duk kana bukatar saninsu. Kamar yadda aka fasara kalmar hacker a wani dictionary mai suna “Merriam-Webster” “Hacker kwararren masanin ilimin sarrafa computer (programmer). Shi kuwa wannan ma’ana da suka ba da ta kunshi kusan mutane da dama masu amfani da computer amma kuma wadanda ba a tunanin zasu iya cutar da wani.

Amma ma’ana ta biyu tafi ta da hankali matuka, domin Hacker shine mutumin da ya shiga cikin Kwamfutar mutum ta barauniyar hanya domin ya saci wasu mahimman bayanan shi ko kuma ya yi maka ta’adi”. Idan muka fuskanci wannan ma’ana ta biyu yana nuna mana cewar dukkanin wani abu da hacker yake kokarin yi shine ta’addanci tare da Kwamfutar mutane ta hanyar da kuma barna, domin hakan na faruwa ba tare da sanin mai amfani da Kwamfutar ba.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. To nidai babu wata dabara dazamuyi sai dai muce muna hannunku, har idan anga irin wadannan cututtukan na kwampiyuta adaure acigaba dabamu sha warwari.