RECYCLER VIRUS – Shi ke cinye Folder ya mayar da ita SHORTCUT

https://youtu.be/Yq-aSi93aFw

RECYCLER VIRUS

Recycler Virus wani daya daga cikin virus ne da ake da su a cikin kusan Virus sama da miliyan bakwai da ake da su a duniya, na san wani zai yi mamaki a kan haka, shi dai makasudin yin wannan virus domin ya rinka hayayyafar kan shi a cikin computer ne, ta yadda zai rinka kirkirar folder da take cikin computer ka. Misali idan wannan virus ya shiga cikin Kwamfutarka kuma babu antivirus a cikin ta zai rinka kirkirar sunan folder yana karawa a cikin folder da ka bude. misali idan ka shiga cikin My Music folder sai ka ga wata irinta da suna My Music ammakarshen zai kare da .exe. Wani yanki na cutarwa da wannan Virus yake yi shi ne zai iya share maka file ko kuma document da ke cikin computer su koma da .exe idan haka kuwa ta faru idan antivirus ya gansu zai sharesu. Bayan da aka gano yadda wannan cutarwar take sai suka canza salo ta yadda idan wannan virus ya kama computer ka ba zai cinye files dinka ba sai ya cinye maka folders da suke cikin computer su koma shortcut.

YA ZAN YI IN DAWO DA FILES DA FOLDERS DA SUKA BACE?

Idan har ka fuskanci irin wannan matsala wacce take a daidai wannan lokaci da muke tattara wannan bayanai, kamfanin Microsoft wanda su suke yin Windows OS, kamar XP da VISTA da Windows 7 suna riga sun toshe waccan kafa da ake amfani da ita har RECYCLER VIRUS ta iya yin ta’adi a cikin Kwamfutarka sai dai tayi a jikin MEMORY, ko FLASH ko kuma EXTERNAL HARD DISK DRIVE, idan har ka ga Kwamfutarka da irin wannan virus ya kamata abu na farko da za ka yi shi ne ka yi Windows Update, idan ka yi wannan updating to ita computer da kanta za ta magance maka wannan matsala. Mataki na biyu shi ne ya kasance kana amfani da Licence Anti-Virus sannan kuma ka yi updating na shi shi ma. Duk wata computer da aka yi updating din windows dinta kuma aka yi updating antivirus dinta ta irin wannan virus na RECYCLER da wadanda ma baka sansu ba idan ya shigo computer ka zai zama kamar file irin su video ko music ko kuma word document bashi da wani tasiri ko kadan. To amma fa ka sani idan har kai baka da damar da za ka yi updating, misali, kana amfani da ita computer a Business Center ne kuma babu Internet Connection a wurin to akwai matsala, hanya mai kyau da za ka iya magance irin wannan matsala shi ne ka je ka yi downloading KASPERSKY RESCURE DISK a website na kaspersky da ke htt://www.kaspersky.com za ka same shi kyauta.

ME KASPERSKY RESCURE DISK KE YI?

Kaspersky Rescure disk yana taimaka maka wajen cire Virus a cikin Kwamfutarka ba tare da ka saka anti-virus ba, wato shi wani mukulline da za ka iya amfani da shi idan kafin Kwamfutarka ta loda windows sai shi wannan program na rescure disk ya fara aiki, zai yi installing kan shi na wucin gadi, wato a maimakon idan ka kunna computer ka ka ga windows ya tashi sai ka ga RESCURE DISK ya dauka. Ko da yake idan ka yi downloading din shi zai zo a dunkulellen file wanda ake kira da (ISO) kana bukatar wani program na musamman da ake burning cd kamar Nero ko Ashampoo Burning Studio da dai makamantansu, su ne za ka iya amfani da su wajen burning wannan file da ka yi downloading ya zama mai amfani. Wato bayan ka yi downloading dole ka mayar da shi ya zama CD ko DVD ta yadda Kwamfutarka za ta iya tashi da shi.

BABU VIRUS A COMPUTER TA AMMA FOLDERS BASU DAWO BA, YA ZAN YI?

Bayan ka kammala wadancan hanyoyi guda biyu, to daga cikin abin da shi wannan Virus yake yi shi ne ya mayar da Folder ya koma Shortcut. Asalin folders da suke cikin Flash Memory ko External Hard Disk suna nan, abin da shi wannan virus yake yi shi ne ya Boye su, su zama baka iya ganinsu ko da ka bude Hidden File da folders, amma dai lallai suna nan a ciki, wanda hakan ta faru da shi ya yi formatting, to ya sani ya yi ta’adin da shi virus din baiyi ba.

YA ZA A YI IN FITO DA BOYAYYUN FOLDER NA?

1. Za ka shiga Control Panel
2. Ka shiga Folder Option
3. Ka click a kan View
4. Ka nemi inda aka rubuta Hidden File and Folder
5. Ka latsa inda aka rubuta Show Hidden File, Folders and Drives
6. Zaka cire abubuwa guda uku da suke karkashin abu na biyar (wato za ka ga an saka alamar good a gefensu sai ka cire su)
7. Hide empty Drives in the computer folders
8. Hide extensions for known file type
9. Hide protected Operating System files (Recommended)
10. Idan ka cire na karshe zai nuna maka wani dan window sai ka latsa a kan OK
11. bayan ka gama sai ka yi clicking a kan Apply sannan ka saka OK
To bayan ka gama wannan matakai kamar yadda muka lissafa sai ka koma MyComputer ka bude Flash Memory ko kuma External Hard Drive za ka ka ga asalin folders da ke ke ciki, amma kuma sunyi dishi-dishi, wannan alama ce da ke nuna cewar wadannan file suna Boye ne, wadancan matakai da ka bi su suka fito maka da su a halin yanzu, sai mataki na karshe shi ne ka mayar da su folders su zama ba a Boye ba.

1. Za ka yi right clicking a kan folder da kake son ka fito da ita
2. Sai ka yi clicking a kan properties
3. Sai zaBi Customize
4. Sai ka latsa Change Icon
5. Wani karamin Window zai bude sai ka yi clicking a kan Restore Default
6. sai ka yi clicking a kan OK
7. sai ka dawo latsa General
8. A karkashin shi za ka ga Hidden sai ka cire good da aka saka
9. Sai ka yi clicking Apply sannan OK

wannan shi ne hanyar da za ka bi ka fito da wannan su wadannan Hidden folder da RECYCLER VIRUS ta Boye, amma kuma kana bukatar bayan ka gama fito da duka folders dinka, cire wancan matakai daka bi ka fito da hidden folder ka, domin barinsu a bayyane zai iya kawo matsalar lalacewar computer ka domin ka fito da dukkan sirrin files da suke cikin computer. za ka bi mataki na 1 zuwa 3 na farko, sai ka nemi Restore Default ka latsa, sannan ka clicking Apply, sannan OK.

 

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *