Protocol Me Wannan KALMA take nufi?

Protocol

Wannan kalma ta Protocol tana da matukar mahimmanci ta fannin sadarwa (Communication Technology) ta bangaren da ya shafi Computer. Ita Kalmar Protocol ararriyar kalma ce daga Girkawa wanda take nufin fallen takarda guda, wanda ya kunshi dukkan bayanin da ke cikin littafin wannan falle.

Amma idan muka danganta wannan kalma a ilimi na Computer ko Information Technology, yana da fage na musamman a bangaren cikakkiyar hanyar sadarwa ta Communication. Idan muka dauki ita wannan kalma ta Protocol zamu ga cewar ana samun ta kusan a kowane fage na hanyar isar da sako ko kuma tabbatar da ingantacciyar hanyar aiko da sako daga na’ura zuwa wata na’ura. Kamar TCP/IP wanda ke nufin Transimission Control Protocol kaga an sami kalmar a nan, Haka IP, shima Internet Protocol ita ma ga kalmar a ciki, haka HTTP wato Hyper-Text Transfer Protocol da dai makamantansu.

A misali, ana samun kalmar Protocol a cikin kowace hanyar sadarwa ta computer kamar yadda muka gani a wadanna kalmomi na baya, ko dai a sami tsarin Protocol a device (Dukkan wani abu da yake amfani da wutar lantarki ko kuma batir shi ake cewa device) ko kuma a application.

Idan ka hada computer da Internet lokacin da ka kunna Internet Browser domin fara amfani da wani shafi daga internet to su TCP/IP su suke da alhakin kaiwa da karbar dukkanin abinda mutum ke gani ko ke aikawa.

TCP na nufi Transmission Control Protocol, wato Protocol ne wanda yake da alhakin watsa dukkanin bayanai da ita internet take da shi, wanda shi TCP shine kuma yake iya hada compter ka da  zamu iya cewa dukkanin wani kulla alaka a tsakanin na’urori guda biyu, misali waya da waye, computer da computer ko kuma waya da computer to suna bukatar tsari guda da zai basu damar kulla wannan alaka, to dukkan wani tsari da zai daidaita tsakanin su shine ake cewa Protocol.

Related Articles

Yadda ake yin Bincike (search) da Google Search Engine (1)

A wannan rubutu da zan yi, zan raba shi kashi uku, kashi na farko bincike mai sauki, wanda ya ku san kowa shi yafi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shine zamu yi dan gyara akai. Kashi na biyu kuwa zamu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai saukaka matuka da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shine na karshe shi kuma zamu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a dduniya baki daya.

kamar yadda mafi yawa daga cikin mu suka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son yayi bincike shine ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta www.google.com a wurin da ake rubuta adireshi shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar, da zarar ya rubuta zai bude mishi shafin farko.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Assalamu alaikum, dafatan duk kunanan lafiya ina mika godiya da nuna farinciki da wannan mujalla da fatan zakusa sunana ajerin masu karanta wannan mujalla, kuma inaso insani mu mutanen garin jos a ina zamu rika samun wannan mujalla, massalam.

    1. Muna godiya kwarai da gaske, muna kuma son mu sanar da kai cewar a halin yanzu ana kan kokarin ganin anfitar da ita tun kusan shekara ta farko da aka fara ba’a sake ba.

  2. amincin allah da rahamarsa da albarkatunsa su tabbata agareku bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ina mika godiya ta gareku dalili kuwa shine yanzu na samu hanyar sauki daga ranar da na sami adireshinku. mb usman magaji suleja allah ya taimake mu baki daya amin.