Mujalla Ta Farko – Barka da Zuwa Duniyar Computer

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Kai, muna yi wa alummar hausawa da masu jin hausa murnar gabatar musu da wannan Mujallar Duniyar Computer.

Mun riga mun yi bayanai na makasudin fito da wannan mujalla a manufofinmu da ke shafi na biyu. Wanda ya kunshi dukkanin bayanai da ya kamata wanda zai karanta wannan mujalla da ya fara karantawa. Amma dangane da abubuwan da yake kunshe a cikin wannan bugu na farko, da farko zamu bai wa mai karatu hakuri na yawan rubutu da zai gani da kuma shafuka masu yawa, wannan ya samo asaline saboda shawara da muka yanke na zubo muku dukkanin abubuwan da muka saka a shafinmu na Internet, da kuma dukkanin tambayoyin da muka amsa a shafin dandalinmu na Facebook.

A cikin wannan fitowa mun yi cikakun bayanai akan mahimmancin ilimin computer, sannan kuma mun saka wata makala wacce take mai mahimmanci mai taken “Hankali ke gani ba ido ba” wanda wannan makala ta taba kowanne bangare na zamantakewar al’ummarmu akan abinda ya shafi ilimi da kuma harkar Computer. Bayan haka mun yi gamsassun bayanai akan abinda ya shafi maganar Computer Virus da yadda yake shiga Computer ko kuma wayar tafi da gidanka, sannan kuma mun kara bayanan cututtuka guda biyar kari akan biyar da muka saka a shafinmu na internet a makalarmu mai taken “Wurare guda 17 da suka fi ko’ina hatsarin shiga a Internet”.

A wannan fitowa mun saka wadansu makalai wadanda babu su a shafinmu na Internet wanda suka hada da babbar mukala mai taken “Mece ce Computer” inda muka warware abubuwa masu yawa akan ita kanta computer daki daki. Sannan mun tattauna da wasu dalibai ‘yan Najeriya da suke karatu a kasar Ghana wanda suka yi gamsassun bayanai akan yadda rayuwarsu take gudana da kuma karatunsu. Duk a cikin wannan fitowa mun saka Cikakken Tarihin Bill Gates.

Sannan kuma mun saka dukkanin tambayoyin da muka amsa a shafinmu na dandalin Facebook, domin wanda yake da irin wannan matsaloli da muka warware ya karanta kuma ya fahimta. Kasancewar wayar tafi da gidanka tana da wani fage mai fadi a computer shima mun tsakuro muku bayanai akan “Yadda ake yin Flashing na waya” wanda ya warware zare da abawa akan abinda ya shafi waya.

Da yake wannan mujallar ta ilimice kuma makasudin mu shine yin bayanai akan abinda ya shafi computer a ilmance, kusan duk abubuwan da muka saka a cikin wannan mujalla sai da aka tabbatar da ingancinsu da kuma tabbacinsu. Sannan kuma mun yi kokarin gwada dukkan wani ilimi da muka saka mun kuma tabbatar da haka yake.

Daga karshe muna son mai karatu ya sani cewar abubuwan da ya gani a wannan mujallar kusan ba shi bane yadda mujallar za ta kasance ba, duk da cewar mun yi kokari wajen tsara makalolinmu akan tsarin Hardware, da Software da networking da portable devices, mun yi magana akan Yadda Akeyi da kuma Ra’ayi wadanda sune tsarin da muka bi a shafinmu na Internet .

Fitowa ta gaba shi ne wanda zai nuna maka shirin wannan mujalla na asali, amma wannna fitowa mun saka dukkanin abubuwan da suke cikin shafin mu na internet sai kuma wasu kare-kare da muka yi domin ku masu karatu. Mun san za a sami gyara a cikin hausa ko kuma rubutu, to, muna neman afuwa akan haka, muna maraba da dukkanin wane korafi da kuma abin ci gaba. Kuma muna maraba da masu rubutu daga ko’ina suke a fadin duniya. Allah yayi mana jagora Amin. A sha karatu lafiya.

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. assalamu alaikum Mlm Salisu barka dakoqari Allah yaqara daukaka Dan Allah tambayata an an itace ya akeyin kutsen interernet yakuma mutum zai yi idan wani yayi masa ngd Allah yakarbi ibadummu smeen

  2. Assalam mlm salisu dafatan kuna cikin koshin lafiya, Inaso nasamu wannan mujjallan amma ni ba a Nigeria nake ba ko shin zaiyu nasamu koda a pdf ne??? Idan zaiyu ya yane sharuddan samun su kuma tayaya zan samu??? Allah ya taimaka!