Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke

Ko ba a gwada ba an san linzami yafi karfin bakin kaza, domin mahimmancin computer da iliminta ya wuce a ce mutum bai sani ba. Domin ko ba a fada maka ba lura da yadda ta mamaye kusan mafi yawanci abubuwan mu na yau da kullun. tun daga makarantunmu, ma’aikatunmu kasuwancinmu, asbitocinmu, gidajen yada labarai da makamantansu, dukkanin su za ka samu a na amfani da ita  Computer.

Kusan a wannan zamani, computer ta samar da sauki wajen tafiyar da alamura ga dan adam. Kama daga rubutun takardar wasika zuwa takardar sanarwa ta wajen aiki ko takardar notice, takardar biyan albashi da lissafin kudaden kasa da yin kasafin kudi, hada da harkar hada- hada, da bayanai na kididdiga da fitar da kudade a bankuna, duk computer ta kawo sauki ta kowanne fanni.

Haka kuma computer ta samar da sauki wajen tafiyar da harkar banki, ka duba ATM yanda yake, computer  take karbar cheque ko kuma ta baka kudi, ko kuma ta cireshi. Ga wadanda suke sayan kaya a kasashen waje suna amfani da computer wajen duba yanayin kayan su da kuma sannin a wane wuri kayan suke da kuma lokacin da kayan zasu iso. Ta bangaren kasuwanci, idan ka zuba wa computer bayanan harkar kasuwancin ka, kayan daka siyo, ka ware mata kudaden wahalhalunka, kama daga kudin abinci, kudin sallamar ma’aikata, kudin dauko kaya, kudin shago da kudin wuta za ta fitar maka da ribarka ko kuma faduwarka a dan kankanin lokaci.

Haka za ta iya a jiye maka wasu mahimman bayannanka bayan tsawo shekaru idan ka nemi ta fitar maka za ta fito maka da su.

Haka da zamu koma wajen fanin kula da lafiya ana amfani da computer wajen binciko yanayin cuta da mazauninta a jikin dan adam, ba tare da likita ya tambaye shi ba, hakanan  ana iya bincikar cikin da mace take dauke da shi a gane lafiyar shi ko rashin lafiyar shi da yanayin kwanciyar shi, duk a cikin dan kankanin lokaci.

Dawo bangaren makarantu zaka samu suna amfani da computer wajen saukaka bincike da nazarin darussa ga yara. Sukan yi amfani da ita computer ta wajen kimiyya da fasaha don gano adadi da kididdiga. Ana samun na’ura da take dauke da muhimman takardu ga daliban fiye da dubu dari uku wanda zai yi wahala a sami wani laburari a karamar makaranta dake de littafi daban daban har dubu goma.

Ta hanyoyin sadarwa computer tana taimakawa gidajen jarida, da na watsa labarai wajen gyare gyaren tarin rubutu ,video da sauti wanda a dan kankanin lokaci sai su gyara ayyukansu don watsawa don haka da taimakon computer ba sa bukatar sai sun shiga studio kafin su dauki bayanan da za su watsa.

Haka nan sadarwa da aka samu ta yin amfani da wayoyin ta fi da gidanka(salula) za ka iya rabuta wasika ka aika, zaka iya aje alama ta tunatarwa, zaka iya daukar hoto ko video zaka iya yin lissafi da dai makamatansu ciki dan kankanin lokaci ba tare da wahala ba.

Kasancewar ci gaban internet ya mamaye dukkan fannonin rayuwar dan adam a yau ba ta tafiya yadda ya kamata sai da internet ilimin computer shine sinadarin cin moriyar internet

Idan kuwa muka duba bangaren tsaro, a zamanin da, zaka samu yana da wahala a gano file(kundin) na laifi da mutum yayi bayan an kai shi kotu, amma yanzu da zarar an saka bayanan shi, nan take za a samu, ka duba irin Computer da take bincikan ‘yan yatsu da fuskar wanda ake zargin shi da laifi, ko da yake yanzu ne aka fara irin wannan tsari a wannan kasa ta mu Najeriya.

Haka idan ka duba hatta cikin motoci da abubuwan hawa kamar jirgin sama, da jirgin kasa da jirgin ruwa za ka samu akwai computer a jikinsu, daga abinda yake sarrafa yanayin zafi ko sanyin abin hawa computer dake ciki take tafiyar da shi. Ballantana uwa uba ire-iren abubuwan hawa da ake kerowa na zamani a yanzu akwai motar da ake samun computer a cikin ta wacce duk inda wannan motar take a duniya za a iya kashe ta ko kuma a kunna ta, haka nan jirgin sama muna da labarin jirage irin na yaki wanda kasahen da suka ci gaba suke da su wadanda babu matuki a cikinsu, computer da ke ciki ita take sarrafa su, wanda ko da abokanen gaba sun harbo wannan jirgin to ba za a rasa rai ba.

Computer ta kawo sauki ga masu ayyuka irin wanda a da sai an dauki tsawon lokaci ko kwanaki kafin ace an kammala su. Misali abin da ya shafi lissafin dukiya don fitar da gado an sami sauki mai yawa ,idan ka duba Computer da take rabon gado wanda duk abinda mutum ya mallaka komai yawansu, komai yawan wanda za su gaje shi, da zarar an gama zuba mata bayanan dukiyar da magadan sakon biyar yayi yawa ta gama raba wannan gado kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fadi ayi ba tare da ta rage wani abu ko ta karashi ga wani ba.

Mu koma bangaren kere-kere shima Computer tana taka mahimmiyar rawa wajen kere- keren abubuwa wanda a zamanin da, sai an sami karti majiya karfi suke iya kera wannan abun. Idan muka koma harkar zane zane, yanzu an kai fagen da idan ka nuna fili kace ga girmanshi, kana son bishiya kaza, filawa kaza,  kana kuma son mota irin kaza, ga irin fenti da kake so, ga irin kofofi da dai dukkan abinda za ka fadi da ya kamata a ganshi, kana gama lissafi wanda zai zana maka gidan yana kwafewa a ‘yar karamar takarda a hannunshi, da zarar ya gama zana gidan sai yayi amfani da daya daga cikin program na Computer ta gina wannan gida a cikin ta kamar yadda kace kana son, ka ganshi kamar da gaske babu wani abu da za ka ce ba na  gaske bane, wanda idan kace kana son a bude maka cikin gidan kaga yadda kujeru da bayi da kayan kichin suke duka za ka gani. Kuma idan aka gama gina maka gidan na zahiri za ka ga babu bambanci tsakanin na cikin Computer da naka na waje. Abun kamar almara.

Dawo bangaren “na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya taras” wato noma da kiwo, wadannan sana’o’i a wannan zamani za ka ga yadda na’urar Computer ta ke taimakawa wajen ganin inganci gona da abinda manomi zai shuka, da yadda ake yin taki, da yadda ake fitar da magungunan kwari, da dai makamantansu. A yau akwai Computoci wadanda suke sarrafa kayan gona, kamar irin computer da take tsotse ruwan jikin tumatiri ta kyafeshi a cikin dan kankanin lokaci, babu ruwanka da shanya da makamantansu.

Idan kuwa muka zo bangaren kasuwanci, ai abin ba a cewa komai, ka duba hada-hada irin ta banki yadda abubuwa suka saukaka, a da, babu yadda za ka je wani banki ka ajiye kudi sannan kaje irin wannan banki ka cire kudinka, ballantana ace kaje wani gari ko kuma kaje wata kasa, ai babu hali. Amma a wannan zamani da ilimin computer ya yawaita, bama ka saka kudi a cikin account dinka ba, hatta saye da sayarwa za ka yi a duk inda kake so a duniya, kuma a kawo maka inda kake so, ba tare da kaje wurin ba, ko kayi magana dasu baki da baki ba, ta Computer za a gama komai, su nuna maka irin kayan da suke da su, da farashinsu, su kuma gaya maka idan har ka siya wadannan kaya kwana kaza za suyi daga kasa kaza zuwa kasa kaza. Koma ga kananan ‘yan kasuwanmu masu sayar da kayan taro da sisi sannan kuma masu son su kididdige cinikinsa, to, kaga abinda yafi dacewa da su itace Computer. Domin itace wacce komai yawan cinikin da akayi a rana ko shekara idan aka ce ta kawo lissafinsa za ta kawo ba tare da wani bata lokaci ba. Ba lissafi kadai za ta iya yi maka ba, hatta  irin ribar da kake son ka samu zata fitar maka, zaka gaya mata kudin kaya, ka gaya mata kudin dako, ka gaya mata kudin abincinka da yaran shagonka, ka gaya mata adadin yawan kayan da ka siyo, ita kuma ta baka mamaki wajen fitar maka da taswirar yadda za ka sami cikakkiyar riba. Kai hatta abubuwan da ka siyar a baya ita Computer zata iya fitar maka da bayanai na ban mamaki, kamar ta gaya maka a shekaru talatin da ka  ke kasuwanci shekara kaza kafi cin riba, sannan wata kaza kafi cin riba, sannan ta fitar maka da shekarar da kafi faduwa da rashin ciniki, sannan ta gaya maka kwastomanka da yafi kowa siyan kaya awurin ka da wanda ya siya kaya sau daya da sanda suka yi kasuwanci na karshe da abinda suka siya da kuma kudin da suka biya.

Sabo da haka, idan ka lura za ka ga cewar Computer wata makami ce da mutane suke amfani da ita wajen tafiyar da alamuransu na yau da kullum, sannan a wannan zamani da muke ciki a yanzu zai wahala dan adam yace zai gujewa amfani da Computer, domin na farko kusan mafi yawan mutane suna amfani da wayar tafi da gidanka (GSM), ga amfani da ATM wajen fito da kudi, da dai makamantansu, ballantana wanda yake da akwatin email, ko kuma yana amfani da dandali irin su Facebook ko twitter, ballantana wanda yake aikin jarida ko ma’aikacin asibiti da dai dukkan wanda rayuwarshi ta shafi harka da Computer.

“Bama a nan gizo ke saka ba” ka duba yadda duk mutumin da yayi karatun zamani komai zurfin karatun da yayi sai ka ga ya hada da na Computer, kuma zai yi wahala ace mutum yana da ilimin Computer ko yaya yake yaje neman aiki ace ba a sa sunan shi a cikin wadanda za a tantance ba, musamman ace ya karanta wani fanni mai mahimmanci, ko kuma wata babbatar ma’aikatar da ta kera wani program ko hardware sun bashi shaidar cewar shi kwararre ne (Certification). Kamar mutumin da ya karanta fannin kasuwanci ya sami daraja ta biyu (Second Class) amma gashi ya iya amfani da Computer  har yana da shaidar kwarewa akan Excel ko Peachtree wanda su wadannan software suna taimakawa wajen warware matsalar kasuwanci. To zai yi wahala yaje neman aiki ya zamanto ga wanda yake da daraja ta farko (First Class) amma bashi da wancan ilimin ace ba a dauke shi ba. Irin wadannan misalai suna da yawa, kamar mutumin da ya karanta fannin zane-zanen gidaje sannan ya zamanto bai iya amfani da computer ta fannin zane ba, kaga zai yi wahala a ce ga wanda ya karanta irin kwas na shi kuma ya san daya daga cikin program da ake zane dasu ace wancan aka dauka ba shi ba.

To ashe idan har gaskiya ne Computer ta kewaye kusan ko ina a harkar mu ta yau da kullum, babu abinda ya fi dacewa illa mutum ya fahimci yadda zai sarrafa wacce yake tare da ita, ko da kuwa yaya kankantarta yake. Na san mutane da yawa ba da son ransu suke son a ce su kai aikin sirrinsu wajen Business Center ba, wajen da babu sirri, ba ka san waye zai karanta sirrinka ba, ga shi kuma kana da Computer a gida ko kuma a ofis amma abin bakin ciki ba ka iya sarrafa ta ba. Ka duba wani abin haushi “nama na jan kare” zaka samu hatta waya a wannan lokaci zaka ga mutane da yawa basu iya sarrafa ta ba, sai dai idan an turo musu da sako su kira wani ya duba musu. Bama wannan shine ya fi ban takaici ba, hatta ATM wanda ba a son wani ya san lambobinka guda hudu da kake amfani da su na sirri ka ciro kudi, sai kaga mutum duk sanda zai ciro kudi sai ya nemo wani sannan ya ciro mishi. Ashe idan haka ne ilimin sanin yadda zaka sarrafa  Computer wajibi ne.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Hakika abun ba acewa komai , domin kuwa computer ta kawo mana sauki a cikin dukkan al’amurra . Muna godiya ga Allah S H W Daya arzitamu da wannan fasaha ta zamani . Allah kara sa mana fahimtarta Amin . Mun gode .