MU CANZA SALON TSARO A MASALLATAI

Kasancewar abubuwa na tashin hankali da suka faru a garin Adamawa da Kano inda aka rasa rayukan mutane da dama da kuma rahoton da na karanta a babban shafin ‘JIBWIS Nigeria’ na cewar an kama wasu da kayan agaji da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, na ga ya dace ni ma in yi amfani da wannan kafar domin kira ga dukkan Al’ummar Musulmi da cewar a ƙara tsaurara matakai a dukkanin Masallatanmu.

Muna kira ga dukkanin shuwagabannin Agaji na kowane fanni, musamman JIBWIS, FITYANU, HIZBAH, JNI da su tsaurara matakai a dukkanin wurin da suke tura ‘yan agajinsu, sannan kuma su sanya waɗansu alamomi ga dukkanin waɗanda aka ce su ne ke da duti a kowace rana. Su kuma hana duk wanda ba shi da duti sanya uniform ko kuma yin aikin da ba a sa shi ba.

Kada ka raina ƙoƙarin makashinka domin zai iya amfani da kowace irin dabara domin ganin ya cutar da kai. A sanya shingaye na bincike nesa da masallaci, a kuma fara tsare wurin ibadu tun da safe.

Su kuma jama’a don girman Allah ku ƙara ba dukkanin jami’ai goyon baya, domin suna sayar da ransu domin su ga ran ka da na sauran al’umma ya kuɓuta. Duk irin abin da ‘yan agaji suka umurci jama’a da su yi mu taimaka mu yi.

Wannan musiba da take sake salo dole kowa shi ma ya canza salo.

Matakai da jama’a za su ɗauka bayan a masallatai ya kasance har da kasuwanni, sannan kuma a guji yin taron da zai tara ɗaruruwan al’umma a wuri guda. Haka a ƙaurace wa duk wani abu da ba a gane mishi ba.

Wannan zai ƙara taimakawa wurin tsare dukiyar jama’a a ciki har da taka da ta ɗan uwanka, da abokanka, da surukanka, da malamanka, da iyayenka baki ɗaya.

Allah Shi ne masanin abin da ke faruwa, kuma shi ya bai wa kanSa masaniya game da irin ƙoƙari da hukumomin suke yi. Amma lallai mu ma sai mun tashi tsaye wurin ganin mun kau da duk wani irin abu da bai kamata ba.

Allah Ya sauƙaƙa mana al’amuranmu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *