Mene ne torrent website?

Menene torrent website? 04 July 2011 at 07:23 AbdulQadir Bello Muhammad

Duniyar Computer Malam AbdulQadir Bello torrent website wadansu gidaje ne na internet wadanda suke saka kayan sata a cikin shafukan su, sukan ajiye kusan dukkan wani software da kasani a duniya, kuma komai tsadarsa kuma kyauta, haka suna ajiyar littattafai ko wani iri, suna ajiyar games kusan dukkan wani abu da kake iya amfani da shi a computer zaka same su a cikin wannan gidaje, to, kasancewar wannan gidaje kasuwar kazamaice ya zamanto basa tace dukkan abinda wani zai saka musu a cikin gidajensu, ko wani irin kaya ka kawo wani yana bukatarshi, kuma idan kana bukatar wani kaya to zaka same shi, amma daga cikin matsalar da ake samu kusan idan aka kasa abinda ake ajiyewa a wannan shafukan 95% ana goya musu virus, shi yasa babu yadda za a yi mutum yana amfani da software ko games ko kuma videos ko kuma e-book na torrent ace computer shi ta rasa virus a cikin ta kuma su irin wadannan virus da ake samun su daga irin wadannan shafuka suna da matukar karfi, domin kwararru da gwanaye ne suke saka su. Ayi hattar kamar yadda muka fadi a darasin mu WURARE GUDA 17 DA SUKA FI KO INA HATSARIN SHIGA A INTERNET mun fadi hanyoyin da mutun zai bi idan har yaga cewar dole sai yayi downloading daga torrent websit.

Related Articles

Ya kamata in damu da Hackers kuwa?

Zaka ji da zarar mutum ya san computer ko kuma ya iya sarrafata sosai sai kaji a na kiran shi da kalmar harcker. A gaskiya kalmar “hacker” tana da ma’anoni da dama da kuma fassara iri-iri, amma idan aka dawo akan harkar da ta shafi computer kuma kana son ka yi maganar hackers da computer to bai wuce ta basu ma’ana guda biyu ba wadanda su wadannan ma’anoni biyun duk kana bukatar saninsu. Kamar yadda aka fasara kalmar hacker a wani dictionary mai suna “Merriam-Webster” “Hacker kwararren masanin ilimin sarrafa computer (programmer). Shi kuwa wannan ma’ana da suka ba da ta kunshi kusan mutane da dama masu amfani da computer amma kuma wadanda ba a tunanin zasu iya cutar da wani.

Amma ma’ana ta biyu tafi ta da hankali matuka, domin Hacker shine mutumin da ya shiga cikin Kwamfutar mutum ta barauniyar hanya domin ya saci wasu mahimman bayanan shi ko kuma ya yi maka ta’adi”. Idan muka fuskanci wannan ma’ana ta biyu yana nuna mana cewar dukkanin wani abu da hacker yake kokarin yi shine ta’addanci tare da Kwamfutar mutane ta hanyar da kuma barna, domin hakan na faruwa ba tare da sanin mai amfani da Kwamfutar ba.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *