Mene Modem ya kuma ake amfani da shi?

Modem dai kamar yadda mu ka sani  wani dan ƙaramn device da ake amfani da shi wajen haɗa computer da internet, da farko dai modem kala biyu suka fi shahara a Nigeria akwai Huawei da ZTE duk waɗannan modem ɗin ana kiransu da plug and play wato da zarar ka saka su a cikin computer zasu yi installing kansu, kuma su fara aiki kamar yadda aka tsara.

Modem waɗanda ake da su basa buƙata a ce mutum ya kasance ƙwararre ne kafin ya san yadda zai sarrafa su. Da zarar ka soka shi a jikin USB port, idan baka taba saka shi a cikin computer ba, zai yi ƙoƙarin ya fahimtar da ita computer cewar nine wane, ga kuma irin aikin da nake yi, daga bi sani zai fito maka da wani ɗan ƙaramin window da zai tambaye ka me kake son kayi da shi modem, nan take sai ka zaɓi Installation (wato zan saka shine ne).

Wani abu da ake kira Installation Wizard zai fito shi wannan wizard shine ke sauƙaƙa wa mutum wurin sanya ko wane irin application a cikin computer zai riƙa yi maka waɗansu ‘yan tambayoyi kai kuma kana bashi amsa ta wurin yin amfani da latsa maɓallin da yake cewa NEXT.

Idan ya gama shigar da application ɗin, zai sake fito maka da wannan ɗan ƙaramin windows irin na farko sai ka sake latsa wannan installation, wannan karan ba zai yi installation bane zai buɗe maka program ɗin ne. To, daga wannan wurine kake buƙatar ya zan fara browsing da shi wannan modem ɗin.

Mataki na farko shine ka sani cewar ko wane modem da ka saya yana zuwa da tsarin kamfanin layin shine, misali MTN modem yana zuwa da configuration na MTN ne kawai, sannan shi modem ɗin layin MTN kawai zai yi aiki da shi, haka ma sauran modem. Ko da yake ana yi amfani da wani application na musamman da yake iya lalata asalin tsarin da kamfanonin modem suka ƙ aga na cewar layi ɗaya kawai zai yi amfani ya koma yana amfani da ko wane irin layi, ma’ana idan kayi craking ɗin shi modem ɗin to zai koma universal moden wanda duk layin da aka sa mishi zai yi aiki.

Abu na biyu, shine dole ka sakawa wannan modem kuɗi dai dai da ƙarfin ka, domin cimma wannan nasara zaka latsa inda ka ga an saka Data Plan sai ka zabi plan ɗin da ka ga yayi maka kuma nawa zaka saka a cikin wannan plan ɗin idan N500 ko N8000 to sai ka buɗe wurin da ka ga an saka alamar kuɗi (Naira Sign) sai ka sayo kati ka rubuta pin ɗin kawai banda code ɗin wato idan Airtel ne ba sai ka saka *126* ba zaka saka pin ɗin ne kawai.

Bayan da ka tabbatar da kuɗin ya shiga sai ka koma wajen plan ɗin sai ka latsa maɓallin dake jikin plan ɗin da kake son saya, daga ƙarshe ka jira saƙon da ke tabbatar maka da cewar sun cire wannan kuɗi, kafin ka haɗa (Connecting) domin idan ba su aiko da sakon sun cire kudi ba kuma ka yi connecting to cikin minti 3 ko da N8000 ka saka internet zata lashe su.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. A gaskiya naji dadin wannan shafi ,sannan kuma ina yiwa wadanda suka bude shi addu’ar alkhairi sannan ina da tambaya amatsayina na wanda bai taba hawa computer ba kuma ina da sha’awar na fara to me yakamata in fara da zarar na sayi tawa.nagode

  2. Mugode da irin wannan gudun mawar dakuke bamu allah yasaka kuma yabarmu dau ma’aikatan wannan sashin da kuma wadan da suka bude sashin,
    fatan alheri daku cigaba agare ku yan’uwa, naku ukasha jibril saleh

  3. Salamu alaikum naga kun ce shi modem kala biyu ne kuma kun yi bayani akan guda daya amma baku kawo dayan ba. Da fatan za ai mana karin bayani.

  4. inasan siyan computer shin meya kamata nafara dubawa Amma sabuwa nakesan siya wane kamfani yakamata insiya? nagode