Karfin Shiga Internet Daga Blom-Blom? Google Yace Hakika!!

Masana kimiyya dake aiki da kamfanin Google sun culla maka-makan ledoji shigen blom blom da aka durawa  iskar da ake kira helium a turance, kamar guda 30 cikin sararin samaniya a kasar New Zealand.

shirin wanda na gwaji ne kamfanin yana fatar idan kome ya kankanma ta hakan zai samar da intenet ga mutane milyan dubu biyar  aduk fadin duniya, wadanda ahalin yanzu basu da damar shiga yanar gizon.

A ranar Asabar, babban kamfanin harkokin fasahar internet din ya kaddamar da wannan shiri a birnin Christchuch dake New Zealand inda masu gidaje da suka amince  da agwada  shirin da gidajensu suka fara samun karfin internet a computocinsu daga blom blom da aka culla sama.

Ledojin wanda iska ce take rike dasu zasu cigaba da  shawagi da nisan kilomita 20 daga doron kasa, kuma an tsara ta yadda zasu dore a can sama na tsawon lokaci sama da wata uku.

Shugaban kula da shirin Mike Cassidy yace injiniyoyi suna fatar samar da sukunin shiga internet kan kudi mai rahusa a duk fadin duniya musamman a sassan da basu sami cigaba ba. Ya bada misalain da  wasu sassan Afirka masu yawa inda kudin shiga internet yake dara albashin wata daya.

Daga: Muryar Amurka (VOA)

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. To amma network din nasu wayales ne kokuma zasuyi amfani namu local network provider domin qara qarfin network?
    Kuma me wayar hanu zai amfana da shirin kokuma sai me computer?