Kana Son Mallakar Windows 10? Ga Wata Sabuwar Hanya

Kamar yadda muka faɗi a cikin muƙalar mu ta yau 29/07/2015 cewar kamfanin Microsoft ya saki sabuwar manhaja ta Windows 10 kuma mun faɗi cewar duk wanda yake da Windows 8.1 ko Windows 7 zai iya saukar da ita wannan manhajar kai tsaye.

A wannan rubutu mun samu wata hanya ce da kowa zai iya saukar da wannan sabuwar manhaja kai tsaye a cikin kwamfutar sa ba tare da ya wata matsala ba.

Amma kafin ka fara saukarwa yana da kyau ka fahimci cewa:

 1. Idan kana amfani da Windows 8 ko Windows 7 za ka iya sauke shi kai tsaye a cikin kwamfutar ka kuma ya saka ba tare da ka rasa dukkanin ƙananan manhajojin da suke cikin ita kwamfutar ba, ballantana ka rasa aikace-aikacen ka.
 2. Idan kuma Windows XP ne ko Vista shi ma zai iya sauka kai tsaye amma kuma ba zai iya shiga kai tsaye ba, sai dai ya shiga a matsayin sabuwar Babbar Manhaja, ke nan dukkanin waɗansu programs ɗin da suke aiki za su tafi sai ka saka wasu daga baya.
 3. Za ka iya saukar da kowane irin tsari na Windows, tun daga Windows 10 Home, ko Home N, ko Home Single Language, ko Windows 10 Pro ko kuma Windows 10 Pro N. Sannan dukkansu suna iya sauka da irin karfin da zubin da Processor ɗin kwamfutar ka yake da shi. Ke nan kana da zaɓin saukar da tsarin 64bit ko 32bit.
 4. Kana buƙatar Intanet da sarari mai girman a kalla 4GB domin saukar da ita wannan manhaja.
 5. Kana bukatar sabon DVD ko Flash wanda za ka saka wannan Windows kafin ka iya aiki da shi a cikin wata kwamfutar.
 6. Idan ba sabunta saka manhajar za su yi ba (Upgrading) ke nan sabon zubi za ayi (Fresh Installation) kana buƙatar makullan amfani da shi.

Bayan ka tabbatar da samuwar waɗannan abubuwan sai ka zabi daya daga cikin wannan fayel domin saukar da su cikin kwamfutar ka

 1. Windows 10 32bit ka taba nan (SAUKE)
 2. Windows 10 64bit ka taba nan (SAUKE)

Dan karamin fayel zai sauko wanda girmanshi bai kai 20MB ba. Idan ya gama sai ka ɗauras hi a kan ita wannan kwamfutar a lokacin zai maka tambayoyi guda biyu.

Intall on this PC – ka ɗaura manhajar a kan wannan kwamfutar da kake saukarwa? Ko kuma Use on other PC ka saukar sannan kayi amfani da ita a wata kwamfutar.

Duk wanda ka zaba a cikin daya sai ka bi amsoshin tambayoyi domin ka sauke a cikin kwamfutarka. Wannan ita ce hanya mafi sauki da zaka iya saukar da Windows 10 cikin ruwan sanyi.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 1. Da farko dai zanyi godiya ne wajen ogana Salisu web master kan wannan wannan abu na alkari da yayi mana sharing Allah ya saka,
  Na biyu tun a karon baya nayi requesting E-book da suka shafi Information Technology to amma ban dace ba , shine nake amfani da wannan dama da kuma sake roko akan a taimaka ayi min sharing books don Allah ni dalibine wanda yake karanta INFORMATION TECHNOLOGY, ga Email adrss diina ahmadadam50@yahoo.com nagode

 2. Ina tambaya ne akan mutumin da yake da crack windows 8, zai iya upgrading? Idan kuma bazan iya ba, a taimaka min da link din da zan sauke shi (dowloading) domin na dora. Akwanakin baya nai ta kokarin saukewa sai yazo 3.7gb sai ya katse. Na gode.

 3. Nayi Downloading setup file na Windows10 amma idan zanyi installing sai yace mini “something happened” daganan kuma shikenan bazaici gaba ba. mene matsalar please? saboda komfuta ta ta mallaki duk wani system requirement da ake buqata.

 4. Assalamu alaikum, Malam Salisu,
  Ni dalibi ne na kwamfuta kuma ina da sha’awar tsara shafin bayani (website), don haka na ji dadin samun wannan shafi naka. Allah ya kara basira.