JAMB COMPUTER BASED TEST – Duniyar Computer

Cikin ikon Allah ganin yadda jama’a suke ta yin korafi a kan cewar su basa garin Kaduna ballantan su ci gajiyar wannan shirin da muke son fara gabatarwa na yadda mutum zai iya amfani da Computer domin ya amsa tambayoyin da za a yi mishi a jarabar Jamb mai zuwa.
 
Cikin kokarin da muka yi mun yi kokarin ganin mu shirya shafi na musamman wanda zai dauki tambayoyi da aka yi na jarabawar jamb da ta gabata kuma wadanda aka riga aka amsa su, mun shirya su kamar yadda Jamb take shirya nata jarabawar, haka mun tsara lokaci kamar yadda ya ke a can.
 
A halin yanzu zaku iya shiga cikin babban shafinmu na Duniyar Computer domin gwada wannan jarabawa wacce duk wanda ya gama zai iya ganin amsa da kuma shin daidai yayi ko kuma kuskure ne?
 
Idan kana son zaban jarabawar sai ka shiga www.duniyarcomputer.com sai ka duba daga sama zaka ga JAMB CBT sai ka taba domin zaban darasi. Amma a halin yanzu guda hudu muka gama shiryawa gasu kamar haka.
 
 
1) Domin Use of English taba wannan link din USE OF ENGLISH
 
2) Domin Mathematics taba wannan link din MATHEMATICS
 
3) Domin Physics taba wannan link din PHYSICS
 
4) Domin Chemistry taba wannan link din CHEMISTRY
 
Da fatan duk wanda yasan yana wajen garin Kaduna zai sanar da duk wani dalibi da yake kokarin rubuta jarabawar Jamb da ya shiga wannan shafi namu domin ga gwada.
 
Muna nan zamu sakar muku bidiyo na musamman na abubuwan da ya kamata mu kiyaye a lokacin da muke son rubuta jarabawa da kwamfuta.
 
Muna rokon Allah Ya baiwa dukkan dalibai sa’ar jarabawa, ya kara buda mana kwakwalanmu domin fahimtar ilimi cikin sauki ya sanya albarka cikin al’amuranmu.
 
Salisu Hassan Webmaster
Babban Edita
Mujallar Duniyar Computer

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *