Hanyoyi biyar (5) da ake bi a gane inda wayar “Android” take bayan ta bace ko an sace!

Dukkanin wani abu da ya kasance karami bashi da wahalar ace an dauke shi ko kuma ya fadi. Kananan wayoyi na hannu suna da dadin sha’ani da kuma saukin amfani, wasu suna da sauki ko arha a wajen siya, wasu kam dan karan tsada ke gare su, wanda ya zamanto sai ka jajirce ka daure zaka iya sayensu.

Mafi yawancin masu rike da wayoyin hannu suna kokarin kaffa-kaffa da su sabo da masu farautarsu. Da wannan dalili ne ya sanya muka zakulo muku wadannan hanyoyi guda biyar (5) da zasu taimakawa wanda yake da waya mai tsarin Android idan ta bace ko an dauke ya iya gano inda take.

  1. Wannan shine fuskar wayar da aka saka mata application an Contact Owner

    Contact Owner: wannan wani dan karamin application da ake samun shi a Android Market wanda yake taimaka maka wajen rubuta bayanai game da kanka wanda idan mutum ya tsinci wayarka zai ga cikakken sunan ka da adireshin ka, wanda hakan zai taimaka wajen neman ka idan wayan ta fada hannun na gari ne. hanyar da ake amfani da wannan dan application hanya ce mai sauki wacce da zarar ka saukar da shi wannan application a cike shine sau daya, zaka iya yin amfani da bayanai naka dake cikin wayar ka, ko kuma ka rubuta su kai tsaye. To duk sanda ita wayar taka ta je dan hutu zata kulle kanta sai wadannan bayanai da ka saka su bayyana a jikin fuskarta.

  2. Where’s My Droid: wannan application yana da matukar amfani wanda shima zai taimaka maka wajen gano inda wayarka ta hanyar amfani da “GPS”. Shi wannan application yana iya baka dam aka kunna Ringtone din wayarka ko kuma ka kasha Ringtone ta hanyar aikawa da Text Message daga wata wayar, kuma idan wayr dauke ta aka yi wannan application zai taimaka maka wajen hana barawon yin wadansu mahimman canje-canjen.
  3. Anti-Virus Software: zaka iya yin amfani da wadansu shahararrun Anti-Virus software domin gano inda wajen inda wayar ka take. Misali AVG Anti-Virus na waya idan ka saka shi a cikin wayar yana zuwa da dan wani karamin application mai suna Lost-Phone-Tracking. Idan ka saka Anti-Virus na AVG sannan kayi “configuration” na shi wannan application nasu, su kamfanin zasu taimaka maka wajen kulle wayar taka sanna ka iya gano wayar ta hanyar amfani da google map. Sannan akwai wani application mai suna Lookout Security & Antivirus shima kusan yana irin wannan aiki wanda suke iya baka damar idan waya ta bace ka iya gano ta ta hanyar Internet.
  4. Kamfanonin SIM: wasu daga cikin kamfanonin da suke bada service na waya kamar T-Mobile, da irin su Verizon dukkansu suna da application na musamman da suka yin domin gano wurin da wayrka take idan ta bace.
  5. Plan B: to idan duk wadannan hanyoyi guda hudu sun ki yin aiki, to, ga wata sabuwar hanya mai suna “Plan B” wanda ko da baka samu damar saka wani application da ke bada damar gano wayar ka ba, to wannan application din zai iya gano maka wayarka ta hanyar turo maka da sakon SMS da kuma taswirar wurin da wayar take zuwa ga akwatin gmail naka. Shiga nan domin sanin cikakken bayani akan Plan B

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. A gaskiya wannan bayani gaskiya tana da matukar amfani ga ma sauran waya da take daukar antivirus,akasari hakan takan taimaka gaya wajen gano inda wayar take ko da ma an canza sim card.Mun gode da wannan karin bayanin mai ilmantarwa.